• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Thursday, August 13, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Uwargida na ce ta biya sadakin aure na da amarya ta – darakta Aminu Saira

by ALI KANO
August 2, 2026
in Ranar Murna
0
0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

FITACCEN daraktan finafinan Kannywood, Malam Aminu Saira, ya bayyana irin gudunmawar da matar sa ta farko, A’isha, ta bayar wajen gudanar da sabon auren sa da Maryam Mahmoud, yana mai cewa ita ce ta biya masa sadakin da kuɗin ta.

A wani saƙon godiya da ya wallafa a soshiyal midiya bayan an ɗaura auren sa da Maryam a garin Azare, Jihar Bauchi, daraktan ya ce Aisha ta nuna karamci da mutunci na musamman tun daga farkon shirin auren, ciki har da biyan sadakin Maryam da kuɗin ta da kuma bayar da gudunmawa a sauran harkokin bikin.

Saira ya ce hakan da ta yi ya ƙara mata daraja a idanun sa da kuma na iyalan amaryar.

Ya ce, “Karamci, mutunci da sadaukarwa na ƙarshen ƙurewa uwargida na Aisha ta nuna a cikin hidimar aure na.”

Ya ƙara da cewa Aisha ba wai kawai ta taimaka wajen gudanar da bikin ba ne, har ma ta karɓi sabuwar abokiyar zaman ta cikin girmamawa da kyakkyawar mu’amala.

“Wannan ya ƙara mata ƙololuwar daraja a idanu na da idon amarya ta da dangin ta. Mace irin Aisha, babu wani ɗan halak da ba zai mata adalci da halacci ba,” inji shi.

Saira ya kuma bayyana dalilin da ya sa ya zaɓi Maryam Mahmoud a matsayin sabuwar matar sa, yana mai cewa ta nuna halayen nagarta tun daga farkon al’amuran auren su.

“Na auri Maryam saboda tana da halayen nagarta na ƙarshe ita ma, kuma su ta yi ta nunawa tun daga farkon al’amari,” inji daraktan.

Ya ce ya gode wa Allah da ya azurta shi da matan sa, yana fatan za su ci gaba da tafiya a kan hanya madaidaiciya.

A wani saƙon godiya da ya wallafa, Saira ya gode wa ’yan’uwa da abokan arziki da suka halarci bikin auren a Azare, da kuma waɗanda ba su samu damar zuwa ba amma suka taya shi da iyalan sa da addu’o’i.

Ya ce, “Ina miƙa saƙon godiya ga ’yan’uwa da abokan arziki da suka halarci bikin aure na a garin Azare da ke Jihar Bauchi, sannan ina miƙa godiya ga mutanen da ba su samu damar halarta ba, suka taya mu da addu’a.”

Daraktan ya bayyana cewa babban abin da yake fata shi ne samun ikon gudanar da rayuwar auren sa bisa adalci da koyarwar addini.

“Mu kuma Allah ya ba mu ikon yin adalci ga matan mu kamar yadda addinin mu ya yi umurni,” inji shi.

Loading

Tags: Aminu Sairaaure
Previous Post

Yadda gwajin ƙwayoyin halitta na jini ya kawo ƙarshen auren Adam A. Zango da Maimuna Musa bayan watanni 11

Next Post

‘Ya’ya biyu mata na Mudassir Kasim sun yi saukar karatun Alƙur’ani

Related Posts

Bikin auren darakta Aminu Saira a Azare ya ja hankalin jama’a
Ranar Murna

Bikin auren darakta Aminu Saira a Azare ya ja hankalin jama’a

July 31, 2026
An taya Aisar, jikar marubuciya Sadiya Garba Yakasai, murnar cika shekaru 5
Ranar Murna

An taya Aisar, jikar marubuciya Sadiya Garba Yakasai, murnar cika shekaru 5

July 15, 2026
Jarumin Kannywood Tijjani Faraga ya aurar da ‘yar sa ta biyu
Ranar Murna

Jarumin Kannywood Tijjani Faraga ya aurar da ‘yar sa ta biyu

July 12, 2026
Mawaƙi Sa’eed Ja’afar ya samu ƙaruwa da ‘ya mace
Ranar Murna

Mawaƙi Sa’eed Ja’afar ya samu ƙaruwa da ‘ya mace

July 6, 2026
Furodusa Alhaji Sheshe da Khairiyyah sun zama ɗaya
Ranar Murna

Furodusa Alhaji Sheshe da Khairiyyah sun zama ɗaya

July 4, 2026
Abokai sun shirya yin walima don taya jarumin Kannywood AS Bello murnar zama Farfesa
Ranar Murna

Abokai sun shirya yin walima don taya jarumin Kannywood AS Bello murnar zama Farfesa

July 2, 2026
Next Post
‘Ya’ya biyu mata na Mudassir Kasim sun yi saukar karatun Alƙur’ani

'Ya'ya biyu mata na Mudassir Kasim sun yi saukar karatun Alƙur'ani

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!