ƘUNGIYAR mata marubuta masu rubutu a kafafen intanet, mai suna Women of Words Writers Association, ta shirya gudanar da taron ƙaddamar da littafin Mutuwar Kasko, tare da bikin cika shekaru biyu da kafuwar ta.
A cikin wata takardar gayyata da ƙungiyar ta aika wa mujallar Fim, ta bayyana cewa za a gudanar da taron ne a ranar Lahadi, 18 ga Oktoba, a ɗakin taro na Gidan Mambayya da ke unguwar Gwammaja, a cikin birnin Kano.
Za a gudanar da taron da misalin ƙarfe 11:00 na safe
Sanarwar ta bayyana cewa Alhaji Ado Ahmad Gidan Dabino, MON, shi ne zai jagoranci taron a matsayin shugaban taro, yayin da mawaƙi Aminu Ladan Abubakar (Aminu Ala) zai kasance uban taron.
Haka kuma, Shugaban Hukumar Tarihi da Al’adu ta Jihar Kano, Arc. Ahmad Abba Yusuf, zai halarci taron a matsayin babban baƙo na musamman, yayin da Alhaji Aminu Ahmad Saddiq zai kasance mai masaukin baƙi.

Daga cikin manyan baƙin da ake sa ran za su halarci taron akwai Farfesa Abdalla Uba Adamu, Hajiya Bilkisu Shehu Maimota, Arc. Aminu Abubakar Dabo, Alhaji Nura Adamu Ahmad da Injiniya Shammilu Abdulƙadir Isah.
Taron na zuwa ne a daidai lokacin da ƙungiyar ke bikin cika shekaru biyu da kafuwa, lamarin da ya sa ake kallon sa a matsayin wani muhimmin mataki wajen bunƙasa harkokin rubuce-rubuce da ƙarfafa gudunmawar marubuta mata a soshiyal midiya.
A saboda haka, shugabannin ƙungiyar sun yi kira ga al’umma, musamman masu sha’awar adabi da rubuce-rubuce, da su halarci taron domin ba da goyon baya ga ƙungiyar da kuma marubutan littafin Mutuwar Kasko.
![]()







