TSOHUWAR jaruma a Kannywood, Halima Adamu Yahaya, ta shirya wa dan ta mai suna Ɗaha Auwal Maikano, bikin saukar Alƙur’ani da Allah ya azurta ta shi da ita.
A ranar Asabar ne dai aka yi bikin saukar a Madarasatuk Itikanil Ƙuri’an da ke garin Rimin Gado a Jihar Kano.
Daha Auwal Maikano yana cikin jerin ɗalibai da suka yi sauka a makarantar.
Don farin ciki, Halima Adamu Yahaya ta shirya taron murnar samun nasarar da ɗan ta ya samu na saukar Alƙur’ani inda ‘yan uwa da abokan arziki suka taru domin taya ta murna.
Halima ta nuna matuƙar farin ciki da godiyar ta, inda take cewa. “Na daɗe ban yi farin ciki ba irin na wannan rana ba, domin duk Musulmi babban burin sa a duniya ba ya wuce uku – aikin Hajji, cikawa da imani, sai haddar Ƙur’ani.

“Ina matuƙar godiya ga Allah da ya nuna mini wannan rana da auta na a maza da ya yi sauka. Ina fatan Ubangiji ya sa ya yi ta tsoron Allah, ya ƙara cusa masa hasken Alƙur’ani a zuciyar sa.

“Mu kuma iyayen sa Allah ya sa sanadiyyar shiga Aljannar mu ne.
“Malamin da ya yi ta ɗawainiya da su shi ma Allah ya biya shi da Aljanna.
“Baƙi kuma da suka zo mana su ma Allah ya sa ka musu da alkhairi.”
![]()







