FITATTUN mutane huɗu a masana’antar nishaɗi, wato Isa Bello Ja, Naziru Ahmad (Sarkin Waƙa), Hausa Guy, da Amal Umar suna daga cikin ɗimbin gwarazan da har da za karrama a bikin Henna Ball da kyaututtukan gidan talbijin na Tozali a Abuja a ranar Asabar mai zuwa, 31 ga Oktoba.
Za a gudanar da gagarumin bikin mai suna “Henna Ball and Tozali People’s Awards” karo na takwas daga ƙarfe 6:00 na yamma a gidan taruka na Los Angeles Event Centre da ke Titin Ahmadu Bello Way, a Abuja, inda masu shirya taron suka yi alƙawarin gudanar da biki da zai haɗa ba da kyaututtuka da al’adun gargajiya, ƙira da ɗinkin zamani, nishaɗi da ayyukan jinƙai.
Kamfanin Tozali Media Group ne yake shirya taron, wanda aka sanya wa taken “Ƙarfafa Wa Waɗanda Suka Tsira Gwiwa Tare Da Maido da Fata” (Empowering Survivors, Restoring Hope).
Taron na shekara-shekara yana tattaro jami’an gwamnati, sarakunan gargajiya, ’yan kasuwa, masu taimakon jama’a, ’yan jarida, masu shirya finafinai da sauran masu nishaɗantarwa, da kuma ƙungiyoyin farar hula domin karrama mutane da hukumomin da suke bayar da gudunmawa ga cigaban ƙasa da al’umma.
Daga cikin manyan baƙin da ake sa ran za su halarci taron akwai tsohuwar uwargidan shugaban ƙasa, Dakta Maryam Sani Abacha, wadda za ta kasance Uwar Ranar; Alhaji Bashir Mohammed Ɗalhatu (Wazirin Dutse) a matsayin shugaban taro kuma babban mai masaukin baƙi; da Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Al’umma, Alhaji Mohammed Idris, a matsayin babban baƙo na musamman.
Sauran manyan baƙin da ake sa ran halartar su sun haɗa da tsohuwar Ministar Harkokin Mata, A’isha Isma’il, wadda za ta gabatar da jawabin musamman, da Mai Martaba Oba na Ife, Oba Adeyeye Enitan Ogunwusi, wanda zai kasance uban taron na sarauta.
Ɗaya daga cikin manyan abubuwan da za su fito fili a wajen bikin shi ne bayar da kyaututtukan Tozali People’s Awards ga fitattun mutane da ƙungiyoyi saboda gudunmawar da suke bayarwa a fannonin shugabanci, hidimar jama’a, ayyukan jinƙai, ƙirƙire-ƙirƙire a harkokin kasuwanci da kuma ƙarfafa wa mata gwiwa.
Daga cikin waɗanda za a karrama akwai tsohuwar uwargidan shugaban ƙasa, Hajiya Turai Umaru Musa Yar’Adua, wadda za ta karɓi kyautar Tozali Woman of Distinction Award, yayin da Sarkin Ife zai karɓi kyautar Tozali Royal Leadership Award.
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, yana cikin waɗanda za su karɓi kyautar Governor of Excellence Award, yayin da takwaran sa na Jihar Taraba, Agbu Kefas, zai karɓi kyautar Champion of Women Empowerment Award.
Ministan Tsaro kuma tsohon Babban Hafsan Tsaron Nijeriya, Janar Christopher Gwabin Musa (mai ritaya), yana cikin waɗanda za a karrama da kyautar Outstanding Security Leadership Award, yayin da Abdussamad Dasuƙi zai karɓi kyautar Distinguished Legislative Award.
Sauran waɗanda za a karrama sun haɗa da Fatima Shinkafi, wadda za ta karɓi kyautar Excellence in Public Service; Gidauniyar Sir Ahmadu Bello Memorial Foundation, wadda za ta karɓi kyautar Humanitarian Excellence; da kamfanin Stonetech Square Limited, wanda zai karɓi kyautar Excellence in Business Innovation.

