HUKUMAR Shirya Finafinai ta Nijeriya (NFC) ta ƙaryata ji-ta-ji-tar da aka riƙa yaɗawa kwanaki a soshiyal midiya cewa wai Manajan Daraktan hukumar, Dakta Ali Nuhu, ya rasu.
A cikin wata sanarwar manema labarai da Daraktan Hulɗa da Jama’a na hukumar, Brian Etuk, ya fitar a jiya Litinin, hukumar ta ce ta samu labarin ji-ta-ji-tar da ake yaɗawa a soshiyal midiya cewa wai Ali ya rasu.
Hukumar ta ce tana sanar da jama’a a hukumance cewa wannan rahoto da ake yaɗawa har ma da haɗa wasu bidiyoyi duk ƙarya ne, da ƙeta kuma ba ta da tushe ko makama.
Ta ce Dakta Ali Nuhu yana nan da rai, cikin ƙoshin lafiya, kuma yana ci gaba da gudanar da aikin sa na shugabancin NFC.
Haka kuma NFC ta ja hankalin waɗanda suka kitsa wannan mummunar ɗabi’a da ba ta dace ba, da ma masu tallafa masu, cewa mummunan sakamako yana jiran su, duk da cewa suna iya ɗaukar abin a matsayin wasa.
Ta ce a halin yanzu an ɗauki wasu matakai na musamman domin kawo ƙarshen wannan mummunar ɗabi’a da rashin ɗa’a.
Hukumar ta gode wa jama’a bisa damuwar da suka nuna, haka kuma ga masu ruwa da tsaki daga ɓangaren gwamnati da masu zaman kan su bisa irin damuwar da su ka bayyana.
Shi dai Ali, wanda fitaccen jarumi ne, Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ne ya naɗa shi shugaban NFC a ranar 12 ga Fabrairu, 2024.
A makon jiya ne aka yaɗa labarin bogi a soshiyal midiya cewa wai ya rasu.
Mujallar Fim ta ruwaito cewa shekaru da dama an sha yi masa irin wannan ƙaryar. Kuma ba shi kaɗai ba, jarumai da dama sun sha faɗawa hannun irin waɗannan maƙaryatan.
Ko a makwanni biyu da suka gabata, an yaɗa ƙaryar cewa jarumi Rabi’u Rikadawa ya rasu.
![]()







