FITACCEN mawaƙi, jarumi kuma furodusa a masana’antar Kannywood, Abdool-Gaya, ya samu ƙaruwar ɗa namiji, lamarin da ya sanya shi cikin farin ciki da godiya ga Allah.
Matar Abdool-Gaya ta haifi ɗan a ranar 15 ga Agusta, 2026, sannan aka yi bikin suna a ranar Asabar, 22 ga Agusta, a gidan sa da ke Kano.
An sanya wa jaririn suna Mubarak, wanda ake yi wa laƙabi da Sabeer.

Da yake bayyana farin cikin sa, Abdool-Gaya ya nuna godiyar sa ga Allah bisa wannan ni’ima da ya samu, tare da roƙon Allah Ya raya masa ɗan sa cikin imani da lafiya.
Ya ce: “Alhamdulillah! Yau rana ce ta farin ciki da godiya ga Allah. Mun yi bikin suna na jaririn mu. Allah ya raya mana shi cikin imani da lafiya. Ya sa ya zama abin alfahari ga iyaye da al’umma. Amin.”



![]()






