• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Monday, October 12, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Bikin auren Ibrahim Nuhu Gudaji da Zainab Adamu (Najlah): Marubuta sun yi wa Hadiza Nuhu Gudaji da Lubabatu Ya’u kara

by MUKHTAR YAKUBU
October 10, 2026
in Ranar Murna
0
Bikin auren Ibrahim Nuhu Gudaji da Zainab Adamu (Najlah): Marubuta sun yi wa Hadiza Nuhu Gudaji da Lubabatu Ya’u kara

Ango Ibrahim Nuhu Gudaji da amarya Zainab Adamu (Najlah)

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

MASU magana sun ce rana ba ta ƙarya, sai dai uwar ‘ya ta ji kunya. Wannan karin magana ya yi daidai da yadda aka gudanar da bikin auren ‘ya’yan fitattun marubuta mata biyu, Hadiza Nuhu Gudaji da Lubabatu Ya’u Ɓaɓura a Kano a ranar Asabar, 10 ga Oktoba, 2026.

Bikin, wanda ya kasance wani babban lamari a duniyar marubutan Hausa, ya ɗauki hankali tare da ƙayatarwa. Haka kuma, ya zama wata muhimmiyar mahaɗa ta sada zumunta tsakanin marubuta da sauran al’ummar da suka halarta, inda aka samu haɗuwar abokan sana’a da dama da suka dade ba su haɗu a irin wannan yanayi ba.

Marubuta maza a wajen bikin da aka yi a Amani Event Centre
Daga dama: Alawiyya Wada da mijin ta Aminu (Ala), Bilkisu Yusuf Ali, Rahama Abdulmajid, da wata

Tun da farko dai, an fara gudanar da shagulgulan bikin ne a ranar Laraba, inda aka shirya taron kamun ango a White Lopt Event Centre da ke kan Titin BUK a cikin birnin Kano.

A rana ta biyu, an gudanar da taron wunin uwa a wani gagarumin biki da aka shirya a unguwar Sharaɗa, cikin Rukunin Masana’antu na II.

Taro na uku kuma ya gudana ne a Amani Event Centre da ke hanyar Tamandu, a Nassarawa GRA, Kano. Wannan taro ya samu halartar manyan marubuta mata da maza daga sassa daban-daban na Nijeriya, har ma da wasu daga ƙetare.

Ango da amarya tare da su Bilkisu Yusuf Ali

Baya ga marubuta, taron ya samu halartar manyan baki daga ɓangarori daban-daban na rayuwa, ciki har da malamai, ‘yan siyasa, ‘yan jarida da masu riƙe da sarautun gargajiya.

Ɗaya daga cikin abubuwan da suka ƙara wa bikin armashi shi ne yadda marubuta mata da maza suka yi cincirindo domin taya iyalai biyu murnar wannan rana mai muhimmanci.

Daga hagu: Aminu Ala, Hadiza Nuhu Gudaji, da uban ango, Alhaji Nuhu Gudaji
Uwar amarya, Lubabatu Ya’u Ɓaɓura (ta 2 daga hagu) da mahalarta taron

Daga cikin marubuta mata da suka halarci taron akwai Fauziyya D. Sulaiman, Sadiya Garba Yakasai, Bushira Nakura, Zuwaira Dauda Kolo, Asma’u Sani, Alawiyya Wada Isa, Hauwa Ƙyalƙyal Banza, Rabi Talle Maifata, Zainab Lawan, Bilkisu Yusuf Ali, Maimuna Idris Beli, Amina Hassan Abdussalam, Ikilima Kassim Bichi, Rahama Abdulmajid, Fatima Abba Gana, Halima K. Mashi, Salma Sa’eed Mailambu da Ummulkhairi Sani Fanisau.

A ɓangaren marubuta maza kuwa, waɗanda suka halarci bikin sun haɗa da Nazir Adam Saleh, Nasir Ciromawa, Aminu Ladan Abubakar (Ala), Muhammad Lawan PRP, Zubairu Ballanaji, Ibrahim Muhammad Indabawa, Ado Ahmad Gidan Dabino, Ayuba Muhammad Ɗanzaki, Kabiru Yusuf Fagge (Anka), Mukhtar Musa Ƙarami da Adamu Yusuf Indabo, da sauran su.

Uwar amarya, Lubabatu Ya’u (a hagu), tare da Halima K. Mashi

Yawan marubutan da suka halarta ya ƙara nuna irin kyakkyawar alaƙar zumunta da ke tsakanin marubutan Hausa, tare da bayyana muhimmancin irin waɗannan taruka wajen ƙarfafa danƙon zumunci da haɗin kai a tsakanin su.

An ɗaura auren Ibrahim Nuhu Gudaji, ɗan marubuciya Hadiza Nuhu Gudaji, da Zainab Adamu, wadda aka fi sani da Najlah, ‘yar marubuciya Lubabatu Ya’u Ɓaɓura, a safiyar ranar Asabar, 10 ga Oktoba, 2026 a Masallacin Aliyu Ibn Abi Dalib, da ke Shataletalen Dangi, a hanyar Zariya, Kano.

Bayan kammala ɗaurin aure da sauran shirye-shiryen bikin, an ɗauki amarya zuwa gidan mijin ta da yammacin ranar, lamarin da ya kawo ƙarshen shagulgulan bikin.

Bikin ya kasance wani abin tunawa ga iyalan ango da amarya, da kuma abokan arziki, musamman marubuta, waɗanda suka samu damar haɗuwa tare da taya sababbin ma’auratan murnar shiga sabon matakin rayuwar su.

Dandazon mahalarta walimar bikin

Loading

Tags: aureHadiza Nuhu GudajiIbrahim Nuhu GudajiLubabatu Ya'umarubutaZainab Adamu (Najlah)
Previous Post

Hukumar Tace Finafinai ta karɓi uzirin Tijjani Gandu

Related Posts

Furodusan ‘Wata Shida’, Hayatuddeen Yakubu ya sake aure wata 7 bayan rasuwar matar sa
Ranar Murna

Furodusan ‘Wata Shida’, Hayatuddeen Yakubu ya sake aure wata 7 bayan rasuwar matar sa

September 28, 2026
An ɗaura auren Faɗima ‘yar furodusan Kannywood marigayi Nura Shariff
Ranar Murna

An ɗaura auren Faɗima ‘yar furodusan Kannywood marigayi Nura Shariff

September 7, 2026
Farha, ‘yar tsohuwar jaruma Halima Atete, ta cika shekara ɗaya
Ranar Murna

Farha, ‘yar tsohuwar jaruma Halima Atete, ta cika shekara ɗaya

September 5, 2026
Mawaƙi Abdool-Gaya ya samu ƙaruwar ɗa namiji
Ranar Murna

Mawaƙi Abdool-Gaya ya samu ƙaruwar ɗa namiji

August 24, 2026
An ɗaura auren mawaƙi Kawu Ɗan Sarki
Ranar Murna

An ɗaura auren mawaƙi Kawu Ɗan Sarki

August 23, 2026
Yadda marubuciya Aunty Baby ta yi bikin cikar shekara 51
Ranar Murna

Yadda marubuciya Aunty Baby ta yi bikin cikar shekara 51

August 19, 2026
  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!