• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Sunday, October 4, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Tsohuwar matar Adam Zango, Maimuna Musa, ta tabbatar da dalilin rabuwar auren su

by ABBA MUHAMMAD
August 2, 2026
in Labarai
0
Tsohuwar matar Adam Zango, Maimuna Musa, ta tabbatar da dalilin rabuwar auren su

Maimuna Musa

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

BAYAN fitaccen jarumin Kannywood Adam A. Zango ya bayyana cewa rabuwar sa da tsohuwar matar sa, jaruma Maimuna Musa, ta samo asali ne daga kasancewar dukkanin su masu Asperger Syndrome (A.S.), ita ma ta fito ta tabbatar da hakan.

A wani saƙo da ta wallafa a soshiyal midiya, Maimuna ta ce abin da tsohon mijin nata ya bayyana gaskiya ne, kuma wannan shi ne babban dalilin rabuwar su.

Ta ce: “Ni Maimuna Musa, tsohuwar matar Adam A. Zango, a yau ina so in tabbatar wa duk wanda ya ji ko ya san maganar da ya faɗa cewa, haƙiƙa, abin da ya ce gaskiya ne.

“Ya ce shi A.S. ne, ni ma A.S. ce, kuma wannan ne ya zama sanadin rabuwar mu. A yau ni ma na tabbatar da hakan. Wannan shi ne abin da ya faru, kuma na karɓi ƙaddarar Allah da zuciya ɗaya.”

Maimuna ta kuma bayyana cewa ba ta riƙe wani ƙorafi ko ƙiyayya a zuciyar ta ga tsohon mijin nata ba.

Ta ce tana yi masa fatan alheri tare da addu’ar Allah ya buɗe masa ƙofofin rahama da arziki, ya ba shi farin ciki na gaskiya, sannan ya haɗa shi da mace tagari wadda za ta zama alheri gare shi a duniya da lahira, tare da ba shi kwanciyar hankali da zaman lafiya.

Haka kuma, ta roƙi Allah ya zaɓa mata abin da ya fi alheri, tana mai cewa Shi ne mafi sanin abin da ya dace da bayin sa.

Ta kammala saƙon ta da addu’ar Allah ya ƙaddara alheri ga kowa.

A jiya ne wannan mujallar ta wallafa labarin rabuwar auren Zango da Maimuna, inda jarumin ya bayyana cewa bambancin halayen da ke tattare da kasancewar su dukkanin su masu A.S. ne ya sa suka yanke shawarar raba auren su cikin fahimtar juna.

Wataƙila fitowar Maimuna da ta tabbatar da bayanin Zango za ta kawo ƙarshen ce-ce-ku-cen da suka biyo bayan rabuwar auren, tare da nuna cewa sun rabu cikin mutuntawa da yi wa juna fatan alheri.

Loading

Tags: Adam A. ZangoMaimuna Musamutuwar aure
Previous Post

Fitaccen mawaƙin siyasa Muhammadu Buhari ‘Kosan Waka’ ya kwanta dama

Next Post

Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba

Related Posts

Tinubu da Remi sun halarci bikin fara nuna fim kan gwagwarmayar Abiola
Labarai

Tinubu da Remi sun halarci bikin fara nuna fim kan gwagwarmayar Abiola

October 1, 2026
Cewar Ability: Ba mu kafa KAFIGAN don sharholiya a Kannywood ba
Labarai

Za a ƙaddamar da reshen Kaduna na KAFIGAN ranar Asabar

October 1, 2026
Zaɓen 2027: Shettima ya nemi goyon bayan ‘yan fim da mawaƙan Arewa wajen sake zaɓen Tinubu
Siyasa

Zaɓen 2027: Shettima ya nemi goyon bayan ‘yan fim da mawaƙan Arewa wajen sake zaɓen Tinubu

September 30, 2026
Ina roƙon Rarara ya saka ni cikin ‘Triple R’ domin in samu na abinci – Baba Duduwa
Siyasa

Ina roƙon Rarara ya saka ni cikin ‘Triple R’ domin in samu na abinci – Baba Duduwa

September 30, 2026
Guguwar zaɓen 2027: Sanata Barau Jibrin ya kori jaruma Rasheeda Maisa’a daga tafiyar sa
Siyasa

Guguwar zaɓen 2027: Sanata Barau Jibrin ya kori jaruma Rasheeda Maisa’a daga tafiyar sa

September 29, 2026
Rashin lafiyar Kamaye: Sauƙi ya fara samuwa
Labarai

Rashin lafiyar Kamaye: Sauƙi ya fara samuwa

September 17, 2026
Next Post
Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba

Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!