• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Wednesday, November 4, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Kamfanin Tozali ya yi kira da a tallafa wa waɗanda suka tsira daga matsalar tsaro a bikin Henna Ball karo na 8

by FATI ABDUL
November 2, 2026
in Al'adu
0
Kamfanin Tozali ya yi kira da a tallafa wa waɗanda suka tsira daga matsalar tsaro a bikin Henna Ball karo na 8

Babbar jami'ar gudanarwa ta Tozali Group of Companies, Hajiya Maimuna Yaya Abubakar, tana amsa tambayoyin 'yan jarida a taron (Hoto: Tozali)

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

Rukunin kamfanonin kafafen labarai na Tozali Media Group ya yi kira da a ƙara tallafa wa mata da ‘yan mata da suka fuskanci sacewa, ‘yan fashi da makami, ta’addanci da sauran nau’o’in matsalar tsaro.

Kiran ya fito ne yayin da rukunin kamfanonin ya gudanar da bikin Henna Ball da Tozali People’s Awards karo na takwas a Abuja, wanda ya haɗa tsofaffin matan shugabannin Nijeriya, gwamnonin jihohi, sarakunan gargajiya da sauran fitattun ‘yan ƙasa domin ƙarfafa ƙoƙarin tallafa wa waɗanda suka tsira daga waɗannan matsaloli.

An gudanar da bikin ne a ranar Asabar, 31 ga Oktoba, 2026, a ɗakin taro na Los Angeles Event Centre da ke kan titin Ahmadu Bello Way, Abuja, ƙarƙashin taken “Ƙara wa Waɗanda Suka Tsira da Matsala Ƙarfi, da Dawo da Ƙauna.”

Bikin na shekara-shekara yana amfani da kafafen yaɗa labarai, nishaɗi da hulɗa da jama’a wajen inganta rayuwar al’umma, musamman ta hanyar jawo hankalin jama’a kan halin da mata da ‘yan mata ke ciki sakamakon matsalar tsaro, tare da neman tallafi domin farfaɗo da rayuwar su, ƙarfafa musu gwiwa da taimaka musu su koma cikin al’umma.

Daga cikin manyan baƙi da suka halarci bikin akwai tsofaffin matan shugabannin Nijeriya, Dakta Maryam Sani Abacha da Hajiya Turai Umaru Yar’Adua, da kuma Sarkin Dutse tare da sauran sarakunan gargajiya.

Sauran manyan baƙin sun haɗa da Gwamnan Jihar Zamfara, Dakta Dauda Lawal; Ministar Fasaha, Al’adu da Tattalin Arzikin Ƙirkire-ƙirkire, Barista Hannatu Musawa, wadda ta kasance babbar mai masaukin baƙi; da Wazirin Dutse, Alhaji Bashir Mohammed Ɗalhatu, wanda ya jagoranci zaman a matsayin shugaban taron.

Tsohon Gwamnan Jihar Neja, Daga Babangida Aliyu (Talban Minna), yana karɓar kambun karramawa daga Wazirin Dutse, Alhaji Bashir Ɗalhatu (a dama), a madadin Gidauniyar Tunawa Da Sardauna … a wurin taron

Gwamnan Jihar Taraba, Dakta Agbu Kefas, ya samu wakilcin Kwamishinan Yaɗa Labarai na jihar.

An karrama wasu fitattun mutane a wajen bikin bisa gudunmawar da suka bayar a fannonin hidimar jama’a, shugabanci, ayyukan jinƙai, nishaɗi, kasuwanci da cigaban ƙasa.

Haka kuma, an gudanar da shagulgulan nuna tufafi da salo na zamani, wasannin kiɗa da raye-raye, da kuma bayar da kyaututtukan karramawa.

Bayan shagulgulan, masu shirya taron sun ce babbar manufar bikin ita ce wayar da kan jama’a kan ƙalubalen da mata da ‘yan mata masu rauni suke fuskanta, tare da tattara tallafi domin taimaka musu wajen farfaɗowa, samun ƙarfin tattalin arziki da sake shiga cikin al’umma.

