• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Saturday, October 31, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Taron gabatar da littafin waƙoƙin Salma ɗiyar marubuciya Halima K Mashi ya rikiɗe zuwa yanayin jimami, mahalarta sun zubar da hawaye

by MUKHTAR YAKUBU
August 30, 2026
in Marubuta
0
Taron gabatar da littafin waƙoƙin Salma ɗiyar marubuciya Halima K Mashi ya rikiɗe zuwa yanayin jimami, mahalarta sun zubar da hawaye

Matashiyar mawaƙiya kuma marubuciya Salma Sa'eed Mailambu tana rera waƙar da ta rikita jama'a a taron

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

TARON gabatar da littafin waƙoƙi mai suna ‘Tambarin Zamani’, wanda matashiyar mawaƙiya kuma marubuciya Salma Sa’eed Mailambu ta wallafa, ya sauya zuwa wani yanayi na jimami da tausayi, inda mahalarta da dama suka kasa riƙe hawaye bayan sauraron wata waƙa da marubuciyar ta rera game da tarihin rayuwar ta.

Salma dai ‘ya ce ga fitacciyar marubuciya Hajiya Halima K/Mashi. Shekarun ta 15 da haihuwa.

An gudanar da taron ne a jiya Asabar, 29 ga Agusta, 2026 a Ɗakin Taro na Sa’adu Zungur da ke Gidan Mambayya a unguwar Gwammaja cikin birnin Kano, inda mutane da dama daga ciki da wajen Jihar Kano suka halarta.

Da yake jawabi a farkon taron, fitaccen marubuci kuma mawallafi Malam Ado Ahmad Gidan Dabino, MON, wanda shi ne jagoran kwamitin shirya taron, ya bayyana cewa manufar shirya taron ita ce gabatar da littafin waƙoƙin ‘Tambarin Zamani’, domin a taskace basirar Salma Sa’eed Mailambu da kuma adana waƙoƙin ta a matsayin wani ɓangare na adabin Hausa.

 

Shugaban taron, Alhaji Aminu Ala, yana Jawabi
Mahaifiyar Salma, Halima K/Mashi (a hagu) tare da Dakta Bilkisu Yusuf Ali
Alhaji Aminu Ala (a dama) tare da Salenken Ƙasar Hausa, Alhaji Abdulrahman Muhammad Mubi

Ya ce Salma, duk da ƙananan shekarun ta, Allah ya hore mata baiwar rubutu da rera waƙoƙi, inda ta tattara waƙoƙi guda 20 da aka ga dacewar wallafa su cikin littafi.

A cewar sa: “Mun ga ya dace a ƙarfafa wannan baiwa da Allah ya yi wa Salma, musamman ganin yadda ta tattara waƙoƙin ta domin a adana su. Wannan wata hanya ce ta taskace adabi da kuma samar da abin karantawa ga al’umma.”

Ya ƙara da cewa ana fatan taron zai samar wa marubuciyar da gudunmawar da za ta ƙarfafa mata gwiwa wajen ci gaba da ayyukan ta na bunƙasa da adana adabin Hausa, tare da taimaka mata wajen ƙara wallafa littattafai domin amfanin al’umma, musamman yara masu sha’awar karatu.

Shi ma da yake jawabi a matsayin sa na uban taro, Sarkin Adabin Ƙasar Hausa, Alhaji Aminu Ladan Abubakar (Alan Waƙa), ya bayyana wallafar ‘Tambarin Zamani’ a matsayin wani babban cigaba ga duniyar adabi.

Jagoran shirya taron, MalamAdo Ahmad Gidan Dabino, yana jawabi
Farfasa Abdalla Uba Adamu yana gabatar da jawabin sa a taron

Ya ce littafin zai taimaka wajen zaburar da yara da matasa masu sha’awar karatu, tare da taimakawa wajen dawo da al’adar karanta littattafai, wadda ya ce tana fuskantar barazanar gushewa a wannan zamani.

Ala ya jinjina wa Salma bisa basirar da Allah ya ba ta, musamman yadda ta yi tunanin tattara waƙoƙin ta tare da wallafa su cikin littafi tun tana ƙarama.

A nasa jawabin, Dakta Mujahid Abdullahi Kudan, malami a Jami’ar Jihar Kaduna (KASU), wanda shi ne ya gabatar da tarihin rayuwar marubuciyar, ya bayyana cewa mutum ne yake rubuta tarihin rayuwar sa, wanda wasu za su karanta bayan shekaru masu yawa ko kuma bayan mutuwar sa.

Ya ce: “Salma Sa’eed Mailambu ta rubuta wani ɓangare na tarihin rayuwar ta a cikin wannan littafi. Mu ne za mu karanta yanzu, sannan waɗanda za su biyo bayan mu su ma za su karanta.”

