FITACCEN jarumin masana’antar Kannywood, Alhaji Tijjani Usman, wanda aka fi sani da Tijjani Faraga, ya aurar da ‘yar sa ta biyu, Rabi’atu Tijjani Usman Faraga (Ummi), a wani biki da aka gudanar a ranar Asabar a Jos, Jihar Filato.
An ɗaura auren Rabi’atu da angon ta, Malam Aliyu Idris Abdullahi, da misalin ƙarfe 11:00 na safe a gidan marigayi babban limamin garin Jos, Sheikh Lawal Adam, bisa sadakin naira 300,000.
Bayan kammala ɗaurin auren, an gudanar da walimar liyafa a gidan iyalan ango, inda baƙi da dama suka halarta domin taya ma’auratan murnar fara rayuwar aure.
Daga cikin fitattun ‘yan Kannywood da suka halarci bikin akwai Al-Amin Buhari, Isma’il Daddy, Oshere, da Abubakar S. Garba.
Haka kuma, Babban Sakataren Hukumar Tace Finafinai da Ɗab’i ta Jihar Kano, Abba El-Mustapha, ya aike da wakilai domin wakiltar sa a wajen bikin. Shi ma mai bai wa Gwamnan Jihar Kano shawara kan harkokin matasa da wasanni, Alhaji Sani Musa Danja, ya tura wakilai tare da isar da saƙon taya murna ga iyalan amarya da ango.

A cewar mujallar Fim, Tijjani Faraga ya bayyana godiyar sa ga dukkan waɗanda suka halarci ɗaurin auren, da waɗanda suka tura wakilai, tare da waɗanda suka taya iyalan sa murna ta hanyar addu’o’i da saƙonnin fatan alheri.
An yi wa ma’auratan addu’ar Allah ya ba su zaman lafiya, soyayya mai ɗorewa da zuri’a ɗayyiba.

![]()







