FITACCIYAR marubuciyar littattafan Hausa kuma shugabar cibiyar magunguna ta Aunty Baby Women Counselling and Consultation Centre, Hajiya Umma Sulaiman ’Yan’awaki (Aunty Baby) ta yi bikin zagayowar ranar haihuwar ta, sakamakon ta cika shekaru 51 a duniya.
Marubuciyar ta shirya wani taron liyafa na musamman a gidan ta da ke Unguwar Samegu, cikin birnin Kano, domin murnar wannan rana tare da ’ya’yan ta da jikokin ta.
A yayin taron, an ga jikokin ta cikin annashuwa, suna wasa da dariya cikin farin ciki, yayin da iyalai suka gudanar da bikin cikin yanayi na nishaɗi da godiya ga Allah.

A ranar Asabar, 15 ga Agusta, 2026, Hajiya Umma ta wallafa hotunan bikin a shafukan ta na sada zumunta, inda ’yan’uwa, abokan arziki da masoyan ta suka yi mata addu’ar fatan alheri da samun nasara a rayuwar ta cikin shekaru masu zuwa.
Da take ƙarin bayani ga wakilin mu kan bikin, Hajiya Umma ’Yan’awaki ta bayyana farin cikin ta da samun damar kai wa wannan matsayi na rayuwa, tana mai cewa babban abin godiyar ta shi ne yadda Allah ya azurta ta da ’ya’ya da jikoki, tare da ba ta damar hidimtawa al’umma.
Ta ce: “Alhamdu lillah, ina godiya ga Allah da Ya nuna mini wannan rana. Yau na cika shekaru 51 a duniya. Allah ya yi mini arzikin ’ya’ya da jikoki, kuma ga shi muna cikin rufin asirin Ubangiji.
“Babbar nasarar da na samu a rayuwa ta ita ce baiwar da Allah ya yi mini ta samun damar hidima ga marayu, marasa lafiya da masu ƙaramin ƙarfi.
“Ya Allah, na gode maka. Allah Ka kula da mu, Ka sa hidimar da muke yi ta zama saboda Kai. Don alfarmar shugaban mu, Muhammadu Manzon Allah (SAW).”


![]()







