• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Monday, October 12, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Darakta Aminu Saira ya yi walimar buɗe gidan da babu mai irin shi a Kannywood 

by MUKHTAR YAKUBU
December 20, 2025
in Ranar Murna
0
Darakta Aminu Saira ya yi walimar buɗe gidan da babu mai irin shi a Kannywood 

Gidan Aminu Saira mai hawa biyu "Aljannar Duniya" ce

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

BAYAN kammala ginin katafaren gidan sa da ya yi, darakta a Kannywood, Malam Aminu Saira, ya shirya wata gagarumar walima domin nuna farin cikin sa da kuma godiyar sa ga Allah bisa ni’imar da ya yi masa.

An yi walimar a jiya Juma’a a gidan da ke unguwar Sharaɗa NNDC Quarters a cikin garin Kano.

Taron, wanda aka fara shi daga ƙarfe 5 na yamma zuwa bayan magariba, ya samu halartar manyan jarumai da daraktoci tare da ‘yan’uwa da abokan arziki.

Dandazon mahalarta walimar buɗe gidan
Darakta Kamal Alƙali (a dama) tare da wasu mahalartan

Tun da farko da yake jawabin maraba, Saira ya bayyana cewa, “Na kira wannan taron tare da shirya walima dangane da damar da Allah ya ba ni ta kammala ginin gida da na yi, wanda a gare ni shi ne abu mafi muhimmanci a rayuwa ta ta yanzu.
Alhamdu lillah, a yanzu wannan waje na kammala aikin sa, don haka ina godiya ga dukkan waɗanda suka amsa gayyatar da na yi domin na ga masoya na da dama da muka daɗe ba mu ga juna ba.

“Babu shakka, fuskokin da na gani a wannan waje suna da muhimmanci a waje na, domin na ga iyayen gida na da abokan aiki na, har ma da abokai na yarinta duk sun haɗu a wannan waje, don haka ina godiya sosai, Allah ya bar zumunci.”

Malam Aminu Saira yana gabatar da jawabin maraba
Wani falo a cikin gidan

Bayan ya kammala jawabin, sai aka shiga cin abincin da aka tanadar wa mahalarta taron, abinci kala-kala na alfarma wanda kowa ya ci iya buƙatar sa.

Da aka gama, sai aka zagaya da jama’a lungu da saƙo na gidan domin ganin yadda yake. Gida ne dai da aka gina hawa biyu wanda ya ƙunshi ɓangaren iyali da na mahaifiyar sa da na yaran sa.

Haka nan akwai ɓangaren ganawa da baƙi, sai ofishin Saira Movies, da situdiyo da sauran su.

Babu shakka, za a iya kiran gidan da aljannar duniya, domin duk da manyan gidaje da ake ganin ‘yan fim sun gina, idan gasar nuna gida za a yi a masana’antar Kannywood a yanzu Malam Aminu Saira sai iya lashe gasar.

Duk wanda ya ga gidan ciki da waje ya san cewa an kashe kuɗin masu yawa.

‘Yan fim da suka je wajen sun haɗa da Hamisu Lamiɗo Iyan-Tama, Bala Anas Babinlata, Salisu A. Fulani, Abdullahi Hikima, Abale, Yasir Auwal, Nura Mado, da ƙanen maigidan, wato mawaƙi Naziru M. Ahmad, da wasu ma.

Kowa na addu’ar Allah sa rai aka yi wa.

Farfajiyar gidan

Loading

Tags: buɗe gidangidaMalam Aminu SairaSaira Movieswalima
Previous Post

Buri na shi ne saƙonnin da suke cikin rubutu na su zama masu tasiri ga al’umma – Hauwa Shehu

Next Post

Darajar Kannywood ta ɗaga a cikin 2025 – MOPPAN

Related Posts

Bikin auren Ibrahim Nuhu Gudaji da Zainab Adamu (Najlah): Marubuta sun yi wa Hadiza Nuhu Gudaji da Lubabatu Ya’u kara
Ranar Murna

Bikin auren Ibrahim Nuhu Gudaji da Zainab Adamu (Najlah): Marubuta sun yi wa Hadiza Nuhu Gudaji da Lubabatu Ya’u kara

October 10, 2026
Furodusan ‘Wata Shida’, Hayatuddeen Yakubu ya sake aure wata 7 bayan rasuwar matar sa
Ranar Murna

Furodusan ‘Wata Shida’, Hayatuddeen Yakubu ya sake aure wata 7 bayan rasuwar matar sa

September 28, 2026
An ɗaura auren Faɗima ‘yar furodusan Kannywood marigayi Nura Shariff
Ranar Murna

An ɗaura auren Faɗima ‘yar furodusan Kannywood marigayi Nura Shariff

September 7, 2026
Farha, ‘yar tsohuwar jaruma Halima Atete, ta cika shekara ɗaya
Ranar Murna

Farha, ‘yar tsohuwar jaruma Halima Atete, ta cika shekara ɗaya

September 5, 2026
Mawaƙi Abdool-Gaya ya samu ƙaruwar ɗa namiji
Ranar Murna

Mawaƙi Abdool-Gaya ya samu ƙaruwar ɗa namiji

August 24, 2026
An ɗaura auren mawaƙi Kawu Ɗan Sarki
Ranar Murna

An ɗaura auren mawaƙi Kawu Ɗan Sarki

August 23, 2026
Next Post
Darajar Kannywood ta ɗaga a cikin 2025 – MOPPAN

Darajar Kannywood ta ɗaga a cikin 2025 - MOPPAN

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!