• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Monday, August 24, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Ba mu ga abin da Ali Nuhu ya tsinana wa Kannywood ba tun da ya shiga gwamnati, inji Shehu Hassan Kano

by MUKHTAR YAKUBU
December 17, 2025
in Labarai
0
Ba mu ga abin da Ali Nuhu ya tsinana wa Kannywood ba tun da ya shiga gwamnati, inji Shehu Hassan Kano

Shehu Hassan Kano (a hagu), da Ali Nuhu

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

SHUGABAN Ƙungiyar Ƙwararru Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya (MOPPAN), Alhaji Shehu Hassan Kano, ya bayyana cewa har yanzu masana’antar Kannywood ba ta ga wani cigaban da Ali Nuhu ya kawo mata ba tun da ya zama Manajan Darakta na Hukumar Shirya Finafinai ta Nijeriya (wato Nigerian Film Corporation, NFC).

MOPPAN ita ce uwar ƙungiyoyin da ke shirya finafinan Hausa.

Shehu ya ɓara ne a wata hira da ya yi da mujallar Fim.

Idan kun tuna, mujallar Fim ta ruwaito labarin cewa jim kaɗan bayan kammala bikin baje-kolin finafinai na Zuma (Zuma Film Festival) wanda NFC ɗin take gudanarwa a duk shekara, ƙungiyar MOPPAN da haɗin gwiwar Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Arewa (Arewa Film Makers Association of Nigeria, AFMAN) sun aika wa da hukumar ƙorafin su kan rashin gayyatar su zuwa bikin da hukumar ta yi, suka ce ta nuna musu wariya.

NFC dai ta zaɓi waɗansu ɗaiɗaikun ‘yan Kannywood ne, ta gayyace su zuwa bikin wanda aka yi a Abuja kwanan nan, har ta karrama wasu da lambobin girmamawa. Ba ta gayyaci kowace ƙungiya daga masana’antar ba.

Ƙorafin ƙungiyoyin biyu, ɗauke da sa-hannun Shehu Hassan Kano (Shugaban MOPPAN) da Alhaji Salisu Mohammed Officer (Shugaban AFMAN), ya tayar da muhawara a industiri, inda aka riƙa musanyar ra’ayi kan rawar da Ali Nuhu yake takawa a NFC, musamman dangantakar sa da sheƙar da aka ƙyanƙyashe shi a cikin ta, wato Kannywood.

A hirar sa da wakilin mu, Shehu Hassan Kano, wanda fitaccen jarumi ne, ya nuna cewa a da NFC takan gayyaci MOPPAN zuwa bikin baje-kolin, kuma ba a ga canji ba sai da Ali Nuhu ya hau kujerar shugabancin hukumar.

Ali dai shi ne ɗan Kannywood na farko da ya zama shugaban hukumar, wanda shi ne muƙami mafi girma da aka taɓa ba wani ɗan fim ɗin Hausa a Gwamnatin Tarayya.

Da yake tsokaci ga mujallar Fim kan dalilin su na yin ƙorafi a rubuce ga NFC, Shehu ya ce: “Babban dalilin dai shi ne da a baya dai ba haka ake yi ba… Shugabannin da suka riƙe ƙungiyoyi irin MOPPAN a baya, gaskiya in an zo tarurruka irin waɗannan da su ake komai, domin ana involving ɗin su a ciki. Ana ma ɗan ba su aiki su taimaka wajen gabatar da wannan festival idan za a yi shi duk shekara.

“To amma abin da ya ba mu mamaki, sai a wannan shekarar da za a yi, kawai sai muka ga cewar kwata-kwata ba a yi involving ƙungiyoyin da suke Arewa ba. Kuma ba a gaya mana dalili ba, ba a kuma gaya mana meye zai gamsar da mu cewa ga abin da ya jawo ba a yi involving waɗannan ƙungiyoyin biyu da suke Arewa ba.

“Ni a matsayi na na Shugaban MOPPAN, a yanzu ne na fara shugabancin MOPPAN, amma duk shugabannin MOPPAN na baya sun san cewa duk shekara in za ai taro irin wannan ana involving ɗin MOPPAN da ire-iren ƙungiyoyi kamar MOPPAN ɗin. Amma sai ga shi bana da za a yi sai ba ai involving ɗin MOPPAN ba. To me ya faru?

“Ka ga ba mamaki kenan su da ba su yi involving ɗin mu ba, su NFC ɗin, su ne za su iya ba mu amsa ta dalilin da ya sa ba su yi involving ɗin mu ba wannan karon.

“Domin mu takardar da muka rubuta, mu NFC muka rubuta wa ba wani individual mutum ba. Ba mu yi addressing mutum ɗaya, muka ce wai shi muka rubuta wa ba personally, a’a, hukumar NFC muka rubuta wa domin su ne suke da concern a kan wannan abin, kuma su ne za su iya ba mu amsar me ya sa bana ba su yi involving ɗin mu ba tunda a baya duk ana yi.”

Da mujallar Fim ta tambaye shi ko ba ya ganin kamar za a yi musu dariya ganin a yanzu ɗan’uwan su ɗan Kannywood ne yake shugabantar hukumar, sai ya ce: “Ba wani wanda zai mana dariya domin magana ce ta neman haƙƙi da ‘yanci. Ƙungiya ce ake yin ta, kuma shi (Ali Nuhu) daga tsatson wannan ƙungiyar ya fito, doron ta ya taka ya je inda ya je.

