• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, October 13, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Ƙungiya ta kai ƙorafi kan shirin ‘Labarina’ zuwa ga gwamnati kan yana ɓata sunan Hausawa

by MUKHTAR YAKUBU
July 2, 2026
in Labarai
0
Ƙungiya ta kai ƙorafi kan shirin ‘Labarina’ zuwa ga gwamnati kan yana ɓata sunan Hausawa

Malam Aminu Saira, Babban Furodusan 'Labarina'

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

WATA ƙungiya da ke garin Funtuwa a Jihar Katsina mai suna Hausawa Development Association for Peace and Unity ta kai ƙorafi ga Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano kan shirin ‘Labarina’ zango na 15, tana zargin cewa shirin yana zubar da mutuncin al’ummar Hausawa.

Ƙorafin yana ƙunshe ne cikin wata wasiƙa da lauyan ƙungiyar, Abubakar Abdulsalam, na ofishin A.A. Zangon Marke & Co. Karaduwa Law Chambers, GRA, Funtua, ya aike wa Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano a ranar 30 ga Yuni, 2026.

Wasiƙar mai taken “Matsaya da Ƙorafi a Kan Shirin Labarina Season 15 Tare da Sanarwa Kafin Shigar da Ƙara” ta bayyana cewa lauyoyin suna wakiltar ƙungiyar ne bisa zargin shirin yana nuno Hausawa a matsayin marasa addini, masu aikata manyan laifuka, kuma marasa tarbiyya.

Ƙungiyar ta buƙaci hukumar da ta sake nazarin shirin tare da umurtar masu shirya shi da su cire ko su gyara sassan da take ganin sun saɓa wa ƙa’idojin tantance finafinai.

Haka kuma, ta bai wa hukumar wa’adin makonni biyu da ta ɗauki matakin da ya dace, tana mai gargaɗin cewa idan ba a yi hakan ba za ta bi hanyoyin shari’a domin neman mafita.

Takardar ƙorafin daga lauyoyin ƙungiyar Hausawan

A ƙoƙarin jin ta bakin mai shirya shirin, Malam Aminu Saira, Mujallar Fim ta yi ƙoƙarin tuntuɓar sa ta waya amma ba a samu nasarar yin magana da shi ba.

Sai dai ɗaya daga cikin na kusa da shi, Ahmad Nagudu, ya shaida wa Mujallar Fim cewa ya ga kwafen wasiƙar bayan an turo masa ta manhajar WhatsApp, kuma ya nuna wa Saira ɗin.

A cewar sa, Saira bai karɓi kwafen wasiƙar kai tsaye ba, kuma ba su da tabbacin ko an kai masa gida ne ba a same shi ba, kasancewar a halin yanzu yana cikin gudanar da ayyukan sa.

Nagudu ya ƙara da cewa tun da ta hannun lauyoyi aka aika da wasiƙar, kamfanin Saira Movies ma yana da nasa lauyoyin da za su bi lamarin ta hanyar doka idan buƙatar hakan ta taso.

Loading

Tags: Ahmad NaguduAminu SairaFuntuwaHausawaHukumar Tace Finafimai ta Jihar KanoƙorafiLabarinaSaira Movies
Previous Post

Marubucin finafinai, Ibrahim Birniwa ya fice daga tafiyar Rarara, ya ce “Rarara ya fi APC baƙin jini”

Next Post

Ƙungiyar Rarara ta ɗauki nauyin aikin ƙanwar jaruma Fati Al-Amin a asibiti

Related Posts

Hukumar Tace Finafinai ta karɓi uzirin Tijjani Gandu
Labarai

Hukumar Tace Finafinai ta karɓi uzirin Tijjani Gandu

October 6, 2026
Tinubu da Remi sun halarci bikin fara nuna fim kan gwagwarmayar Abiola
Labarai

Tinubu da Remi sun halarci bikin fara nuna fim kan gwagwarmayar Abiola

October 1, 2026
Cewar Ability: Ba mu kafa KAFIGAN don sharholiya a Kannywood ba
Labarai

Za a ƙaddamar da reshen Kaduna na KAFIGAN ranar Asabar

October 1, 2026
Zaɓen 2027: Shettima ya nemi goyon bayan ‘yan fim da mawaƙan Arewa wajen sake zaɓen Tinubu
Siyasa

Zaɓen 2027: Shettima ya nemi goyon bayan ‘yan fim da mawaƙan Arewa wajen sake zaɓen Tinubu

September 30, 2026
Ina roƙon Rarara ya saka ni cikin ‘Triple R’ domin in samu na abinci – Baba Duduwa
Siyasa

Ina roƙon Rarara ya saka ni cikin ‘Triple R’ domin in samu na abinci – Baba Duduwa

September 30, 2026
Guguwar zaɓen 2027: Sanata Barau Jibrin ya kori jaruma Rasheeda Maisa’a daga tafiyar sa
Siyasa

Guguwar zaɓen 2027: Sanata Barau Jibrin ya kori jaruma Rasheeda Maisa’a daga tafiyar sa

September 29, 2026
Next Post
Ƙungiyar Rarara ta ɗauki nauyin aikin ƙanwar jaruma Fati Al-Amin a asibiti

Ƙungiyar Rarara ta ɗauki nauyin aikin ƙanwar jaruma Fati Al-Amin a asibiti

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!