KWAMITIN yaƙin neman sake zaɓen Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin (Maliya), a Kano ya bayyana korar fitacciyar furodusa kuma jaruma a Kannywood, Hajiya Rasheeda Adamu Abdullahi Maisa’a, daga muƙamin ta na mai taimaka wa Sanata Barau.
Sanarwar korar Hajiya Rasheeda ta fito ne daga hannun Hon. Shitu Madaki Ƙunchi, mai magana da yawun Sanata Barau.

A cewar sanarwar, mai ɗauke da kwanan wata 28/9/2026, matakin ya zama dole ne domin kare haɗin kan jam’iyyar APC da tabbatar da cewa ayyukan masu riƙe da muƙamai a ofishin Sanatan ba su zama sanadin rikici ko rarrabuwar kai a cikin jam’iyyar ba.
Wata majiya ta faɗa wa mujallar Fim cewa wannan matakin ya biyo bayan zargin cewa ana ƙoƙarin amfani da jarumar wajen haifar da hargitsi da rarrabuwar kai a cikin jam’iyyar APC ta Kano, musamman a yankin Kano ta Arewa.
Majiyar ta ƙara da cewa korar ta na da alaƙa da wasu kalamai da kuma ayyukan da ake zargin ana danganta su da ita, waɗanda aka bayyana a matsayin yunƙurin yin abin da jam’iyyar ke kallo a matsayin yi wa jam’iyyar zagon ƙasa (anti-party activities). An ce irin waɗannan ayyuka suna iya haifar da rashin fahimta da kuma rarrabuwar kai tsakanin membobin jam’iyyar.
Sai dai, ƙoƙarin da wakilin mu ya yi na jin ta-bakin Hajiya Rasheeda kan wannan korar da aka yi mata da kuma zarge-zargen da aka yi mata bai cimma nasara ba domin ya ji ko yaushe wayar ta a kashe, kuma har zuwa lokacin kammala wannan rahoto, ba a samu martanin ta kai-tsaye kan maganar ba.
![]()