Sanata Datti Yusuf Baba-Ahmed, Nasiru Danu da Mohammed Bashir Ɗalhatu ma suna cikin waɗanda aka ware domin karramawa saboda gudunmawar su a fannonin shugabancin kasuwanci, ayyukan jinƙai da kuma nasarorin rayuwa.
A ɓangaren manishaɗanta, za a karrama Alhaji Isa Bello Ja da kyautar “Best Actor of the Year Award”, Amal Umar da kyautar “Best Actress of the Year”, Naziru Ahmad (Sarkin Waƙa) da kyautar “Music Artist of the Year Award”, sai Hausa Guy da Kyautar “Most Impactful Social Media Influencer Award”.
Baya ga bayar da kyaututtukan, taron zai ƙunshi bikin baje kolin kayan sawa na zamani mai suna Runway Royal Fashion Show, wanda kamfanin Mohani zai gabatar, tare da raye-raye da kiɗa, halartar fitattun mutane, shimfiɗar jan kafet, da damar tattaunawa da ƙulla hulɗa tsakanin baƙi.
A cewar masu shirya taron, bikin zai kasance wata dama ta nuna ƙwarewa, ƙirƙire-ƙirƙire da al’adun Nijeriya, tare da samar da yanayin da shugabanni da masu ruwa da tsaki daga sassa daban-daban za su haɗu su tattauna.

Sai dai masu shirya taron sun bayyana cewa babban manufar bikin ba ta tsaya ga nishaɗi da karramawa kawai ba, domin an kuma mayar da hankali kan ayyukan jinƙai, musamman taimaka wa mata da ’yan mata da suka tsira daga sacewa, ayyukan ’yan bindiga, ta’addancin Boko Haram, gudun hijira da sauran nau’o’in tashin hankali.
Ta hanyar haɗin gwiwar ta da gidauniyar Tozali Girl Child and Women Foundation, ƙungiyar na neman wayar da kan jama’a da tattara tallafi domin taimaka wa waɗanda suka tsira daga irin waɗannan matsaloli. Tallafin zai mayar da hankali kan kula da lafiyar ƙwaƙwalwa, ilimi, kiwon lafiya, ƙarfafa tattalin arziki, farfaɗowa da sake shigar da waɗanda abin ya shafa cikin al’umma.
Masu shirya taron sun ce taken “Ƙarfafa Wa Waɗanda Suka Tsira Gwiwa Tare Da Maido da Fata” yana nuna muhimmancin samar wa mata da ’yan mata masu rauni tallafi da damarmakin da za su taimaka musu wajen sake gina rayuwar su cikin mutunci.
Sun ƙara da cewa aikin kafafen yaɗa labarai bai kamata ya tsaya ga bayar da rahoton abubuwan da ke faruwa kawai ba, domin suna da rawar da za su taka wajen haɗa kan al’umma, faɗakar da shugabanni da kuma bai wa masu rauni damar bayyana halin da suke ciki domin samar da sauyi mai ma’ana a cikin al’umma.
A bikin na shekarar 2026, Trust Media Group ce babbar abokiyar hulɗar kafafen yaɗa labarai, yayin da Gidan Talbijin na Ƙasa (NTA) yake cikin abokan hulɗar yaɗa labarai. Bankin TAJBank ne abokin hulɗar banki, yayin da Mohani yake abokin hulɗar fannin kayan sawa.
Sauran abokan hulɗar yaɗa labarai na intanet sun haɗa da Northern Hibiscus, Hausa Fulani, PR Nigeria, Newspoint Nigeria, da Fim Magazine, tare da wasu kafafen yaɗa labarai da ke tallafa wa taron.
Yayin da saura kwana bakwai kafin gudanar da bikin, kamfanin Tozali Media Group ya gayyaci jami’an gwamnati, sarakunan gargajiya, shugabannin kamfanoni, abokan hulɗar cigaba, ’yan jarida da sauran al’umma da su halarci taron.
Kamfanin ya bayyana cewa bikin zai haɗa bikin murnar nasarori da sabon yunƙuri na tallafa wa mata da ’yan mata masu rauni, tare da bunƙasa ayyukan jinƙai a sassa daban-daban na Nijeriya.
![]()






