MARUBUCIN finafinai kuma tsohon Sakataren Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a na ƙungiyar Tripple R Kannywood, Malam Ibrahim Birniwa, ya bayyana ficewar sa daga ƙungiyar siyasa da mawaƙi Dauda Kahutu Rarara yake jagoranta, tare da yin murabus daga muƙamin sa.
Ficewar Birniwa na zuwa ne bayan wasu fitattun membobin ƙungiyar, ciki har da Mansurah Isah da marubuci Abdulkareem Papalaje, sun ba da sanarwar barin tafiyar a kwanakin baya.
Birniwa ya bayyana murabus ɗin sa ne ta hanyar wani saƙo da ya wallafa a shafin sa na soshiyal midiya.
A wata tattaunawa da ya yi da mujallar Fim, Birniwa ya ce dalilai da dama ne suka sa ya yanke shawarar ficewa, amma babban abin da ya fi damun sa shi ne yadda ake gudanar da ƙungiyar.
A cewar sa, ƙungiyar ba ta da ingantaccen tsari na shugabanci, domin duk da kasancewar akwai shugabanni da sakatare, babu wanda ke da ikon yanke hukunci face Rarara.
“Ƙungiyar kamar ta mutum ɗaya ce. Duk abin da za a yi sai Rarara ya amince, kuma babu wani da ke da ikon yanke hukunci ko gudanar da aiki ba tare da shi ba,” inji Birniwa.
Ya ce wani abin da ya ƙara tabbatar masa da hakan shi ne yadda aka gudanar da wani al’amari bayan tawagar ƙungiyar ta je Jihar Gombe domin wani aiki.
A cewar sa, shi da wasu mambobi sun samu wani muhimmin aiki a Abuja, inda suka sanar da shugaban ƙungiyar da sakataren ta kafin su bar Gombe zuwa Abuja. Sai dai, duk da sanarwar da suka bayar, daga baya aka ɗauki matakin da ya nuna kamar sun aikata laifi.
Birniwa ya ce hakan ya nuna cewa ba a mutunta shugabannin ƙungiyar ko tsarin gudanarwa, lamarin da ya sa ya fara ganin babu adalci a tafiyar.
Ya kuma bayyana cewa tun kafin kafuwar Tripple R Kannywood, wasu daga cikin membobin ƙungiyar suna gudanar da wata tafiya ta daban, amma daga baya aka nemi su dakatar da ita.
A cewar sa, Mansurah Isah ta ƙi amincewa da hakan, inda ta fi zaɓar ficewa daga Tripple R Kannywood maimakon ta yi watsi da aikin da ta fara tun da farko.
Birniwa ya ce irin waɗannan abubuwa ne suka nuna masa cewa ana tafiyar da ƙungiyar ne bisa ra’ayin mutum ɗaya, ba bisa ƙa’ida da tsarin shugabanci ba.
Da yake bayyana dalilin da ya sa ya ce Rarara ya fi jam’iyyar APC rashin karɓuwa a idon jama’a, Birniwa ya ce salon jagorancin Rarara yana janyo wa masu tallata jam’iyyar ƙiyayya daga al’umma.
“A halin da ake ciki yanzu, kafin Rarara ya jawo mutum ya zaɓi APC, zai iya sa wanda yake son zaɓen ta ya fasa. Saboda yadda yake tafiyar da al’amurra ne ya sa mutane suke kallon ƙungiyar da mummunan ido,” inji shi.
Ya ƙara da cewa siyasa tana buƙatar lallashi, wayar da kai da kuma bayyana manufofin gwamnati cikin hikima, maimakon tilastawa ko amfani da salon da zai fusata jama’a.
A cewar sa, gwamnatin APC tana da wasu nasarori da ya kamata a bayyana wa jama’a cikin natsuwa, amma ya yi zargin cewa salon Rarara ya sa saƙonnin ba sa isa yadda ya kamata.
Birniwa ya ce wannan ne ya sa ya ga ya fi dacewa ya sauka daga muƙamin sa tare da ficewa daga ƙungiyar domin ya ci gaba da harkokin sa.
Ya kuma yi iƙirarin cewa akwai wasu manyan membobin ƙungiyar da su ma za su bayyana ficewar su nan gaba kaɗan.
“Na ga canza hanya shi ne mafita. Ba zan ci gaba da kasancewa cikin tsarin da ba ya mutunta ra’ayin mutane ba. Na rubuta takardar murabus daga muƙami na na Sakataren Yaɗa Labarai kuma na fice daga ƙungiyar. Ina kuma ganin akwai wasu manyan jiga-jigan da za su biyo baya nan gaba kaɗan,” inji Birniwa.
![]()







