• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, August 25, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Ƙungiyar Kannywood Kwankwasiyya ta ziyarci Hukumar Tace Finafinai 

by MUKHTAR YAKUBU
December 17, 2025
in Labarai
0
Ƙungiyar Kannywood Kwankwasiyya ta ziyarci Hukumar Tace Finafinai 

Alhaji Abba El-Mustapha tare da 'ya'yan ƙungiyar Kannywood Kwankwasiyya a lokacin ziyarar a ofishin Hukumar Tace Finafinai da Ɗab'i ta Jihar Kano a ranar Litinin

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

WATA sabuwar ƙungiyar tafiyar siyasar ‘yan fim mai suna Kannywood Kwankwasiyya ta kai wa Hukumar Tace Finafinai da Ɗab’i ta Jihar Kano Abba El-Mustapha ziyara domin gabatar kan ta da kuma nuna goyon bayan su a ga hukumar bisa manufofi da kuma tsare-tsaren Gwamnatin Abba Kabir Yusuf da jagoran siyasar Kano, Sanata Rabi’u Musa kwankwaso.

‘Yan ƙungiyar sun kai ziyarar a ranar Litinin, inda suka samu kyakkyawar tarba daga Babban Sakataren hukumar, Alhaji Abba El-Mustapha.

A lokacin ziyarar, shugaban ƙungiyar, Alhaji Isma’il Khalil Ja’en Mahy, ya bayyana cewa sun kafa ƙungiyar ne “duba da yadda aka bar Kannywood a baya babu wata ƙungiya da take morar gwamnati da wani abu duk da Kannywood muna da yawa, sannan Kwankwasiyya tana da mabiya da yawa a Kannywood.

“Amma ko a kwanaki Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya taimaki ƙungiyoyi da dama amma babu ƙungiyar Kannywood ko ɗaya a ciki.

“Wannan dalili ya sa muka tabbatar da wannan ƙungiyar da za ta rinƙa tallata ayyukan Gwamna Abba Kabir Yusuf birni da ƙauyuka don wayar da kan al’umma a kan gwamnatin Jihar Kano ƙarƙashin Abba Kabir Yusuf.”

Babban Sakataren Hukumar Tace Finafinai da Ɗab’i ta Jihar Kano Abba El-Mustapha (a dama) tare da Shugaban ƙungiyar Kannywood Kwankwasiyya, Alhaji Isma’il Khalil Ja’en Mahy, a lokacin ziyarar

Da yake mayar da jawabi, El-Mustapha ya nuna farin ciki da jin daɗin sa bisa wannan ziyara, sannan ya bayyana ƙungiyar a matsayin wadda ta zo da kyakkyawar manufa.

Shugaban ya ce zai yi iya bakin ƙoƙarin sa wajen taimakon ƙungiyar.

El-Mustapha ya yi jan hankali a kan duk wanda zai bada gudunmawa a harkar Kwankwasiyya a ja shi a jiki a yi tafiyar da shi kuma kada a yi ƙungiya don cin zarafin wasu, ya zama an yi ta ne don samar wa Kannywood cigaba tare da nemo hanyar da gwamnati za ta taimaki ‘yan Kwankwasiyya na Kannywood.

A tawagar ‘yan ƙungiyar Kannywood Kwankwasiyya ɗin dai akwai da Isma’il Khalil Ja’en, Tijjani Faraga, Safiya Kishiya, Yahanasu Sani, Hassana Musa, Mariya Ibrahim, da sauran su.

El-Mustapha (a dama) da jarumi Tijjani Faraga a lokacin ziyarar

Loading

Tags: Abba El-MustaphaGwamna Abba Kabir YusufIsma'il Khalil Ja'en MahyKannywood Kwankwasiyyaƙungiyasiyasaziyara
Previous Post

Ba mu ga abin da Ali Nuhu ya tsinana wa Kannywood ba tun da ya shiga gwamnati, inji Shehu Hassan Kano

Next Post

Buri na shi ne saƙonnin da suke cikin rubutu na su zama masu tasiri ga al’umma – Hauwa Shehu

Related Posts

Mutuwar aure na ƙaddara ce – Jaruma Khadija Yobe
Labarai

Mutuwar aure na ƙaddara ce – Jaruma Khadija Yobe

August 23, 2026
Aina’u Ade ta raba wa tsofaffin jaruman Kannywood tallafin kuɗi
Labarai

Aina’u Ade ta raba wa tsofaffin jaruman Kannywood tallafin kuɗi

August 23, 2026
Ƙungiyar ‘Triple R Kannywood’ ta ziyarci jarumi Tanimu Akawu a asibiti
Labarai

Ƙungiyar ‘Triple R Kannywood’ ta ziyarci jarumi Tanimu Akawu a asibiti

August 23, 2026
Ƙungiyar Triple R ta ba jarumin Kannywood Mustapha Musty tallafin N500,000
Labarai

Ƙungiyar Triple R ta ba jarumin Kannywood Mustapha Musty tallafin N500,000

August 18, 2026
Yadda na gamu da ibtila’in karaya a ƙafa – Jarumi Ɗan’azumi Kamaye
Labarai

Yadda na gamu da ibtila’in karaya a ƙafa – Jarumi Ɗan’azumi Kamaye

August 14, 2026
Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba
Labarai

Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba

August 8, 2026
Next Post
Buri na shi ne saƙonnin da suke cikin rubutu na su zama masu tasiri ga al’umma – Hauwa Shehu

Buri na shi ne saƙonnin da suke cikin rubutu na su zama masu tasiri ga al'umma - Hauwa Shehu

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!