• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, August 25, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

An ɗora sababbin marubuta a kan hanya a taron horar da marubutan Kannywood

by MUKHTAR YAKUBU
December 14, 2025
in Labarai
0
An ɗora sababbin marubuta a kan hanya a taron horar da marubutan Kannywood

Ali Nuhu a tsakiyar wasu mahalarta taron ɓangaren maza

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

AƘALLA matasan marubuta labarin fim masu tasowa sama da 50 suka samu damar halartar taron bayar da horo da aka gudanar na masana’antar Kannywood a ƙarƙashin Hukumar Shirya Finafinai take Nijeriya (NFC).

‘Nigeria Film Corporation’ wadda Dr. Ali Nuhu yake jagoranta.wanda aka

Taron, wanda aka gudanar a ranar Asabar a ɗakin taro na Kannywood TV da ke Titin Muhammadu Buhari a cikin garin Kano, an shirya shi ne domin ƙara ƙwarewar wasu marubutan tare ƙyanƙyashe sababbin marubuta a masana’antar.inda

Ƙwararrun malamai masana rubutun fim daga tashar Arewa 24 kamar Nazir Adam Salih da Fauziyya D. Sulaiman da Zuwairiyyah Girei da Nasir NID su ne suka bayar da wannan horo.

Tun da farko da yake jawabi a kan manufar shirya taron, Malam Kabiru Yusuf Fagge (Anka) ya ce: “Manufar shirya wannan taro shi ne horas da matasa su samu sana’ar rubutun labarin fim domin samar da hanyar ƙwarewa ta yadda za su ci gajiyar harkokin domin haka ne aka samar da ƙwararru a kan rubuta labari da kuma tsara shi da za su gabatar da jawabai a wannan wajen.

“Sai dai marubuta labarin su sani mun shirya wannan taro ne domin samar musu da kyakkyawar hanyar rubuta labarin, amma ba yadda za su sayar da shi ba.

“Muna buƙatar a koya a ƙware ta yadda za a ga ƙwarewar mutum a neme shi har inda yake ba tare da yana neman masu buƙatar sa ba.

Hajiya Zuwairiyya Adamu Girei, tana gabatar da jawabi

“Muna fatan wannan taro da za a yi ya zama wata hanya ta samar da ƙwararrun marubutan Kannywood da za su ci gajiyar harkar a nan gaba.”

Nazir Adam Saleh shi ne ya fara gabatar da jawabi, inda ya yi dogon bayani a kan yadda ake tsara rubutun labarin fim daidai da zamani, inda ya kawo misalai masu yawa wajen yadda za a tsara rubutun labarin da zai yi daidai da zamani da aka gina fim din, kamar wajen da ya kawo misalin idan za a rubuta labarin da ya faru a 1960 ba za a kawo maganar yarinya tana tuyar awara ba, saboda da babu ita a wancan lokacin.

Haka nan ya yi dogon bayani a kan daidaita labari da kuma yadda za a ƙirƙiri jigon labarin da yadda za a tafi da shi har zuwa ƙarshe ba tare da ya karye ba.

Mahalarta taron, ɓangaren mata
Wasu daga cikin mata mahalarta

Shi kuwa Nasir Umar Ciromawa, wato ‘Nasir NID’, ya yi jawabi ne a kan hanyar fitar da labari da ya shafi isar da saƙo, inda ya kawo misalai da finafinan tashar Arewa 24 waɗanda labarai ne da ake tsara su waɗanda ake shigar da saƙo a cikin su, ta yadda kana cikin kallo sai a shigar maka da saƙo kuma ka rinƙa ganin sa a wani ɓangare na fim ɗin.

Ita kuma Fauziyya D. Sulaiman ta yi jawabi ne a kan samar da jarumi a cikin labarin fim da yadda jarumin ya kamata ya zama tun daga farko ya kasance ya dace da wajen da aka saka shi yadda masu kallo za su gamsu da sakon da ake so a nuna musu
Zuwairiyya Adamu Girei kuwa ta gabatar da nata jawabin ne a kan yadda sababbin marubuta ya kamata su kasance wajen koyar rubutun nasu.

