ƘUNGIYAR Abokai na Ƙuruciya ta Wudil (The Childhood Group of Friends, Wudil) ta shirya walimar karramawa domin taya ɗaya daga cikin mambobin ta kuma jarumi a Kannywood, Farfesa A.S. Bello, murnar samun muƙamin Farfesa.
An tsara za a gudanar da walimar ne a ranar Asabar mai zuwa, wato 4 ga Yuli, 2026, da misalin ƙarfe 1:30 na rana, a Top Star Events & Sport Arena, da ke Titin Fanpale, a Ƙaramar Hukumar Wudil ta Jihar Kano.
Mataimakin Shugaban Jami’ar Ilimi ta Tarayya da ke Zariya, Farfesa Yahaya Isa Bunkure, shi ne zai jagoranci taron a matsayin shugaban taro, yayin da Birgediya Janar A.A. Bello zai kasance mai ɗaukar nauyin walimar.
Haka kuma, fitaccen mawaƙi Alhaji Aminu Ladan Abubakar (Alan Waƙa) zai halarci taron domin nishaɗantar da baƙi da sauran mahalarta.
Mujallar Fim ta ruwaito cewa an buɗe ƙofar halartar walimar ga kowa da kowa. Sai dai Farfesa A. S. Bello ya roƙi duk wanda ba zai samu damar halarta ba da ya sanya shi cikin addu’a.
Farfesa A.S. Bello fitaccen jarumi ne a masana’antar Kannywood, sannan malami ne a Jami’ar Ilimi ta Tarayya da ke Zariya. Haka kuma, marubuci ne kuma manazarci da ya bayar da gagarumar gudunmawa wajen bunƙasa ilimi da harkokin finafinan Hausa.
![]()







