• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, October 6, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Yadda gwajin ƙwayoyin halitta na jini ya kawo ƙarshen auren Adam A. Zango da Maimuna Musa bayan watanni 11

by ABBA MUHAMMAD
August 1, 2026
in Labarai
0
Yadda gwajin ƙwayoyin halitta na jini ya kawo ƙarshen auren Adam A. Zango da Maimuna Musa bayan watanni 11

Ƙurunƙus! Zaman Adamu da Maimuna ya ƙare

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

FITACCEN jarumin Kannywood, Adam A. Zango, ya tabbatar da rabuwar sa da matar sa, jaruma Maimuna Musa, bayan kusan watanni 11 da ɗaura auren su, yana mai bayyana cewa gwajin ƙwayoyin halitta na jini (genotype) ne ya nuna cewa su biyun masu nau’in AS ne, lamarin da ya sa suka yanke shawarar kawo ƙarshen auren domin kauce wa matsalolin da ka iya shafar ‘ya’yan su a nan gaba.

Jarumin ya bayyana hakan ne a cikin wani saƙo da ya wallafa a shafukan sa na sada zumunta cikin harshen Turanci, inda ya ce:

“Yes, it is true that we discovered we have the same genotype. I am AS, and she is also AS. Please, I kindly ask everyone not to turn this personal matter into an issue or spread false information. I only want my fans to understand the reason behind the end of our marriage, while respecting the privacy and dignity of everyone involved. As you can see, this video was recorded today as she was leaving my house happily.”

Fassarar saƙon nasa shi ne:

“E, gaskiya ne mun gano cewa muna da irin ƙwayar halittar jini iri ɗaya. Ni AS ne, ita ma AS ce. Ina roƙon kowa kada ya mayar da wannan batu na wata babbar muhawara ko ya yaɗa bayanan ƙarya. Abin da kawai nake so masoya na su fahimci ainihin dalilin da ya sa auren mu ya zo ƙarshe, tare da mutunta sirri da martabar duk wanda abin ya shafa. Kamar yadda kuke gani, an ɗauki wannan bidiyon ne a yau yayin da take barin gida na cikin farin ciki.”

Sanarwar Zango mai nuna Maimuna a ƙofar gidan sa

Kafin wannan sanarwa, an shafe kwanaki ana yaɗa ji-ta-ji-tar cewa ma’auratan sun rabu. Rahotanni sun nuna cewa batun ya fara yawo ne a tsakanin masu ruwa da tsaki a masana’antar Kannywood, musamman a wuraren ɗaukar finafinai (lokeshin), kafin daga bisani ya bazu a kafafen sada zumunta.

A ranar Juma’a ne dai lamarin ya ƙara ɗaukar hankalin jama’a, yayin da kafafen sada zumunta da na yaɗa labarai na yanar gizo suka cika da rahotanni da muhawara kan rabuwar ma’auratan.

Haka kuma, wani bidiyo ya nuna lokacin da ake kwashe kayan Maimuna daga gidan Adamu. Wasu daga cikin ‘yan jarida sun samu damar tattaunawa da jarumar, inda ta tabbatar da cewa rabuwar tasu ta tabbata.

Bayanin da Zango ya fitar ya kawo ƙarshen ji-ta-ji-tar da ake yaɗawa, tare da fayyace cewa rabuwar tasu ba ta samo asali ne daga saɓani ko rikicin zaman aure ba, sai dai bayan da gwajin ƙwayoyin halitta na jini ya nuna cewa su biyun masu genotype AS ne.

Rabuwar tasu ta sake jawo hankalin jama’a kan tarihin rayuwar auren jarumin, domin wannan shi ne karo na bakwai da ake rahoton auren sa ya zo ƙarshe.

Adam A. Zango dai ya taɓa bayyanawa, bayan rabuwar sa da tsohuwar matar sa, Safiyya Umar Chalawa, cewa ba zai ƙara yin aure ba har abada. To amma daga baya ya canja wannan matsayin nasa, ya auri Maimuna.

Mujallar Fim ta ruwaito cewa auren Zango da Maimuna bai cika shekara guda ba. Kamar yadda muka ba ku labari a ranar 19 ga Agusta, 2025, an ɗaura auren ne a ranar Lahadi, 18 ga Agusta, 2025, jim kaɗan bayan an sallamo jarumin daga asibiti, inda ya yi jinya na wani lokaci sakamakon mummunan haɗarin mota da ya ritsa da shi yayin da yake kan hanyar sa ta zuwa Kano domin halartar wasan Sallah.

Auren ya ɗauki kusan watanni 11 da wasu ‘yan kwanaki kafin ya zo ƙarshe.

Loading

Previous Post

Bikin auren darakta Aminu Saira a Azare ya ja hankalin jama’a

Next Post

Uwargida na ce ta biya sadakin aure na da amarya ta – darakta Aminu Saira

Related Posts

Tinubu da Remi sun halarci bikin fara nuna fim kan gwagwarmayar Abiola
Labarai

Tinubu da Remi sun halarci bikin fara nuna fim kan gwagwarmayar Abiola

October 1, 2026
Cewar Ability: Ba mu kafa KAFIGAN don sharholiya a Kannywood ba
Labarai

Za a ƙaddamar da reshen Kaduna na KAFIGAN ranar Asabar

October 1, 2026
Zaɓen 2027: Shettima ya nemi goyon bayan ‘yan fim da mawaƙan Arewa wajen sake zaɓen Tinubu
Siyasa

Zaɓen 2027: Shettima ya nemi goyon bayan ‘yan fim da mawaƙan Arewa wajen sake zaɓen Tinubu

September 30, 2026
Ina roƙon Rarara ya saka ni cikin ‘Triple R’ domin in samu na abinci – Baba Duduwa
Siyasa

Ina roƙon Rarara ya saka ni cikin ‘Triple R’ domin in samu na abinci – Baba Duduwa

September 30, 2026
Guguwar zaɓen 2027: Sanata Barau Jibrin ya kori jaruma Rasheeda Maisa’a daga tafiyar sa
Siyasa

Guguwar zaɓen 2027: Sanata Barau Jibrin ya kori jaruma Rasheeda Maisa’a daga tafiyar sa

September 29, 2026
Rashin lafiyar Kamaye: Sauƙi ya fara samuwa
Labarai

Rashin lafiyar Kamaye: Sauƙi ya fara samuwa

September 17, 2026
Next Post
Uwargida na ce ta biya sadakin aure na da amarya ta – darakta Aminu Saira

Uwargida na ce ta biya sadakin aure na da amarya ta - darakta Aminu Saira

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!