Kwamitin shirya taron Ranar Marubuta ta Duniya 2026 ya ba da cewa Jihar Katsina ce za ta karɓi baƙuncin taron na bana, yayin da kuma aka fara rajistar waɗanda za su halarta.
Kwamitin ya bayyana cewa sauya wurin gudanar da taron zuwa Katsina ya biyo bayan ƙoƙarin tabbatar da ingantaccen tsari da samar da wuraren da suka dace domin gudanar da taron cikin walwala.
A wata sanarwa da Jami’in Yaɗa Labarai na kwamitin, Malam Kabiru Yusuf (Anka), ya fitar, ya ce an yanke shawarar sauya wurin taron daga Kano ne saboda rashin samun masaukin da zai iya ɗaukar dukkan marubutan da za su halarta a wuri guda, tare da samun ɗakin taro a kusa.
Ya ce: “Wannan sauyi daga Kano ya faru ne saboda gaza samun gamsasshen masauki da zai ɗauki dukkanin marubuta a wuri guda, da kuma ɗakin taro a kusa wanda zai ba mu damar gudanar da taro cikin kwanciyar hankali.”
Anka ya ƙara da cewa kwamitin ya samu dukkan abubuwan da yake buƙata domin gudanar da taron a Jihar Katsina.
Sai dai ya ce har yanzu ƙofa a buɗe take ga duk wanda zai iya samar da abubuwan da kwamitin ke buƙata a Kano ko wani wuri daban da ya dace da gudanar da taron.
Haka kuma, ya bayyana cewa masu sha’awar karɓar baƙuncin taron daga Zariya sun nemi a ba su uzuri zuwa baɗi.
A halin yanzu, an riga an fara rajistar mahalarta taron, inda masu sha’awar halarta za su iya shiga shafin Ranar Marubuta domin cike bayanan rajista.
Ranar Marubuta ta Duniya wani babban dandali ne da ke haɗa marubutan Hausa daga ƙasashen Afrika da sauran sassan duniya domin musayar ilimi da ra’ayoyi, ƙara fahimtar juna da kuma ƙarfafa zumunci tsakanin marubuta.
A bara, an gudanar da taron Ranar Marubuta ɗin ne a Dutse, babban birnin Jihar Jigawa.
![]()







