• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, October 20, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Maikatanga ya shiga kwamitin alƙalan gasar Wole Soyinka ta aikin jaridar bincike

by MUKHTAR YAKUBU
October 19, 2026
in Labarai
0
Maikatanga ya shiga kwamitin alƙalan gasar Wole Soyinka ta aikin jaridar bincike

Malam Sani Mohammed Maikatanga

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

CIBIYAR Aikin Jaridar Bincike ta Wole Soyinka (WSCIJ) ta naɗa fitaccen mai ɗaukar hoton nan, Malam Sani Mohammed Maikatanga, a matsayin ɗaya daga cikin alƙalan da za su tantance ayyukan da aka gabatar domin gasar Kyautar Wole Soyinka ta Rahoton Binciken ’Yan Jarida (WSAIR) karo na 21.

Gasar, wadda ake gudanarwa a duk shekara, tana karrama ’yan jaridar Nijeriya waɗanda ayyukan su suka nuna ƙwarewa a fannin bincike, bin ƙa’idojin aikin jarida, ƙirƙira da jajircewa wajen kare muradun al’umma.

A cikin wasiƙar naɗin da Babbar Darakta kuma Babbar Jami’ar Gudanarwa ta WSCIJ, Motunrayo Alaka, ta rattaba wa hannu, ta bayyana cewa Maikatanga zai taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da sahihanci da adalci a gasar, tare da taimakawa wajen zaɓen fitattun ayyukan jarida masu zurfin bincike a Nijeriya.

Wasiƙar ta bayyana cewa bayan Kwamitin Tantance Ayyukan da aka Gabatar ya kammala aikin tantancewa na farko, za a miƙa ayyukan da suka cancanta ga kwamitin alƙalan domin gudanar da cikakken nazari da ba su maki bisa ƙa’idojin gasar da kuma ra’ayoyin su masu zaman kan su.

Haka kuma, mambobin kwamitin za su halarci zaman tantancewa da tattaunawar alƙalai, inda za su yanke shawarar ayyukan da za su kai matakin ƙarshe da kuma waɗanda za su lashe kyaututtukan.

Cibiyar ta WSCIJ ta jaddada aniyarta ta ci gaba da karrama ’yan jaridar Nijeriya waɗanda suka nuna ƙwarewa, ƙirƙira, jajircewa wajen kare ƙa’idojin aikin jarida da kuma sadaukarwa wajen yi wa al’umma hidima.

Gasar ta shekarar 2026 za ta karrama ƙwarewa a fannoni shida, waɗanda suka haɗa da jaridu da mujallu, rediyo, talbijin, ɗaukar hotunan labarai, kafafen intanet da kuma zane-zanen barkwanci masu sharhi kan al’amuran yau da kullum.

Da yake mayar da martani kan naɗin, Maikatanga ya nuna godiyar sa ga cibiyar bisa amincewar da ta yi da shi, yana mai bayyana farin cikin sa na kasancewa cikin waɗanda aka zaɓa domin tantance ayyukan ’yan jarida a wannan muhimmiyar gasa.

Maikatanga tsohon editan mujallar Fim ne, inda ya bayar da gudunmawa wajen gudanar da ayyukan mujallar kafin ya bar muƙamin a shekarun baya. Ya kuma yi fice a fannin ɗaukar hotunan labarai.

Loading

Tags: ɗaukar hotogasaSani MaikatangaWole SoyinkaWSCIJ
Previous Post

KILAF 2026: Mun samu finafinai 659 daga ƙasashe 77 na duniya — Galadima

Related Posts

Hukumar Tace Finafinai ta karɓi uzirin Tijjani Gandu
Labarai

Hukumar Tace Finafinai ta karɓi uzirin Tijjani Gandu

October 6, 2026
Tinubu da Remi sun halarci bikin fara nuna fim kan gwagwarmayar Abiola
Labarai

Tinubu da Remi sun halarci bikin fara nuna fim kan gwagwarmayar Abiola

October 1, 2026
Cewar Ability: Ba mu kafa KAFIGAN don sharholiya a Kannywood ba
Labarai

Za a ƙaddamar da reshen Kaduna na KAFIGAN ranar Asabar

October 1, 2026
Zaɓen 2027: Shettima ya nemi goyon bayan ‘yan fim da mawaƙan Arewa wajen sake zaɓen Tinubu
Siyasa

Zaɓen 2027: Shettima ya nemi goyon bayan ‘yan fim da mawaƙan Arewa wajen sake zaɓen Tinubu

September 30, 2026
Ina roƙon Rarara ya saka ni cikin ‘Triple R’ domin in samu na abinci – Baba Duduwa
Siyasa

Ina roƙon Rarara ya saka ni cikin ‘Triple R’ domin in samu na abinci – Baba Duduwa

September 30, 2026
Guguwar zaɓen 2027: Sanata Barau Jibrin ya kori jaruma Rasheeda Maisa’a daga tafiyar sa
Siyasa

Guguwar zaɓen 2027: Sanata Barau Jibrin ya kori jaruma Rasheeda Maisa’a daga tafiyar sa

September 29, 2026
  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!