MANYAN ƙungiyoyin shirya finafinan Hausa sun yi ƙorafi kan salon shugabannin Ali Nuhu a Hukumar Finafinai ta Nijeriya (NFC), suka ce hukumar tana nuna masu wariya a harkokin ta.
Ƙungiyar Ƙwararru Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya (MOPPAN), wadda ita ce babbar ƙungiyar ‘yan Kannywood, tare da haɗin gwiwar Ƙungiyar Furodusoshi ta Arewa (AFMAN), sun nuna matuƙar damuwa kan yadda suka ce NFC tana ƙoƙarin mayar da su saniyar ware.
A wata wasiƙa da suka aika zuwa ga NFC a hedikwatar ta da ke Jos, Jihar Filato, shugaban MOPPAN, Alhaji Shehu Hassan Kano, da na AFMAN, Alhaji Salisu Mohammed Officer, sun bayyana damuwar su bisa yadda ake nuna musu wariya da sakaci da al’amuran su waɗanda ke ci gaba da yawaita daga ɓangaren wakilan NFC na Arewa.
Suka ci gaba da cewa, “Gabanin daraktan ya kama aiki, hukumar tana iya bakin ƙoƙarin ta wajen ganin ta kiyaye aiki tare da ƙungiyoyin ta yadda take bada gudunmawa ga cigaban finafinan mu, ayyukan al’adu, inganta matasa da haɗin kan ƙasa ta harkar fim.”
Sun nuna cewa ba haka abin yake ba, inda suka bada misali da taron baje-kolin finafinai na Zuma na bana, wanda NFC ta shirya kwanan nan a Abuja, suka ce duk da cewa MOPPAN da AFMAN suna da muhimmanci da babbar rawa da za su iya takawa a kai, amma babu wata gayyata ta musamman da aka aika masu.
MOPPAN da AFMAN sun bayyana cewa cigaban ƙasa ta ayyukan fasaha, musamman ta masana’antar finafinai, zai samu ne yayin da aka samu haɗin gwiwa tsakanin dukkan ɓangarorin ƙasa tare da damawa da su ta yadda kowanne ɓangare zai bada tasa gudunmawar.
Don haka suka yi kira ga hukumar ta NFC da ta yi nazari kan wannan al’amarin tare da ɗaukar matakan da suka dace wajen warware matsalolin duba da yadda Kannywood, wadda ita ce masana’antar fim da ke kan gaba a arewacin Nijeriya, take bada gagarumar gudunmawa a fannin.
![]()







