An shiga alhini a yau Lahadi, bayan samun labarin rasuwar fitaccen mawaƙin Hausa, Muhammad Buhari, wanda aka fi sani da Kosan Waƙa.
Kosan Waƙa, wanda ɗan asalin Ƙaramar Hukumar Ɓatagarawa a Jihar Katsina ne, ya rasu a yau Lahadi yana da shekaru 47 a duniya.
An gudanar da jana’izar Kosan Waƙa a mahaifar sa da ke garin Tsanni a Jihar Katsina da yammacin yau.
Shugaban jam’iyyar APC na Jihar Kano, Hon. Umar Haruna Doguwa, shi ne ya jagoranci tawagar gwamnatin Jihar Kano a madadin Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf inda suka je garin domin halartar sallar jana’iza.

Labarin rasuwar Kosan Waƙa ya fara yaɗuwa ne bayan da Shugaban Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano, Abba El-Mustapha, da wasu daga cikin abokan sana’ar sa suka tabbatar da hakan ta shafukan sada zumunta.
Kosan Waƙa, ɗan asalin Ƙaramar Hukumar Ɓatagarawa da ke Jihar Katsina, ya shahara a matsayin ɗaya daga cikin fitattun mawaƙan siyasa a Arewacin Nijeriya. Muryar sa mai armashi da salon rerawa na musamman sun sa waƙoƙin sa suka yi tasiri sosai a tsakanin jama’a, musamman a lokutan yaƙin neman zaɓe da kuma harkokin wayar da kan al’umma.
Marigayin ya yi wa fitattun ‘yan siyasa da dama waƙoƙi, amma waƙar ‘Abba Ka Cika Gwarzo’ da ya yi wa Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ta kasance ɗaya daga cikin waƙoƙin sa da suka fi shahara da karɓuwa. Haka kuma, ya yi waƙoƙi da dama da suka shafi zaman lafiya, haɗin kai, al’adu da kuma kyawawan ɗabi’u.
Rahotannin farko sun nuna cewa rasuwarsa ta girgiza masoya, abokan sana’a da sauran al’ummar da ke bibiyar harkokin waƙoƙin Hausa. Da dama sun bayyana jimamin su a shafukan sada zumunta, inda suka yi ta bayyana irin gudunmawar da ya bayar ga cigaban masana’antar waƙoƙin Hausa.

A makon da ya gabata, an ga marigayin kwance a gadon asibiti cikin mawuyacin hali, lokacin da Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya kai masa ziyarar jinya tare da yi masa addu’ar samun lafiya. Hotuna da bidiyon ziyarar sun bazu sosai a kafafen sada zumunta, lamarin da ya sa masoyan sa suka ci gaba da yi masa addu’ar samun lafiya kafin daga bisani labarin rasuwar sa ya bayyana.
A lokacin kammala wannan rahoto, ba a fitar da cikakken bayani kan musabbabin rasuwar sa ba.
Rasuwar ta zo ne a daidai lokacin da har yanzu waƙoƙin sa ke ci gaba da ɗaukar hankalin masoya, musamman matasa masu sha’awar waƙoƙin siyasa da na faɗakarwa.
Mutuwar sa ta bar babban giɓi a fagen waƙoƙin Hausa, inda masana da masoya ke ganin zai yi wuya a cike gurbin da ya bari cikin gaggawa.
Masoya, abokan sana’a da sauran al’ummar da suka san Kosan Waƙa na ci gaba da bayyana alhinin su tare da yi masa addu’ar Allah ya gafarta masa, ya jiƙan sa da rahama, Ya sanya Aljannatul Firdausi ta zama makomar sa, sannan ya ba iyalan sa, abokan sa da ɗaukacin masoyan sa haƙurin jure wannan babban rashi.
Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya bayyana matuƙar alhinin sa kan rasuwar Kosan Waƙa, inda ya bayyana shi a matsayin muryar zaman lafiya wadda ta yi amfani da waƙa wajen inganta haɗin kai, al’adu da wayar da kan al’umma.
Kosan Waƙa, wanda ɗan asalin Ƙaramar Hukumar Ɓatagarawa a Jihar Katsina ne, ya rasu a yau Lahadi yana da shekaru 47 a duniya.
A cikin wata sanarwa da Babban Sakataren Yaɗa Labarai na Gwamnan Jihar Katsina, Ibrahim Kaula Mohammed, ya fitar a ranar Lahadi, Gwamna Radda ya ce marigayin ya yi amfani da basirar sa wajen wa’azin zaman lafiya da kuma ilmantar da al’umma kan harkokin siyasa da shugabanci.
“Kosan Waƙa ya yi amfani da waƙoƙin sa wajen wa’azin zaman lafiya, inganta al’adun mu da kuma wayar da kan jama’a kan harkokin siyasa da shugabanci. Yana ɗaya daga cikin mawaƙan da na fi so tun lokacin da nake Darakta Janar na SMEDAN,” inji gwamnan.

Gwamna Radda ya ce marigayin ya halarci shirye-shirye da dama da gwamnatin Jihar Katsina ta shirya, kuma a ko da yaushe yana amfani da muryar sa wajen tallafa wa manufofin da ke ƙarfafa haɗin kan al’umma.
“Rasuwar sa babban rashi ne ga Jihar Katsina, masana’antar kiɗa da kuma dukkan mu da muka taso muna sauraron waƙoƙin sa. Za mu yi kewar kuzarin sa da kuma saƙonnin da yake isarwa ta hanyar waƙoƙin sa,” inji Raɗɗa.
Gwamnan ya yi addu’ar Allah ya gafarta wa marigayin kurakuran sa, ya kuma ba shi Aljannar Firdausi.
Haka kuma ya miƙa ta’aziyyar sa ga iyalan marigayin, al’ummar Ƙaramar Hukumar Ɓatagarawa da kuma masoyan sa a faɗin Jihar Katsina.
![]()







