WATA ƙungiyar addinin Musulunci ta naɗa furodusa kuma tsohuwar jarumar Kannywood, Mansurah Isah, a matsayin uwar marayun ƙungiyar Musulmi ta NASFAT tare da ba ta kambun girmamawa.
Ƙungiyar, mai suna Annur the Light of Islamic Teachings, ta naɗa jarumar ne tare da karramawar a wani taro da ta gudanar a ranar Asabar, 14 ga Disamba a ofishin ta da ke Titin Abeokuta cikin Sabon Garin Kano.
Ƙungiyar ta bai wa Mansurah muƙamin saboda irin gudunmawar da take yi wa marayu na ba su abinci da sutura da kuma kula da lafiya, da sauran abubuwa na buƙatun yau da kullum.
Mansurah ta nuna farin cikin ta da irin wannan abin alheri da aka yi mata da aka zaɓo ta daga cikin ɗimbin jama’a aka ba ta wannan matsayi da kuma karramawa.
A cewar ta, “Wannan wani al’amari ne na Allah, da yake yi wa bayin sa baiwa ta inda ya so, don haka ina godiya a gare shi. Kuma ina godiya ga ita ƙungiyar Annur da suka ga abubuwan da nake yi na alheri suka ba ni wannan kambu na girmamawa.”
Ta ƙara da cewa, “Wannan ya ƙara mini ƙaimi a kan abin da nake yi na taimaka wa mutane wajen samar musu da rayuwa mai kyau da inganci.
“Kuma ina roƙon Allah da ya ƙara ba ni damar faɗaɗa abin da nake yi har ya fi wanda aka gani a baya.
“Kuma ina roƙon Allah ya zama duk abin da zan yi ya zama ina yi ne domin sa.”
Mansurah ta samu ‘yan rakiya cikin ƙawayen ta da kuma abokan arziki, waɗanda suka haɗa da Saddika J Sarki, Jamila Gamdare, Ladidi Tubles, Fati Sulaiman, da Nura Mado.