A YAYIN da ya rage ƙasa da mako guda a yi babban taron Ranar Marubutan Hausa ta Duniya, shirye-shiryen bikin suna gab da kammaluwa.
Za a gudanar da taron a Manpower Development Institute da ke birnin Dutse a Jihar Jigawa.
A taron na wuni biyu, ana sa ran malamai da manazarta a kan abin da suka shafi rubutu da adabi za su gabatar da jawabai.
Cikin manyan baƙin da ake sa ran za su gabatar da jawabai akwai Farfesa Mu’azu Sa’idu Muhammad wanda ƙwararre ne a fannin rubutu, domin ya wallafa littatafai da yawa tare da ƙasidu a mujallu na ƙasa da ƙasa da kuma aikin fassara.
Haka nan za gabatar da dandali mai taken “Rubutun Zuben Hausa a Onlayin: Ina Aka Dosa?” inda za a rabe aya da tsakuwa kan abin da ya shafi rubutu a onlayin daga inda aka fito da kuma inda aka dosa.
A wannan dandalin ake sa ran masana irin su Dakta Aishatu Shehu Maimota, Dakta Abu-Ubaida Sani, Amrah Auwal Mashi, Bamai Dabuwa da Hassana Labaran Ɗanlarabawa za su jagoranta.

Haka nan za a gabatar da dandali mai taken “Rubutun Hausa a Wajen Ƙasar Hausa” inda masa a fannin, irin su Muhammad Rabi’u Abu Hidaya, Injiniya Alhaji Abdourahman Mahaman, Alhaji Sule Muhammad Adamu Sarkin Hausawan ƙasar Gini Bissau, Alhaji Muhammad Bilal da Alhaji Soulemana Yahaya za su gabatar da jawabai.
Akwai kuma wasu muhimman abubuwan da za a gabatar a lokacin taron.
Za a rufe taron a ranar 1 ga Janairu, 2026 inda kuma a ranar ne za a bayyana sakamakon gasar rubutu ta Ranar Marubutan Hausa ta Duniya.
Ana sa ran taron zai samu halartar marubuta daga sassa daban-daban na duniya.

![]()