Ƙungiya ce ake yin ta, kuma shi (Ali Nuhu) daga tsatson wannan ƙungiyar ya fito, doron ta ya taka ya je inda ya je.

“Ai a ƙa’ida ma ya kamata a ce shi da kan sa da ya ga ba a yi involving waɗannan professional bodies ɗin ba na ƙungiyoyin, kuma ya san da can a baya ana yi, shi kuma yana gurin ya ga kuma ba a yi ba, to ai shi ya kamata ma ya fara magana kafin mu, a ƙa’ida ma tun kafin ma a fara, in ya duba programme ɗin ya ga ba a sa waɗannan ƙungiyoyin na Arewa a ciki ba. Da sai dai mu ji daga can sama kurum ana hayaniya da shi a kan cewa ba a yi involving ƙungiyoyin Arewa a cikin wannan abin ɗin ba.

“To ka ga kenan ashe don mun nemi haƙƙin mu ko ‘yancin mu a matsayin mu na ƙungiya tsakanin mu da hukumar da take ta ƙasa ta gwamnati kuma Gwamnatin Tarayyar Nijeriya – ba fa ta mutum ɗaya ba ce, ba ta Inyamiri ba ce, ba ta Bayarabe ba ce, ba ta Bahaushe ba ce.

“Kuma ko da ba ma shi ne a gurin ba, ko ma wani Inyamiri ne ko Bayarabe – ko waye – aka tashi yin wannan abin, kuma ba a yi involving ɗin mu ba, muna da haƙƙi, muna da ‘yanci mu rubuta takarda mu yi ƙorafi a kan cewa me ya sa bana ba a yi ba, ko me ya sa a yanzu ba a yi ba? To, za a ba mu amsa. Ba wai don yana gurin muka yi ba, a’a, domin tun kafin ya je gurin da ƙungiyoyin da ma ake yi.”

Dangane da irin cigaban da Kannywood ta samu tun daga lokacin da Ali Nuhu ya shiga gwamnati a matsayin shugaban hukumar, Shehu ya ce, “To, ni dai a matsayi na na zaɓaɓɓen Shugaban MOPPAN wanda na fara tafiya da wannan abin nan ɗin, ni dai ban ga wani cigaba da aka samu ba don yana wannan wajen a masana’antar mu. Amma wataƙila ɗaiɗaikun mu sun san da cigaban, domin ka ga da farko dai ni ba furodusa ba ne balle a ce a’a ina da fim da na yi furodusin kuma NFC ta yi min wani tallafi a ciki. Ni ba marubuci ba ne, ni ba darakta ba ne. Ni jarumi ne mai taka rawa a finafinai.

“Amma a matsayi na na wanda yake kan kujerar shugabanci, idan da akwai cigaban da shi a zuwan sa gurin ya kawo wa masana’antar Kannywood, to ya kamata a ce ina ɗaya daga cikin waɗanda za mu ga wannan cigaban, kuma mu shaida, ko da ma a rubuce ne. To amma gaskiya ni dai ban gani ba.

“Ta yiwu wasun mu sun gani ko sun sani, in ma sun amfana, amma mu dai a ƙungiyance da ni da Exco ɗina ba mu ga wannan cigaban ba, ba mu san da shi ba. In kuma an yi ƙila sai a zo a yi mana bayani.”

Loading

Tags: AFMANAli NuhuHukumar Shirya Finafinai ta Nijeriya NFCKannywoodƙorafiShehu Hassan KanoZuma Film Festival
Previous Post

Ɗaha, ɗan tsohuwar jaruma Halima Adamu Yahaya ya yi saukar Alƙur’ani 

Next Post

Ƙungiyar Kannywood Kwankwasiyya ta ziyarci Hukumar Tace Finafinai 

Related Posts

Mutuwar aure na ƙaddara ce – Jaruma Khadija Yobe
Labarai

Mutuwar aure na ƙaddara ce – Jaruma Khadija Yobe

August 23, 2026
Aina’u Ade ta raba wa tsofaffin jaruman Kannywood tallafin kuɗi
Labarai

Aina’u Ade ta raba wa tsofaffin jaruman Kannywood tallafin kuɗi

August 23, 2026
Ƙungiyar ‘Triple R Kannywood’ ta ziyarci jarumi Tanimu Akawu a asibiti
Labarai

Ƙungiyar ‘Triple R Kannywood’ ta ziyarci jarumi Tanimu Akawu a asibiti

August 23, 2026
Ƙungiyar Triple R ta ba jarumin Kannywood Mustapha Musty tallafin N500,000
Labarai

Ƙungiyar Triple R ta ba jarumin Kannywood Mustapha Musty tallafin N500,000

August 18, 2026
Yadda na gamu da ibtila’in karaya a ƙafa – Jarumi Ɗan’azumi Kamaye
Labarai

Yadda na gamu da ibtila’in karaya a ƙafa – Jarumi Ɗan’azumi Kamaye

August 14, 2026
Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba
Labarai

Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba

August 8, 2026
Next Post
Ƙungiyar Kannywood Kwankwasiyya ta ziyarci Hukumar Tace Finafinai 

Ƙungiyar Kannywood Kwankwasiyya ta ziyarci Hukumar Tace Finafinai 

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!