Dakta Maryam Sani Abacha riƙe da kambun karramawar ta a wurin taron

Da take jawabi a wajen taron, babbar jami’ar gudanarwa ta Tozali Group of Companies, Hajiya Maimuna Yaya Abubakar, ta nuna godiya ga manyan baƙi, sarakunan gargajiya, waɗanda aka karrama, masu ɗaukar nauyin taron, abokan hulɗar kafafen yaɗa labarai da sauran mahalarta bisa gudunmawar da suka bayar wajen tabbatar da nasarar bikin.

Ta bayyana cewa Henna Ball ya wuce taron nishaɗi na shekara-shekara, domin dandali ne na karrama nagarta tare da jawo hankalin jama’a kan muhimman al’amurran jinƙai da ya kamata a ci gaba da ba su kulawa.

Haka kuma, ta yaba wa abokan hulɗa da masu ɗaukar nauyin taron, inda ta ce tallafin su ya ƙara ƙarfafa ƙudirin kamfanin na amfani da tasirin kafafen yaɗa labarai wajen gudanar da ayyukan da za su amfani al’umma.

Ta kuma yaba wa ma’aikatan kamfanin, masu sa kai, kwamitocin shirya taron, masu samar da hidimomi da ‘yan jarida bisa jajircewa da ƙwazon da suka nuna wajen shiryawa da gudanar da bikin.

Tozali Media Group ya bayyana cewa nasarar gudanar da bikin karo na takwas ta ƙara ƙarfafa ƙudirin sa na ci gaba da wannan shiri tare da faɗaɗa ayyukan jinƙai, musamman domin tabbatar da cewa ana ci gaba da tattauna buƙatu da matsalolin waɗanda suka tsira daga hare-hare da sauran nau’o’in matsalar tsaro a matakin kasa.

Kamfanin ya sake jaddada cewa duk wanda ya tsira daga irin waɗannan matsaloli ya cancanci mutuntawa, samun damarmaki da tallafin da zai taimaka masa wajen sake gina rayuwar sa.

Ya bayyana cewa haɗin gwiwa, wayar da kai da ƙarfafa wa waɗanda abin ya shafa gwiwa su ne muhimman hanyoyin dawo da ƙauna a gare su.

Loading

Previous Post

Hotunan taron Tozali Henna Ball da karramawa

Next Post

Zuwairiyyah Girei ta zama Manajar Darakta ta gidan talbijin na Mahanga mallakin jarumin Kannywood Nuhu Abdullahi

Related Posts

Mu guji duk abin da zai jawo farraƙa tsakanin Hausawa da Fulani – Aminu Ala
Al'adu

Mu guji duk abin da zai jawo farraƙa tsakanin Hausawa da Fulani – Aminu Ala

August 12, 2026
Gwamna Abba Kabir Yusuf yana Jawabi a wajen taron
Al'adu

Ranar Al’adu ta Duniya: Gwamnan Kano na so a yi riƙo da al’adun gargajiya

August 10, 2025
Al'adu

Kare Sabbin Kalmomin Hausa “Saskiyā” (Synonym) da “Gīɗiyā” (Antonym) ta Hanyar ‘Yancin Binciken Ilimi

May 22, 2025
Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II kadara ne mai daraja ga Jihar Kano
Al'adu

Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II kadara ne mai daraja ga Jihar Kano

January 28, 2024
Minista Hannatu Musawa ta ƙudiri aniyar kafa Gidan Tarihi da Gidan Wasanni na Ƙasa a Abuja
Al'adu

Minista Hannatu Musawa ta ƙudiri aniyar kafa Gidan Tarihi da Gidan Wasanni na Ƙasa a Abuja

December 14, 2023
Khalifa Muhammadu Sanusi II
Al'adu

Sanusi: Magajin Sanusi da Kukuna

June 23, 2023
Next Post
Zuwairiyyah Girei ta zama Manajar Darakta ta gidan talbijin na Mahanga mallakin jarumin Kannywood Nuhu Abdullahi

Zuwairiyyah Girei ta zama Manajar Darakta ta gidan talbijin na Mahanga mallakin jarumin Kannywood Nuhu Abdullahi

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!