• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Wednesday, August 12, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Gidauniya ta ƙaddamar da littattafai biyu domin inganta rayuwar mata

by MUKHTAR YAKUBU
December 8, 2025
in Marubuta
0
Gidauniya ta ƙaddamar da littattafai biyu domin inganta rayuwar mata

Shugabar gidauniyar kuma mawallafiyar littattafan, Hajiya Mariya Inuwa Durumin Iya, tana gabatar da jawabi a taron

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

GIDAUNIYAR Wayar da Kan Mata da Cigaban Al’umma (The Foundation for Social Orientation and Gender Development) ta ƙaddamar da littattafai biyu a ranar Asabar a Kano.

Sunan littattafan ‘Abokiyar Zama’ da kuma ‘Lokaci’, waɗanda Shugabar ƙungiyar, Hajiya Mariya Inuwa Durumin Iya, ta rubuta.

An yi taron a shekaranjiya Asabar a ɗakin taro na Mahmoud Tukur da ke tsohuwar Jami’ar Bayero, Kano.

Tun da farko da yake jawabin maraba, Mataimakin Shugaban Jami’ar Khalifa Isyaka Rabi’u, Farfesa Abdurrashid Garba, ya bayyana irin gudunmawar da mata suke bayarwa a wajen cigaban al’umma a matsayin su na iyaye, don haka ba abin mamaki ba ne idan aka ce mata sun wallafa littattafai domin faɗakarwa kan cigaban rayuwa a wannan lokacin.

Ya ce samar da waɗannan littattafai da ƙungiyar ta yi wani abin alfahari ne.

Ya ci gaba da cewa, “Babu shakka, wannan aiki da gidauniyar ta yi a ƙarƙashin shugabancin Hajiya Mariya Inuwa Durumin Iya ya zo a daidai lokacin da ya dace.

“Wannan ya sa da aka zaɓe ni a matsayin mai gabatarwa na ga ya dace na zo na bayar da tawa gudunmawar, domin a hadu cikin aikin alheri da ni.

“Kuma waɗannan littattafai da Hajiya Mariya Inuwa Durumin Iya ta fitar zai amfanar da yaran mu, musamman mata da ake shirin yi musu aure. Saboda ko a al’adance mata an nuna musu kishiya ba abar ƙauna ba ce, wannan ya sa ko a wasan ‘yartsana da yara suke yi ba za ka ji an kawo maganar kishiya ba.

“To ita wannan marubuciya ta yi magana a kan zama da kishiya don haka ta yi littafi mai suna ‘Abokiyar Zama’, ka ga a nan ba ta kira ta da kishiya ba sai ta kira ta da abokiyar zama.

“Littafi na biyu kuma, ‘Lokaci’, an yi bayani ne kan muhimmancin yin amfani da lokaci a rayuwa, wanda shi muka rasa a yanzu don haka muke tafiya cikin rashin tsari.

“Don haka ina fatan za a yi amfani da abubuwan da littattafan suka ƙunsa idan an karanta domin samar da sabuwar rayuwa mai ɗorewa.”

Mahalarta a zauren taron

Da take nata jawabin, shugabar gidauniyar kuma mawallafiyar littattafan, Hajiya Mariya Inuwa Durumin Iya, ta bayyana dalilin ta na kafa gidauniyar tun a shekara ta 2020 saboda kishin da take da shi game da rayuwar mata, musamman marayu da masu ƙaramin ƙarfi.

Ta ce: “Tun daga kafuwar gidauniyar an samar da hanyoyin samun sauƙi ga rayuwar mata da yara ta hanyar koya musu sana’a da ba su jari ɗaukar nauyin marasa lafiya

“Saboda neman hanyoyin da za mu faɗaɗa ayyukan gidauniyar ne muka ga ya dace mu samar da waɗannan littattafai, ‘Abokiyar Zama’ da ‘Lokaci’, domin wayar da kan al’umma.

“Ta gefe guda kuma mu ƙaddamar da littattafai da kuma gidauniyar ta yadda za mu samar da kuɗaɗen da za mu ci gaba da taimaka wa mabuƙata saboda da muna da su masu yawa, kuma a kullum sai ƙaruwa suke yi.

“Muna fatan za mu samu goyon bayan ku wajen bayar da gudunmawa a game da ayyukan da muka sa a gaba.”

A nata jawabin, babbar mai ƙaddamarwa, Shugabar Ƙaramar Hukumar Tudun Wada, kuma shugabar Ƙungiyar Shugabannin Ƙananan Hukumomi ta Jihar Kano, Hajiya Sa’adatu Salisu Yusha’u Soja, ta bayyana farin cikin ta game da ayyukan gidauniyar.

Ta ce: “Na tsaya ina gabatar da jawabi a wannan taron ne a matsayi na na mace ba na Shugabar Ƙaramar Hukumar Tudun Wada ba, domin wannan taron abin da ya kawo ni, na ji za a yi magana ne a kan abin da ya shafi mata da hanyar taimaka musu. Domin ni kai na abin bayar da misali ce, shi ya sa na tabbatar na ga na zo wajen wannan taron.”

