MATASHIN furodusa, kuma tsohon ma’aikacin mujallar Fim, Malam Isah Bawa Doro, zai angwance a Katsina jibi Asabar.
Za a ɗaura auren Isah Bawa da santaleliyar amaryar sa Nafisa Suleiman da misalin ƙarfe 1:10 na rana, a masallacin Bilal Ibn Rabah da ke WTC Roundabout, a cikin birnin Katsina.
A wani ɓangare na shirye-shiryen wannan biki, an shirya gudanar da gasar ƙwallon ƙafa a yau, Alhamis, 26 ga Nuwamba a Continental Sports and Events Centre, da ke bayan Katsina City Mall, Katsina.
Gasar za ta haɗa ƙungiyoyi takwas da za su fafata domin neman kofin gasar. A wasan farko, Gwagware Film Makers za ta kara da Doro Dynamic da ƙarfe 5:00 na yamma, yayin da Almu Family za ta fafata da Katsina Government House da ƙarfe 5:20.
Haka kuma, Matazu FC za ta kara da Wazirin Tinubu FC da ƙarfe 5:40, sai Mai Kwashewa da Gwagware Modern Singers da ƙarfe 6:00 na yamma.
Bayan kammala wasannin farko, za a buga wasan kusa da na ƙarshe guda biyu. Na farko zai gudana da ƙarfe 6:30, yayin da na biyu zai gudana da ƙarfe 7:00. Daga nan ne za a buga wasan ƙarshe da ƙarfe 7:30 na yamma domin zaƙulo zakaran gasar.
A gobe Juma’a, 27 ga Nuwamba, kuma an tsara gudanar da dina da ƙarfe 8:00 na dare, sai dai ba a bayyana ɗakin taron da za a gudanar da bikin ba.
Isah Bawa Doro, wanda ya shahara a fannin shirya finafinai na Kannywood, tsohon ma’aikacin mujallar Fim ne, kuma auren sa da Nafisa Suleiman na daga cikin muhimman abubuwan da ake gudanarwa a Kannywood a wannan ƙarshen mako.
![]()