Ta ce, “Tun da farko sai marubuci ya ajiye tunanin zai yi kuɗi, kawai ya ji a ran sa zai yi rubutu ne domin isar da saƙo. Za ka iya yin kuɗi, kuma za ta yiwu ka yi rubutun ba ka yi kuɗi ba, amma dai ana so a samu kuɗin, sai dai kada ya zama kuɗi shi ne a gaba.”

Ta ci gaba da cewa, “A yanzu muna buƙatar sabbin marubuta masu tasowa saboda mu da aka sani a yanzu, lokaci na zuwa ko mun ƙi ko mun so dole mu bar harkar ga ‘yan baya.

“Saboda bayan mu ta yi kyau ne muka ga dacewar mu samar da waɗanda za su gaje mu ta yadda za su tafiyar da harkar, mu kuma muna gefe a matsayin masu bayar da shawara.”

Shi kuwa Shugaban NFC, Malam Ali Nuhu, a matsayin sa na baƙo mai jawabi.

Ya nuna matuƙar farin cikin sa ga yadda ya samu kan sa cikin mahalarta taron. A cewar sa, “Yadda na ga mutanen da suka halarci wannan taro na tabbatar da samun nasarar da aka shirya taron domin ta. Saboda na ga fuskokin mutane masu buƙatar su koyi abin da ake so a koya musu, don tun da na shigo wajen na gan su a natse suna fuskantar abin da suke koya.”

Don haka ya yi kira a gare su da su mayar da hankali wajen cimma nasarar abin da suka sa gaba, domin ta haka ne za a samar da marubutan labarin fim da ake bukata a nan gaba da za su tafiyar da harkar.

Haka nan ya yaba da yadda ya ga mafi yawancin mutanen da suke karbar horon mata ne, waɗanda ko da suka zaune a gidan auren su, za su ci gajiyar harkar domin su rike kan su da iyalin su.

An dai shafe tsawon wuni guda ana gudanar da taron wanda bayan amsa tambayoyin mahalarta aka rufe da misalin ƙarfe da 5:30 na yamma.

Loading

Previous Post

Sarkin Daura ya naɗa Rarara Sarkin Waƙar Ƙasar Hausa

Next Post

Ɗaha, ɗan tsohuwar jaruma Halima Adamu Yahaya ya yi saukar Alƙur’ani 

Related Posts

Mutuwar aure na ƙaddara ce – Jaruma Khadija Yobe
Labarai

Mutuwar aure na ƙaddara ce – Jaruma Khadija Yobe

August 23, 2026
Aina’u Ade ta raba wa tsofaffin jaruman Kannywood tallafin kuɗi
Labarai

Aina’u Ade ta raba wa tsofaffin jaruman Kannywood tallafin kuɗi

August 23, 2026
Ƙungiyar ‘Triple R Kannywood’ ta ziyarci jarumi Tanimu Akawu a asibiti
Labarai

Ƙungiyar ‘Triple R Kannywood’ ta ziyarci jarumi Tanimu Akawu a asibiti

August 23, 2026
Ƙungiyar Triple R ta ba jarumin Kannywood Mustapha Musty tallafin N500,000
Labarai

Ƙungiyar Triple R ta ba jarumin Kannywood Mustapha Musty tallafin N500,000

August 18, 2026
Yadda na gamu da ibtila’in karaya a ƙafa – Jarumi Ɗan’azumi Kamaye
Labarai

Yadda na gamu da ibtila’in karaya a ƙafa – Jarumi Ɗan’azumi Kamaye

August 14, 2026
Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba
Labarai

Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba

August 8, 2026
Next Post
Ɗaha, ɗan tsohuwar jaruma Halima Adamu Yahaya ya yi saukar Alƙur’ani 

Ɗaha, ɗan tsohuwar jaruma Halima Adamu Yahaya ya yi saukar Alƙur'ani 

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!