• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Saturday, October 31, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result

  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Ƙungiyar ANA Kano za ta horas da matasa dabarun rubuta gajerun labarai

by MUKHTAR YAKUBU
August 24, 2026
in Marubuta
0
Ƙungiyar ANA Kano za ta horas da matasa dabarun rubuta gajerun labarai

Malam Jamilu Haruna Jibeka

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

Kungiyar Marubuta ta Nijeriya (ANA), reshen Jihar Kano, ta ɓullo da wani shiri na horas da matasa dabarun rubuta gajerun labarai, da nufin farfaɗo da harkar rubuce-rubucen adabi tare da dasa sha’awar karatu da rubutu a zukatan matasan.

A wata sanarwa da kwamitin editoci na ƙungiyar ya fitar, ANA Kano ta ce tana farin cikin sanar da membobin ta masu son ƙara ƙwarewa, masu sha’awar koyon rubutu, da ɗaliban makarantun sakandare game da wani taron bita na musamman da ƙungiyar za ta riƙa shirya wa dukkan rubu’in shekara.

Sanarwar ta ce bitar wannan rubu’in za ta mayar da hankali ne kan “Dabarun Rubuta Gajerun Labarai”, inda mahalarta za su koyi dabarun da ake amfani da su wajen tsara gajeren labari mai armashi da tasiri a zuciyar mai karatu.

A cewar ƙungiyar, a karon farko ta gayyaci sananne kuma gogaggen marubuci, Malam Jamilu Haruna Jibeka, domin jagorantar bitar tare da ilimantar da mahalarta kan dabarun rubuta gajerun labarai.

Muhimman bayanan bitar

  • Take: Dabarun Rubuta Gajerun Labarai
  • Jagora: Jamilu Haruna Jibeka
  • Rana: Asabar, 5 ga Satumba, 2026
  • Lokaci: 10:00 na safe
  • Wuri: Jami’ar Khalifa Isyaku Rabi’u, Ƙofar Gadon Ƙaya, Kano

Rijista da abin da ta ƙunsa

Ƙungiyar ta ce kuɗin rijistar mahalarta shi ne N2,000, yayin da ɗaliban da aka gayyata za su halarci bitar kyauta.

Rijistar ta ƙunshi samun shaidar halarta (satifiket), kayayyakin karatu da rubutu, da kuma ɗan abin taɓawa.

Yadda za a yi rijista

Masu sha’awar halartar bitar za su biya kudin rijista ta asusun 8065270511 na Opay, sannan su aika da rasitin biyan kudin tare da cikakken suna da lambar waya ta WhatsApp zuwa 08065270511.

Kungiyar ta ce wa’adin aika bayanan rijistar shi ne Talata, 2 ga Satumba, 2026.

Ta kuma bayyana cewa za a taƙaita adadin mahalarta domin samar da kyakkyawan yanayin koyarwa da koyo, inda ta buƙaci masu sha’awar shiga bitar da su gaggauta yin rijista domin samun gurbi.

Loading

Tags: ANAbitaJamilu Haruna JibekaKanomarubuta
Previous Post

Mawaƙi Abdool-Gaya ya samu ƙaruwar ɗa namiji

Next Post

Ranar Marubuta 2026: Katsina za ta karɓi baƙuncin taron, an fara rajistar mahalarta

Related Posts

Ƙungiyar Women of Words za ta ƙaddamar da littafin ‘Mutuwar Kasko’ a yayin cika shekara biyu
Marubuta

Ƙungiyar Women of Words za ta ƙaddamar da littafin ‘Mutuwar Kasko’ a yayin cika shekara biyu

October 14, 2026
Taron gabatar da littafin waƙoƙin Salma ɗiyar marubuciya Halima K Mashi ya rikiɗe zuwa yanayin jimami, mahalarta sun zubar da hawaye
Marubuta

Taron gabatar da littafin waƙoƙin Salma ɗiyar marubuciya Halima K Mashi ya rikiɗe zuwa yanayin jimami, mahalarta sun zubar da hawaye

August 30, 2026
Ranar Marubuta 2026: Katsina za ta karɓi baƙuncin taron, an fara rajistar mahalarta
Marubuta

Ranar Marubuta 2026: Katsina za ta karɓi baƙuncin taron, an fara rajistar mahalarta

August 27, 2026
Taron Ranar Marubuta Hausa ta Duniya: Sanarwar Bayan Taro
Marubuta

Taron Ranar Marubuta Hausa ta Duniya: Sanarwar Bayan Taro

January 10, 2026
Taron Ranar Marubutan Hausa ta Duniya ya gabato, shirye-shirye sun kankama
Marubuta

Taron Ranar Marubutan Hausa ta Duniya ya gabato, shirye-shirye sun kankama

December 25, 2025
‎Sanata Shehu Sani ya ba gwarazan gasar Hikayata kyautar miliyan ɗaya a taron liyafa
Marubuta

‎Sanata Shehu Sani ya ba gwarazan gasar Hikayata kyautar miliyan ɗaya a taron liyafa

December 25, 2025
Next Post
Ranar Marubuta 2026: Katsina za ta karɓi baƙuncin taron, an fara rajistar mahalarta

Ranar Marubuta 2026: Katsina za ta karɓi baƙuncin taron, an fara rajistar mahalarta

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!