• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Saturday, October 31, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Sha’iri Aminu Ala ya gudanar da taron Mauludi a Kano

by MUKHTAR YAKUBU
September 1, 2026
in Addini
0
Sha’iri Aminu Ala ya gudanar da taron Mauludi a Kano

Sarkin Adabin Ƙasar Hausa, Alhaji Aminu Ladan Abubakar (Ala), yana gudanar da taron Maulidi a Kano a ranar 27 ga Agusta, 2026

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

FITACCEN mawaƙi kuma Sarkin Adabin Ƙasar Hausa, Alhaji Aminu Ladan Abubakar (Ala), ya gudanar da taron Mauludin da ya saba shiryawa a duk shekara domin tunawa da murnar zagayowar watan haihuwar Manzon Allah (S.A.W.).

An gudanar da taron ne a ranar Alhamis, 27 ga Agusta, a Taskar Ala, da ke Titin Gidan Zoo a cikin birnin Kano.

Taron ya samu halartar manyan malamai, jarumai da kuma shahararrun mawaƙa, waɗanda suka gabatar da jawabai da waƙoƙin yabon Manzon Allah (S.A.W.).

Da yake jawabi kan dalilin shirya taron, Ala ya bayyana cewa taron wani muhimmin al’amari ne da suka saba gudanarwa a Taskar Ala duk shekara idan watan Mauludi ya kama.

Aminu Ala tare da sauran mahalartan taron

Ya ce manufar taron ita ce ƙarfafa zumunci da haɗa kan jama’a, tare da gudanar da karatun Alƙur’ani Mai Tsarki da kuma yabon Manzon Allah (S.A.W.), domin tunawa da wannan wata mai albarka.

A cewar sa, babu wani abu da ya fi dacewa Musulmi su riƙa yi kamar yawaita ambaton Manzon Allah (S.A.W.), kasancewar sa mafi daraja cikin halittun Allah.

Ya ce: “Mu a matsayin mu na Musulmi, babu abin da ya fi ambaton Manzon Allah (S.A.W.) muhimmanci a gare mu, domin shi ne mafi daraja cikin dukkan halittun Allah.

“Saboda haka ne muke haɗuwa domin tunatar da juna game da haƙurin Manzon Allah (S.A.W.), da kyautatawar sa ga masu ƙaramin ƙarfi da kuma sauran kyawawan halayen sa, domin shi ne babban abin koyi a gare mu.

“Muna fatan wannan haɗuwa tamu za ta amfani juna wajen koyon kyawawan ɗabi’u da halayen Manzon Allah (S.A.W.).

Matan Aminu Ala, wato Alawiyya Babba (a hagu) da Alawiyya Ƙarama, suna yi masa liƙi
Dandazon mahalarta taron Mauludin

Shi ma da yake jawabi, jarumin masana’antar Kannywood, Nura Hussaini, ya ja hankalin Musulmi kan muhimmancin riƙo da sunnar Manzon Allah (S.A.W.) da kuma yin koyi da shi a dukkan al’amurran rayuwa.

Ya yi kira ga mawaƙa da masu shirya waƙoƙin yabon Manzon Allah (S.A.W.) da su riƙa kula da irin kalaman da suke amfani da su, domin su kasance masu sauƙin fahimta ga masu sauraro.

A cewar ta sa, ya kamata masu waƙoƙin yabon Manzon Allah (S.A.W.) su guji amfani da kalaman da za su rikitar da jama’a, su kuma riƙa amfani da lafuzza masu kyau da hikima, kasancewar Manzon Allah (S.A.W.) ya gudanar da kira cikin hikima da kyawawan kalamai.

A yayin taron, Malam Hussaini Ladan Abubakar ya karanta ‘Ziyara Ga Manzon Allah (S.A.W.)’, yayin da sauran mawaƙa suka nishaɗantar da mahalarta taron da waƙoƙin yabo da ambaton kyawawan halayen Manzon Allah (S.A.W.).

Daga cikin fitattun sha’iran da suka halarci taron akwai Malam Kabiru Maulana Shalelen Waƙa, Sarkin Sha’iran Gezawa, tare da tawagar sa, da Zainab Wudil, Auwalu Lale Sayyadi, Suraj Gombe, da sauran mawaƙa.

Taron dai ya kasance wata dama ta haɗuwar masoya da mawaƙan yabon Manzon Allah (S.A.W.), inda aka yi addu’o’i da tunatarwa kan muhimmancin yin koyi da kyawawan halaye da koyarwar Annabi Muhammad (S.A.W.).

Alhaji Aminu Ala da wasu sha’irai a taron

Loading

Tags: Aminu Ladan Abubakar AlaKanoMaulidiNura Hussainisha'irai
Previous Post

Taron gabatar da littafin waƙoƙin Salma ɗiyar marubuciya Halima K Mashi ya rikiɗe zuwa yanayin jimami, mahalarta sun zubar da hawaye

Next Post

Sha’irai sun baje koli a taron Mauludi da ƙungiyar Triple R Kannywood ta yi a Kano

Related Posts

Mahmud Nagudu zai gabatar da taron Mauludi ranar Lahadi
Addini

Mahmud Nagudu zai gabatar da taron Mauludi ranar Lahadi

October 1, 2026
HOTUNA: Taron Mauludi na Sayyada Raihan Imam Ahmad Ƙamshi
Addini

HOTUNA: Taron Mauludi na Sayyada Raihan Imam Ahmad Ƙamshi

September 6, 2026
Yadda Sayyada Raihan Ƙamshi ta gudanar da taron Mauludi a Kano
Addini

Yadda Sayyada Raihan Ƙamshi ta gudanar da taron Mauludi a Kano

September 6, 2026
Sha’irai sun baje koli a taron Mauludi da ƙungiyar Triple R Kannywood ta yi a Kano
Addini

Sha’irai sun baje koli a taron Mauludi da ƙungiyar Triple R Kannywood ta yi a Kano

September 2, 2026
Jaruma Raihan Imam da Triple R Kannywood za su yi tarurrukan Mauludi a Kano
Addini

Jaruma Raihan Imam da Triple R Kannywood za su yi tarurrukan Mauludi a Kano

August 30, 2026
Nafisa ‘yar tsohuwar jarumar Kannywood Fati Sulaiman ta yi bikin kammala haddar Alƙur’ani
Addini

Nafisa ‘yar tsohuwar jarumar Kannywood Fati Sulaiman ta yi bikin kammala haddar Alƙur’ani

June 29, 2026
Next Post
Sha’irai sun baje koli a taron Mauludi da ƙungiyar Triple R Kannywood ta yi a Kano

Sha'irai sun baje koli a taron Mauludi da ƙungiyar Triple R Kannywood ta yi a Kano

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!