TSOHON Editan mujallar Fim kuma fitaccen jarumi a Kannywood, Malam Aliyu Abdullahi Gora II, ya aurar da ‘yar sa ta biyu, Zainab, a ranar Asabar, 28 ga Disamba, 2024.
An ɗaura auren Zainab A. Gora II da abin ƙaunar ta Sadiq Ahmad da misalin ƙarfe 1:30 na rana a Masallacin Juma’a na Abubakar Mahmud Gumi da ke Malali Low-Cost, Kaduna, bisa sadaki N150,000.

Bayan an ɗaura auren, an yi walima a Gambia Street, inda ‘yan’uwa da abokan arziki suka halarta. An ci, an sha, an gyatse.
Mahaifin amaryar ya yi godiya ga Allah da waɗanda suka halarci ɗaurin auren, inda ya ce, “Na gode wa Allah da ya ba ni ikon sauke wannan nauyi. Na gode wa Allah, na gode wa Allah, na gode wa Allah.
“Kuma gaskiya ina godiya ga ɗimbin mutanen da suka halarci wannan ɗaurin aure. Waɗanda ban yi tsammani ba ma na gan su. Allah ya bar zumunci.


“Haka kuma ina godiya ga waɗanda suka ba ni gudunmawa. Akwai waɗanda suka ba ni gudunmawa ta kuɗi, akwai waɗanda suka ba ni gudunmawa ta addu’a, akwai waɗanda suka yi mani fatan alkhairi da sauran su. Dukkan su masoya na ne. Na gode ƙwarai da gaske. Ubangiji Allah ya saka wa kowa da alkairi.”
Allah ya ba su zaman lafiya da zuri’a ɗayyiba.
![]()







