Ƙungiyar Triple R Kannywood, ƙarƙashin jagorancin fitaccen mawaƙi Dauda Kahutu (Rarara), ta gudanar da taron Mauludi a Kano domin murnar zagayowar watan haihuwar Annabi Muhammadu (S.A.W.).
Taron, wanda aka gudanar a ranar Laraba, 2 ga Satumba, a wani rufaffen ɗakin taro da ke Kasuwar Baje-koli, a kan Titin Gidan Zoo a Kano, ya samu halartar manyan malamai, mawaƙa da masu shirya waƙoƙin yabo, da kuma jaruman masana’antar Kannywood.
Da yake jawabi bayan buɗe taron da addu’a, shugaban ƙungiyar Triple R Kannywood, fitaccen jarumi kuma furodusa Alhaji Lawan Ahmad, ya bayyana cewa manufar shirya taron ita ce haɗa kan al’ummar Musulmi domin taya juna murnar zagayowar watan da aka haifi fiyayyen halitta, Annabi Muhammadu (S.A.W.).

Ya ce, “Manufar shirya wannan taro ita ce mu haɗu domin taya juna murnar zagayowar wannan wata na haihuwar Manzon Allah (S.A.W.). Don haka ne muka gayyaci al’ummar Musulmi domin mu haɗu mu taya juna murnar wannan wata mai albarka, wanda a cikin sa ne aka haifi fiyayyen halitta, Annabi Muhammad, Manzon Allah, ɗan Abdullahi.”
Lawan ya ƙara da cewa daga cikin abubuwan da aka tsara gudanarwa a taron akwai sauraron jawabai daga malamai, tare da bai wa mawaƙa da masu shirya waƙoƙin yabon Manzon Allah damar gabatar da waƙoƙin su.


Ya ce, “Bayan malamai sun kammala jawaban su, za mu bai wa mawaƙa dama su gabatar da waƙoƙin yabon Manzon Allah (S.A.W.) har zuwa lokacin da za mu tashi daga taron. Muna fatan za mu gudanar da taron lafiya, kuma mu tashi lafiya.”
Daga nan sai aka gabatar da Sheikh Bazallah Sheikh Muhammad Nasiru Kabara, wanda ya gabatar da wa’azi kan rayuwa da koyarwar Manzon Allah (S.A.W.).

Malamin ya yi bayani mai tsawo kan haƙuri da kyawawan halayen Manzon Allah (S.A.W.), da yadda yake mu’amala da sahabban sa.
Sheikh Bazallah ya kawo darussa daga Yaƙin Uhudu, inda ya bayyana yadda rashin bin umurnin Manzon Allah (S.A.W.) ya haifar da sauyin al’amura a lokacin yaƙin.
Ya yi kira ga al’ummar Musulmi da su dage wajen bin umurnin Manzon Allah (S.A.W.) tare da riƙo da koyarwar sa a dukkan fannoni na rayuwa.
Haka kuma ya jaddada muhimmancin yafiya, haƙuri da juna, da kyautata dangantaka tsakanin Musulmi, kamar yadda koyarwar Manzon Allah (S.A.W.) ta tanada.

Bayan kammala wa’azin ne aka fara ba mawaƙa da sha’irai fili suka riƙa gabatar da waƙoƙin yabon Manzon Allah (S.A.W.). Sun haɗa da Bashir Ɗandago, Jamilu Ƙofar Waika, Ahmad Gwangwazo, Mai Tajul-Izzi, Hafiz Abdallah, da sauran su.
Dauda Rarara ne ya rufe taron da waƙoƙin yabon Manzon Allah (S.A.W.), yayin da matar sa, Sayyada Aisha Ahmad Idris (Ayshatulhumaira), tana yi masa amshi.
Taron na yini guda ne, inda aka fara shi daga ƙarfe 10 na safe aka gama da misalin ƙarfe 7 na yamma.



![]()







