FITACCIYAR jarumar shirin ‘Izzar So’, Khadija Yobe, ta bayyana cewa mutuwar auren ta wata ƙaddara ce daga Allah.
Ta faɗi haka ne a hirar da ta yi da mujallar Fim.
Kusan shekaru biyar kenan ba a sake jin ɗuriyar Khadija Yobe ba, wadda aka fi sani da Karima a cikin ‘Izzar So’, tun bayan da ta yi aure.
Jarumar ta auri wani mawaƙin siyasa mai suna Izuddeen, kuma Allah ya albarkaci auren nasu da samun ’ya mace.
Sai dai a ’yan kwanakin nan, wasu hotuna da bidiyoyin da Khadijar ke wallafawa a soshiyal midiya sun fara jawo hankalin masoyan ta, lamarin da ya sa wasu ke tambayar halin da auren ta yake ciki.
A yanzu dai, jarumar ta tabbatar da cewa auren ta ya mutu.
A tattaunawar da ta yi da mujallar Fim ta wayar tarho, Khadija ta ce mutuwar auren nata yana daga cikin jarabawowin rayuwa da Allah ya ƙaddara mata.
“Gaskiya ne aure na ya mutu, kuma yana daga cikin jarabawar da ta same ni. Allah ne ya ƙaddara zan yi aure, sannan daga baya a rabu,” inji ta.
A cewar ta, tun bayan bayyanar labarin rabuwar tasu, tana ci gaba da karɓar kiraye-kiraye da saƙonni daga jama’a da masoyan ta, musamman waɗanda ke bayyana ra’ayoyin su a soshiyal midiya.
Ta ce: “Na daɗe ina karɓar kira daga al’umma da kuma ganin comments game da mutuwar aure na, amma dai mutane su fahimci cewa Allah ne ya ƙaddara hakan.”
Da wakilin mu ya tambaye ta ko tana shirin komawa harkar fim bayan rabuwar auren, jarumar ta ce ba ta yanke shawarar komawa ko kuma ƙin komawa fim ba.
“Ai ina kan ganiya ta na ajiye fim na rungumi aure, don haka ƙaddara ce ta yi sanadin mutuwar auren. Saboda haka ba zan ce zan koma fim ko ba zan koma ba,” inji ta.
Khadija Yobe ta yi kira ga masoyan ta da su ci gaba da yi mata addu’ar samun zaɓin Allah da abin da ya fi alheri a rayuwar ta.
“Ina kira ga masoya na su ci gaba da yi mini addu’ar fatan Allah ya zaɓa mini abin da ya fi alheri a rayuwa ta,” inji ta.
Khadija Yobe na daga cikin fitattun jaruman Kannywood da suka samu gagarumar karɓuwa, musamman sakamakon rawar da ta taka a cikin shirin ‘Izzar So’, inda take fitowa a matsayin Karima.

![]()