Dakta Mujahid ya bayyana tarihin Salma tun daga haihuwar ta a Kaduna, da yadda ta taso, da farkon bayyana baiwar ta ta waƙa, tare da ambaton kasancewar ta ɗaliba a ƙaramin matakin sakandare mai shekaru 15 a duniya.

Dakta Aisha Shehu Maimota tana ta’aliƙi kan littafin
Wani sashe na mahalartan taron
Tsohon Editan mujallar Fim, Alhaji Ashafa Murnai Barkiya, yana jawabi

Shi kuma Dakta Murtala Uba Muhammad shi ne ya gabatar da sharhin littafin, yayin da Dakta Aisha Shehu Maimota ta yi ta’aliƙi kan littafin.

Waƙar da ta sauya yanayin taro

Bayan kammala jawabai, an gayyaci Salma domin ta zaɓi waƙar da za ta rera wa mahalarta, ko dai daga cikin waƙoƙin gargajiya da ta kwaikwaya ko kuma daga cikin waƙoƙin da ke cikin littafin ta. Sai ta zaɓi wata waƙa da ta ƙirƙira da kan ta mai taken ‘Ƙaddarar Rayuwa ta.’

Tun farkon fara waƙar ne Salma ta kasa riƙe hawayen ta, inda ta ci gaba da rerawa cikin kuka da wani yanayi mai matuƙar taɓa zuciya. A cikin waƙar, ta bayyana yadda ta taso tun tana ƙarama cikin kulawa da ƙauna daga mahaifin ta da mahaifiyar ta, tare da irin kulawar da take samu daga ‘yan’uwan ta, yayyen ta da sauran mutanen da ke kewaye da ita.

Daga hagu: Uwargidan Alhaji Aninu Ala, Hajiya Alawiyya Wada Isa; Dakta Bilkisu Yusuf Ali, da Hajiya Fatima Ɗanbarno
Hajiya Fauziyya D. Sulaiman a taron

Sai dai, kamar yadda ta bayyana cikin waƙar, ƙaddara ta sauya mata tsarin rayuwa, bayan rabuwar aure tsakanin mahaifin ta da mahaifiyar ta, lamarin da ya kawo sauye-sauye masu yawa a rayuwar ta.

Ta bayyana yadda wannan al’amari ya shafi karatun ta, zamantakewar ta da dangantakar ta da ‘yan’uwan ta da sauran dangi, tare da sauya mata fannoni daban-daban na rayuwa.

Kafin ta kai ƙarshen waƙar, ɗakin taron ya yi tsit, yayin da hawaye suka cika idanun mahalarta da dama. Wasu suna kuka, wasu kuma fuskokin su sun nuna tsananin damuwa da tausayi.

A lokaci guda, sai taron da aka shirya domin murnar gabatar da littafi ya rikiɗe zuwa wani yanayi na alhini da jimami, kamar yadda mahalarta suka natsu cikin tunani da tausayin irin abubuwan da matashiyar marubuciyar ta bayyana.

Jama’a sun sayi littafin domin ƙarfafa marubuciyar

Bayan kammala waƙar, sai aka shiga gabatar da littafin ga mahalarta domin saye da bayar da gudunmawa wajen ƙarfafa wa Salma gwiwa. Waɗanda suka bayar da gudunmawar kuɗi sun haɗa da:

1. Babban mai gabatarwa, Alhaji Salisu Hamza Rimaye, wanda ya sayi kwafi huɗu kan kuɗi N200,000;

2. Babban furodusan finafinai a Kannywood, Alhaji Abdul Amart Mohammed, ya sayi kwafe biyu kan N500,000;

3. Salanken Ƙasar Hausa, Alhaji Abdurahman Muhammad Mubi, ya ba da N100,000;

4. Gidauniyar Dakta Bukar Usman ta bayar da N150,000;

5. Dakta Ibrahim Sheme, wanda Alhaji Ashafa Murnai Barkiya ya wakilta, ya ba da N100,000;

6. Tsohon Editan mujallar Fim, jaridar Leadership Hausa, da jaridar Rariya, Alhaji Ashafa Murnai Barkiya, ya bayar da N50,000, matar sa ta bayar da N20,000, yayin da ‘yar sa ta bayar da N10,000. Bugu da ƙari, Alhaji Ashafa ɗin dai ya ɗauki nauyin karatun Salma na tsawon shekara guda;

7. Mai ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Yaɗa Labarai, Alhaji Abdulaziz Abdulaziz, wanda Dakta Bilkisu Yusuf Ali ta wakilta, ya ba da N200,000;

8. Hajiya Aisha Humaira, matar fitaccen mawaƙi Dauda Abdullahi Kahutu (Rarara), ta ba da N200,000;

9. Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano, ƙarƙashin Shugaban ta Alhaji Abba El-Mustapha, ta sayi kwafe biyu kan N50,000;

