FITACCIYAR marubuciyar finafinan Hausa, Hajiya Zuwairiyyah Adamu Girei, ta zama sabuwar Manajan Daraktar gidan talbijin na Mahanga TV, wanda shahararren jarumin Kannywood, Nuhu Abdullahi, ya kafa a Kano.
An gabatar da Zuwairiyyah a wannan matsayin a wani taron miƙa mata muƙamin da aka gudanar a yau Litinin, a ofishin Mahanga TV da ke lamba 5, Titin Guda Abdullahi, a unguwar Farm Centre da ke Kano.
A yayin taron, Alhaji Nuhu Abdullahi da kan sa ne ya gabatar da ita a hukumance, lamarin da ke nuna cewa ta karɓi ragamar jagorantar harkokin gudanarwa na tashar.

Kafin wannan sabon muƙami, Hajiya Zuwairiyyah ta shafe sama da shekaru 10 tana aiki a gidan talbijin na Arewa 24, inda ta yi fice a fannin rubuta labaran finafinai. Ta kasance jagorar sashen rubutun labarin shirin ‘Daɗin Kowa’, da sauran finafinan Hausa da tashar ke samarwa.
Ficewar ta daga Arewa 24 a ƙarshen watan Oktoba da ya gabata da kuma sabon muƙamin da ta samu a Mahanga TV na nuna wani sabon babi a rayuwar ta ta sana’a, musamman a fannin shirya finafinai da gudanar da harkokin kafafen yaɗa labarai.
Ƙwararriyar marubuciya ce wadda ta taɓa yin rubutun hikaya a mujallar Fim, musamman bayan an wallafa littafin ta na farko mai suna ‘Da Ma A Ce…’
Tuni dai jama’a da dama suka aika saƙonnin taya ta murna bisa wannan sabon matsayi, tare da yi mata fatan alheri da nasara a sabon aikin da ta kama.



![]()