Ta ci gaba da cewa, “Shi bayar da ilimi ga ‘ya mace abu ne mai matuƙar muhimmanci, domin idan tana da yara goma ka ba ta ilimi, to ka ba su duka, saboda ita ce ta fi kusa da su. Kuma idan ‘ya ce kake da ita ka ba ta ilimi, za ta je ta yi aure ta haifi yara kuma ta ba su ilimi, don haka bayar da ilimi ga mata na addini da na boko wani abu ne da ya zama wajibi a wannan lokacin.

Babbar mai ƙaddamarwa, Hajiya Sa’adatu Salisu Yusha’u Soja, tana gabatar da nata jawabin a taron

“Ilimin addini shi ne yake ƙarfafa na boko, don idan mace tana da ilimin boko ba ta da na addini, sai ka ga rayuwar ta akwai naƙasu a ciki, saboda shi ilimin addini shi ne yake saita rayuwar mutum.

“Don haka iyaye mata ina kira a gare ku da ku mayar da hankali wajen neman ilimi saboda shi ne zai ceci rayuwar ku, ba don komai ba saboda yanzu yanayi ya sauya, abubuwan da maza suke yi na ɗaukar nauyin gida a yanzu wasu sun gaza, don haka a yanzu an sakar wa mata abubuwa da dama, ta yadda a yanzu mace ita za ta dafa wa yara abinci, ta kai su makaranta, idan kayan yaro ya yage ke za ki gyara, idan kayan makaranta ya mutu ke za ki san yadda za ki ɗinka masa sabo; ko kuɗin makaranta aka turo yaro gidan ba za a nemi uba ba, uwa za a nema.

“Don haka ya kamata mata su tashi domin kula da harkokin gida sun koma hannun su, to dole a nemi ilimi kuma a nemi sana’ar da za ta rufa muku asiri ke da yaran ki don kada su tashi cikin wani halin da ba za su amfane ki ba, ba za su amfani kan su ba. Don a yanzu ko da auren ‘ya mace ne idan ya tashi, abin da uba zai yi shi da dangin sa shi ne kawai ya yi kayan gado, kuma wannan abin da zai yi za ki ga kuɗi ne da gidan miji suka kawo a matsayin dukiyar aure da shi za a haɗa a saya mata gado, sauran kayayyaki masu yawa an bar wa uwa da dangin ta.

“Haka nan idan an yi aure, ba ta da lafiya, uwa ce ke kula da ita, haka idan haihuwa ta yi da sauran wahalhalu.

“Don haka ya zama wajibi iyaye su tashi tsaye wajen neman ilimi da kiyon sana’ar da za samu hanyar dogara da kan su ba tare da sun jira maigida ya kawo ba.

“Don haka ina goyon bayan wannan gidauniya da kuma ayyukan ta.

“Don haka a matsayi na na Shugabar Ƙungiyar Shugabannin Ƙananan Hukumomin Jihar Kano, kowacce ƙaramar hukuma cikin ƙananan hukumomi 44 da muke da su kowacce za ta sayi kwafen littattafai goma a kan dubu ɗari domin bayar da tamu gudunmawar ga ayyukan ta.”

An dai tara kuɗaɗe masu yawa wanda ƙungiyoyin mata da jami’an gwamnati da sauran al’umma suka saya domin bayar da tasu gudunmawar ga cigaban ayyukan gidauniyar.

Loading

Previous Post

Darakta a Kannywood, Balarabe Murtala Baharu zai yi bikin auren da ɗan sa ranar Asabar

Next Post

Ciroma ya yi murabus daga muƙamin ƙungiyar KAFIGAN

Related Posts

Taron Ranar Marubuta Hausa ta Duniya: Sanarwar Bayan Taro
Marubuta

Taron Ranar Marubuta Hausa ta Duniya: Sanarwar Bayan Taro

January 10, 2026
Taron Ranar Marubutan Hausa ta Duniya ya gabato, shirye-shirye sun kankama
Marubuta

Taron Ranar Marubutan Hausa ta Duniya ya gabato, shirye-shirye sun kankama

December 25, 2025
‎Sanata Shehu Sani ya ba gwarazan gasar Hikayata kyautar miliyan ɗaya a taron liyafa
Marubuta

‎Sanata Shehu Sani ya ba gwarazan gasar Hikayata kyautar miliyan ɗaya a taron liyafa

December 25, 2025
Ban san farin ciki yana hana barci ba sai da aka ce ni ce ta ɗaya a gasar Hikayata – Fadila Lamiɗo
Marubuta

Ban san farin ciki yana hana barci ba sai da aka ce ni ce ta ɗaya a gasar Hikayata – Fadila Lamiɗo

December 24, 2025
Buri na shi ne saƙonnin da suke cikin rubutu na su zama masu tasiri ga al’umma – Hauwa Shehu
Marubuta

Buri na shi ne saƙonnin da suke cikin rubutu na su zama masu tasiri ga al’umma – Hauwa Shehu

December 19, 2025
Karatu yana gina tunani da halayya – marubuciyar ‘Rufaffen Duma’, Ummulkhari Sani Panisau
Marubuta

Karatu yana gina tunani da halayya – marubuciyar ‘Rufaffen Duma’, Ummulkhari Sani Panisau

November 1, 2025
Next Post
Ciroma ya yi murabus daga muƙamin ƙungiyar KAFIGAN

Ciroma ya yi murabus daga muƙamin ƙungiyar KAFIGAN

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!