10. Gidauniyar Ahmed Ɗangiwa daga Katsina ta ba da N50,000.

Malamin addinin Musulunci, Sheikh Ibrahim Khalil, yana jawabi

11. Wasu daga cikin tsofaffin marubuta, ciki har da Umma Sulaiman ‘Yan’awaki, Amina Hassan Abdulsalam (AHA), da Hajiya Iklima Ƙassim Musa Bichi, sun ba da N50,000;

12. Iyalan Farfesa Ibrahim Satatima, babban malami a Jami’ar Bayero, Kano, sun ba da N50,000;

13. Fitacciyar marubuciya Hajiya Fatima Ɗanbarno, ta ba da N50,000;

14. Shugaban taron, Alhaji Aminu Ladan Abubakar (Alan Waƙa), ya ba da N100,000;

15. Tsohon Shugaban Jami’ar NOUN, Farfesa Abdalla Uba Adamu, ya ba da N10,000;

16. Ƙungiyar marubuta mata ta Mace Mutum ta ba da N50,000;

17. Ƙungiyar marubuta Alƙalam, daga Kaduna, wadda Hajiya Umma Rimaye take shugabanta, ta ba da N10,000;

18. Marubuciya kuma mai fafutukar agajin talakawa, Hajiya Fauziyya D. Sulaiman, ta ba da N100,000;

19. Fitacciyar marubuciya Hajiya Maimuna Sani Beli, N30,000;

20. Fitacciyar marubuciya Hajiya Zuwairiyyah Adamu Girei, N10,000.

Wasu marubutan da suka halarci taron sun haɗa da Kabiru Yusuf Anka, Hajiya Fatima Muhammad, Hajiya Fa’iza Muhammad Sajo, Alhaji Yazid Nasudan, da Dakta Nasiru Wada Khalil.

An kuma samu wasu mutane da ƙungiyoyi da suka aiko da saƙonnin gudunmawa, yayin da sauran mahalarta suka sayi littafin kan farashin sa na N3,000 kowanne kwafe.

Furodusa Alhaji Abdul Amart Mohammed yana jawabi

Makarantar su Salma ta ɗauki nauyin karatun ta

Wani abin farin ciki da ya bayyana a taron shi ne shugabar makarantar sakandaren da Salma take karatu ta ba da sanarwar ta ɗauki nauyin karatun ta har zuwa lokacin da za ta kammala. Ta kuma bayyana cewa makarantar za ta biya mata kuɗaɗen jarabawar WAEC da NECO.

An kammala taron lafiya, sai dai cikin yanayi mai cike da jimami da tausayawa.

Har ma da jawabin godiya da aka shirya mahaifiyar Salma za ta gabatar bai samu yiwuwa ba, sakamakon yanayin kuka da alhinin ta bayan sauraron waƙar ‘yar ta.

Manyan baƙi tare da Salma Sa’eed Mailambu bayan an kammala taron
Daga hagu: Salanken Ƙasar Hausa Alhaji Abdulrahman Muhammad Mubi, Halima K/Mashi, Salma, Aminu Ala, da Alawiyya Wada Isa
Salma tare da mahalartan taron

Loading

Previous Post

Hassada da gasa ne matsalar sha’irai mata – Shamsiyya Khadimar Ma’aiki

Next Post

Sha’iri Aminu Ala ya gudanar da taron Mauludi a Kano

Related Posts

Ƙungiyar Women of Words za ta ƙaddamar da littafin ‘Mutuwar Kasko’ a yayin cika shekara biyu
Marubuta

Ƙungiyar Women of Words za ta ƙaddamar da littafin ‘Mutuwar Kasko’ a yayin cika shekara biyu

October 14, 2026
Ranar Marubuta 2026: Katsina za ta karɓi baƙuncin taron, an fara rajistar mahalarta
Marubuta

Ranar Marubuta 2026: Katsina za ta karɓi baƙuncin taron, an fara rajistar mahalarta

August 27, 2026
Ƙungiyar ANA Kano za ta horas da matasa dabarun rubuta gajerun labarai
Marubuta

Ƙungiyar ANA Kano za ta horas da matasa dabarun rubuta gajerun labarai

August 24, 2026
Taron Ranar Marubuta Hausa ta Duniya: Sanarwar Bayan Taro
Marubuta

Taron Ranar Marubuta Hausa ta Duniya: Sanarwar Bayan Taro

January 10, 2026
Taron Ranar Marubutan Hausa ta Duniya ya gabato, shirye-shirye sun kankama
Marubuta

Taron Ranar Marubutan Hausa ta Duniya ya gabato, shirye-shirye sun kankama

December 25, 2025
‎Sanata Shehu Sani ya ba gwarazan gasar Hikayata kyautar miliyan ɗaya a taron liyafa
Marubuta

‎Sanata Shehu Sani ya ba gwarazan gasar Hikayata kyautar miliyan ɗaya a taron liyafa

December 25, 2025
Next Post
Sha’iri Aminu Ala ya gudanar da taron Mauludi a Kano

Sha'iri Aminu Ala ya gudanar da taron Mauludi a Kano

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!