• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Wednesday, August 12, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Darajar Kannywood ta ɗaga a cikin 2025 – MOPPAN

Shekarar 'Yan Kannywood ta 2025

by MUKHTAR YAKUBU
December 21, 2025
in Labarai
0
Darajar Kannywood ta ɗaga a cikin 2025 – MOPPAN

Alhaji Shehu Hassan Kano, Shugaban MOPPAN na Ƙasa

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

ƘUNGIYAR Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya (Motion Picture Practitioners Association of Nigeria, MOPPAN) ta bayyana cewa 2025 ta kasance shekara mai cike da tarihi, nasarori da kuma cigaban masana’antar shirya finafinan Hausa.

Cikin wata takarda da MOPPAN ta fitar fitar da sunan rahoto kan Shekarar ‘Yan Kannywood ta 2025, ƙungiyar ta ce:

“Shekarar 2025 ta zo da ƙalubale da dama, amma duk da haka ta kasance shekara mai albarka wadda ta ga yawaitar finafinai masu inganci, da kuma fitowar sababbin fasahohi da salo a masana’antar Kannywood.

“Masu shirya finafinai sun nuna jajircewa da sadaukarwa wajen samar da finafinai masu ilimantarwa, nishaɗantarwa da kuma isar da saƙonni masu amfani ga al’umma.”

A cewar MOPPAN, “An samu cigaba mai kyau a fannin labari, ɗaukar hoto, shirya fim da kuma kula da ƙa’idojin sana’ar fim, wanda hakan ya taimaka wajen ɗaga darajar Kannywood a matakin Nijeriya, Afrika da ma duniya baki ɗaya.”

Ƙungiyar ta bayyana finafinai biyar da suka fi ɗaukar hankali a shekarar, kamar haka:

  1. KAKANDA: Fim ɗin da furodusa Dakta Ahmad Sarari tare da Malam Khalid Musa suka rubuta, fim ne mai ingantaccen labari, salo na zamani da kuma tsari mai ƙarfi, wanda ya ja hankalin masu kallo sosai.
  2. MANYAN MATA: Fim ɗin furodusa Abdul Amart, wanda ya fito da darajar mata da rawar da suke takawa a cikin al’umma, ya samu karɓuwa sosai daga masu kallo.
  3. GARWASHI: Fim ɗin furodusa Umar UK, wanda ke nuna gwagwarmaya da juriya a rayuwar ɗan’adam, ya nuna ƙwarewa ta musamman a fannin rubutu da aiwatarwa.
  4. LABARI NA: Fim ɗin darakta Malam Aminu Saira, wanda ya nuna hazaƙa da zurfin tunani a tsarin labari da kuma jagoranci.
  5. WATA SHIDA: Fim ɗin furodusa Hayatuddeen Yakubu, wanda aka shirya bisa littafin Kamilu Ɗanhausa, ya samu karɓuwa a cikin gida da kuma ƙasashen Afrika, tare da nuna ƙarfin labarin Hausa a duniya.

Rahoton ya ambaci ‘Mai Martaba’ wanda Prince Aboki ya shirya kuma ya jagoranta a matsayin fim mafi shahara a shekarar. Fim ɗin ya samu nasarori masu yawa tare da ɗaga darajar Kannywood a idon duniya.

Haka nan MOPPAN ta yaba da gudunmawar da shugaban ta, Alhaji Shehu Hassan Kano, bisa jagoranci da ƙoƙarin sa na haɗa kai da kuma bunƙasa sana’ar fim.

Ta miƙa godiya ga dukkan furodusoshi da sauran ‘yan Kannywood bisa biyayya da goyon baya ga ƙungiyar.

MOPPAN ta roƙi Allah ya saka wa kowa da alheri, ya kuma nuna mana shekarar 2026 cikin kwanciyar lafiya.

Rahoton na MOPPAN

Loading

Tags: 2025bitar shekaraKannywoodMOPPANrahoto
Previous Post

Darakta Aminu Saira ya yi walimar buɗe gidan da babu mai irin shi a Kannywood 

Next Post

Furodusa a Kannywood, Mansurah Isah ta naɗa ɗan kasuwa Sani Isah shugaban kwamitin amintattu na gidauniyar ta

Related Posts

Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba
Labarai

Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba

August 8, 2026
Fitaccen mawaƙin siyasa Muhammadu Buhari ‘Kosan Waka’ ya kwanta dama
Labarai

Fitaccen mawaƙin siyasa Muhammadu Buhari ‘Kosan Waka’ ya kwanta dama

August 2, 2026
Yadda gwajin ƙwayoyin halitta na jini ya kawo ƙarshen auren Adam A. Zango da Maimuna Musa bayan watanni 11
Labarai

Yadda gwajin ƙwayoyin halitta na jini ya kawo ƙarshen auren Adam A. Zango da Maimuna Musa bayan watanni 11

August 1, 2026
Jami’an gwamnati sun yi zama da Kannywood domin fara aiwatar da shirin ba da inshorar lafiya kyauta ga ‘yan fim na Kano
Labarai

Jami’an gwamnati sun yi zama da Kannywood domin fara aiwatar da shirin ba da inshorar lafiya kyauta ga ‘yan fim na Kano

July 15, 2026
Kannywood tana buƙatar farfaɗo da gidajen sinima domin bunƙasa tattalin arzikin ƙirƙira – Sani Mu’azu
Labarai

Kannywood tana buƙatar farfaɗo da gidajen sinima domin bunƙasa tattalin arzikin ƙirƙira – Sani Mu’azu

July 14, 2026
A hira da mujallar Fim, mawaƙi Ado Gwanja ya aiko da saƙo ga masoyan sa daga gadon asibiti
Labarai

A hira da mujallar Fim, mawaƙi Ado Gwanja ya aiko da saƙo ga masoyan sa daga gadon asibiti

July 9, 2026
Next Post
Furodusa a Kannywood, Mansurah Isah ta naɗa ɗan kasuwa Sani Isah shugaban kwamitin amintattu na gidauniyar ta

Furodusa a Kannywood, Mansurah Isah ta naɗa ɗan kasuwa Sani Isah shugaban kwamitin amintattu na gidauniyar ta

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!