• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Monday, August 24, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Adam A. Zango ya yi aure bayan ya dawo daga asibiti

* Da mun san gaibu, ba za mu bari ya yi tafiya ba, inji Yerima Shettima

by ABBA MUHAMMAD
August 19, 2025
in Labarai
0
Adam A. Zango ya yi aure bayan ya dawo daga asibiti

Adam A. Zango da amarya Maimuna Musa

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

JARUMIN Kannywood Adam A. Zango ya yi aure, kwanaki kaɗan bayan ya dawo Kaduna daga Kano inda ya yi jinya sakamakon haɗarin mota da ya yi.

An ɗaura masa auren a shekaranjiya Lahadi, inda ya auri sabuwar jaruma a Kannywood, mai suna Maimuna Musa.

Idan kun tuna, a farkon watan Yuni da ya gabata Zango ya yi mummunan haɗarin mota a hanyar sa ta zuwa Kano domin wasan Babban Sallah, har wata mace matashiya ta rasu a motar.

An kwantar da jarumin a asibiti tsawon lokaci, da aka sallame shi kuma ya ci gaba da yin jinya a Kano.

A makon jiya ya dawo gida Kaduna, kuma aka ɗaura masa aure.

Mujallar Fim ta ruwaito cewar ya yi wannan auren ne shekaru biyu da wata huɗu bayan rabuwar sa da matar sa ta shida da ya aura, wato Safiyya Umar Chalawa wadda suke da ‘ya ɗaya a tsakanin su.

Tun da ya dawo gida yake ta samun ɗimbin maziyarta daga sassa daban-daban na ƙasar nan, musamman ‘yan fim na Jihar Kaduna, masu zuwa yi masa jajen abin da ya faru.

Ɗaya daga cikin su, aminin da ne, Alhaji Yerima Shettima, wato shugaban Ƙungiyar Masu Ruwa da Tsaki ta Arewa (Northern Stakeholders Initiative, NSI).

Shettima da tawagar sun kai ziyarar dubiyar a jiya Litinin a gidan Zango da ke unguwar Barakallahu GRA da misalin ƙarfe 3:30 na yamma.

Yerima Shettima da Adam A. Zango
Yerima Shettima da Adam A. Zango
Yerima da tawagar sa a falon Adam Zango
Yerima da tawagar sa a falon Adam Zango

Su Yerima sun iske shi a falon sa, inda a nan aka yi masa addu’o’i na samun lafiya.

Yerima, wanda ɗan siyasa ne kuma mijin tsohuwar jarumar Kannywood Fati Ladan, ya jefi tsuntsu biyu da dutse ɗaya ne, domin bayan jajen, sai kuma ya taya shi murnar auren da ya yi.

Da yake jawabi yayin ziyarar, Yerima ya ce:

“Da mun san gaibu, ba za mu bari ka yi tafiyar nan ba domin har ɗaure ka zan sa a yi a gida na in ka ce sai ka tafi. Amma da yake lamari ne na Ubangiji, babu wanda ya isa ya ja. Sanin gaibu sai Allah.”

Ya ƙara da cewa, “Ana gobe za ka samu haɗarin, ka kai kusan goma na dare a gida na, har ina tunanin za ka zo wasan ƙwallon da za a yi a ranar, ashe tsautsayi ya kira ka. Allah ya ba ka lafiya.”

A nasa ɓangaren, Zango ya ce, “Ni kai na ba a ranar ya kamata in tafi ba. Amma haka Allah ya tsara lamarin sa. Ina godiya sosai da wannan ziyara, Allah ya saka da alkhairi, Allah ya bar zumunci. Na gode.”

Alhaji Shehu Sani Sado, Dakta Bashir Umar da Mista Ɗanjuma Don J

Wasu daga cikin waɗanda suka je ziyarar sun haɗa da Alhaji Shehu Sani Sado, Mista Ɗanjuma Don J, Mista Yabo, Dakta Bashir Umar, Honarabul Aminu Monye, Honarabul Ibrahim PDP, Zaharaddeen Sani, Muhammad Ayuba (Karl Marx), Kwamared Sagir Umar, DJ Abdul, Nuhu Ɗanmani, Kwamared Mustapha, Ibrahim Alhassan, Ibrahim Auwal, Hajiya Maryam Masha, da Khadija Mukhtar.

Loading

Previous Post

Ali Nuhu na nan a raye babu abin da ya same shi – NFC

Next Post

Sarkin Kano Muhammadu Sunusi ll ya buƙaci iyaye su saka ido kan finafinan da yaran su ke kallo

Related Posts

Mutuwar aure na ƙaddara ce – Jaruma Khadija Yobe
Labarai

Mutuwar aure na ƙaddara ce – Jaruma Khadija Yobe

August 23, 2026
Aina’u Ade ta raba wa tsofaffin jaruman Kannywood tallafin kuɗi
Labarai

Aina’u Ade ta raba wa tsofaffin jaruman Kannywood tallafin kuɗi

August 23, 2026
Ƙungiyar ‘Triple R Kannywood’ ta ziyarci jarumi Tanimu Akawu a asibiti
Labarai

Ƙungiyar ‘Triple R Kannywood’ ta ziyarci jarumi Tanimu Akawu a asibiti

August 23, 2026
Ƙungiyar Triple R ta ba jarumin Kannywood Mustapha Musty tallafin N500,000
Labarai

Ƙungiyar Triple R ta ba jarumin Kannywood Mustapha Musty tallafin N500,000

August 18, 2026
Yadda na gamu da ibtila’in karaya a ƙafa – Jarumi Ɗan’azumi Kamaye
Labarai

Yadda na gamu da ibtila’in karaya a ƙafa – Jarumi Ɗan’azumi Kamaye

August 14, 2026
Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba
Labarai

Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba

August 8, 2026
Next Post
Sarkin Kano Muhammadu Sunusi ll ya buƙaci iyaye su saka ido kan finafinan da yaran su ke kallo

Sarkin Kano Muhammadu Sunusi ll ya buƙaci iyaye su saka ido kan finafinan da yaran su ke kallo

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!