GWAMNATIN Jihar Kano, ta hannun Hukumar Gudanar da Inshorar Lafiya ta Jihar Kano (KSCHMA), ta naɗa tsohuwar jarumar finafinan Hausa, Halisa Muhammad, a matsayin jakadiyar waɗanda suka tsira daga cutar kansar mama, domin ƙarfafa hulɗa tsakanin waɗanda suka warke daga cutar da hukumar.
Wannan na ƙunshe ne cikin sanarwar da Jami’in Hulɗa da Jama’a na hukumar, Aminu Ahmad Turaki, ya fitar.
A cewar sanarwar, naɗin ya biyo bayan ƙaddamar da shirin shigar da waɗanda suka tsira daga cutar kansar mama cikin tsarin kula da lafiya na AbbaCare, wanda aka gudanar a hedikwatar hukumar da ke Kano, bisa umarnin Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf.
Sanarwar ta bayyana cewa Hajiya Halisa, wadda ta taɓa fama da cutar sankarar mama amma ta samu waraka, ita ce shugabar gidauniyar Women for Cancer Early Detection and Treatment Foundation, wadda ke wayar da kan al’umma kan muhimmancin gano cutar da wuri da kuma samun magani cikin lokaci.
Da take karɓar naɗin, Halisa ta bayyana cewa Gwamna Abba ya tallafa mata da sama da naira miliyan 30 domin biyan kuɗaɗen jinyar cutar sankarar mama da ta yi fama da ita.
Ta ce wannan tallafi ya ƙarfafa mata gwiwar kafa gidauniyar da manufar ta ita ce wayar da kan jama’a game da cutar kansar mama, musamman muhimmancin gano ta tun kafin ta kai wani mataki mai tsanani.
A nata ɓangaren, Shugabar KSCHMA, Dakta Rahila Aliyu Mukhtar, ta bayyana cewa naɗin Halisa zai taimaka wajen isar da buƙatu, ƙalubale da damuwar waɗanda suka tsira daga cutar zuwa ga hukumar, domin samar musu da kulawa da tallafin da suke buƙata.
Ta ƙara da cewa haɗa kai da waɗanda suka taɓa fama da cutar zai taimaka wajen inganta tsarin kula da lafiyar su tare da ƙarfafa shigar da su cikin shirye-shiryen hukumar.
Halisa ta yi alƙawarin yin aiki tare da hukumar da sauran masu ruwa da tsaki domin inganta wayar da kan jama’a, sauƙaƙa samun bayanan kiwon lafiya da kuma ƙarfafa tallafin da ake bai wa waɗanda suka tsira daga cutar sankarar mama.
![]()







