• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Thursday, May 14, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Za a ƙarfafa gyare-gyaren tsarin tattalin arziki da Tinubu ke yi a 2025, inji Ministan Yaɗa Labarai

by WAKILIN MU
December 17, 2024
in Nijeriya
0
Za a ƙarfafa gyare-gyaren tsarin tattalin arziki da Tinubu ke yi a 2025, inji Ministan Yaɗa Labarai

Minista Mohammed Idris yana gabatar da jawabin sa a taron na VON

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

MINISTAN Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya tabbatar da cewa shekarar 2025 za ta zama shekarar da za a ƙarfafa gyare-gyaren da ake aiwatarwa ƙarƙashin Ajandar Sabunta Fata ta Shugaba Bola Ahmed Tinubu, waɗanda tuni suke haifar da sakamako mai kyau a fannonin tsarin tattalin arziki.

Idris ya bayyana haka ne a ranar Talata a Abuja a wurin taron atisayen shugabanci da gudanarwa wanda gidan rediyon Muryar Nijeriya (VON) ya shirya wa ma’aikatan sa.

A jawabin sa, Idris ya jaddada rawar da kafafen yaɗa labarai ke takawa wajen bayyana nasarorin gwamnatin.

Ya ce: “Babu tantama, ina tabbatar maku da cewa shekarar 2025 za ta ƙarfafa gyare-gyaren Ajandar Sabunta Fata ta Shugaban Ƙasa, waɗanda tuni suke haifar da sakamako mai kyau a fannoni daban-daban na rayuwar mu ta zamantakewa, tattalin arziki, da siyasa.”

Ministan ya jaddada shirin Shugaba Tinubu na aiwatar da manyan gyare-gyaren kuɗi don ƙara wa jihohi da ƙananan hukumomi yawan kuɗaɗen da suke samu domin ciyar da al’ummar Nijeriya gaba, bisa tsarin gaskiya na tarayya.

Wani sashe na mahalartan taron

Ya yi kira ga VON, a matsayin sa na gidan watsa labaran ƙasa da ƙasa, da ya bayyana wa da duniya nasarorin da Nijeriya take samu.

Ya ce, “Dole ne gidan rediyon Muryar Nijeriya ya sanar wa da duniya cewa Nijeriya ta dawo kan turbar aiki; cewa muna samun nasara a yaƙin da muke yi da ta’addanci, ’yan fashi, da rikicin ƙabilanci; cewa muna ƙarfafa al’ummar mu domin samar da cigaba mai ɗorewa; cewa matasan mu sun samu hanya mafi sauƙi don ilimi mai inganci ta hanyar Asusun Ba da Lamuni na Ilimi na Ƙasa (NEL), sannan kuma abu mafi muhimmanci, cewa ƙasar mu tana kan matakin sauyin makamashi wanda zai tabbatar da wutar lantarki da iskar gas mai ɗorewa don amfani a gidaje da masana’antu.”

Ya ƙara da cewa dole ne VON ta tabbatar “ba a bar giɓi ba wajen tattara nasarorin da Nijeriya take samu” ta hanyar rahotanni da nazari da ake watsa wa al’ummar duniya.

Idris ya nanata cewa gwamnati za ta ci gaba da amfani da damar da VON take da ita domin yaƙar barazanar labaran ƙarya waɗanda ke barazana ga ƙasar nan a matakin duniya.

Ministan ya yi kira ga ƙungiyoyin kafofin watsa labarai kamar VON da su rungumi fasahohin zamani domin su ci gaba da yin gogayya a duniyar watsa labarai, tare da inganta inganci da isar da shirye-shiryen su.

Ya kuma yaba wa Darakta-Janar na VON, Malam Jibrin Baba Ndace, tare da masu gudanarwa da ma’aikatan VON bisa sadaukarwar su da hangen nesa wajen tafiyar da hukumar zuwa ga kyakkyawan aiki.

Daga hagu: Darakta Janar na Muryar Nijeriya (VON), Malam Jibrin Baba Ndace; Minista, Mohammed Idris; Daraktar Kula da Ofishin Babbar Sakatare a Ma’aikatar Yaɗa Labarai, Madam Comfort Ajiboye; tsohon Darakta Janar na VON, Mista Osita Okechukwu; Jakaden ƙasar Bulgeriya a Nijeriya, Mista Yanko Yordanov, da Darakta-Janar na FRCN, Dakta Mohammed Bulama, a taron na VON

Loading

Tags: Jibrin Baba NdaceMohammed Idristattalin arzikiVoice of Nigeria (VON)
Previous Post

Ƙungiyar Annur ta karrama furodusa Mansurah Isah

Next Post

Ministan Yaɗa Labarai ya ƙaddamar da ginin Radio House da aka gyara, tare da alƙawarin ƙarin gyare-gyare

Related Posts

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa
Nijeriya

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa

November 7, 2025
Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji
Nijeriya

Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji

November 2, 2025
Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba
Nijeriya

Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba

November 2, 2025
Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje
Nijeriya

Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje

October 29, 2025
Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai
Nijeriya

Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai

August 31, 2025
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar da Sababbin Cibiyoyin Maganin Ciwon Daji

July 24, 2025
Next Post
Ministan Yaɗa Labarai ya ƙaddamar da ginin Radio House da aka gyara, tare da alƙawarin ƙarin gyare-gyare

Ministan Yaɗa Labarai ya ƙaddamar da ginin Radio House da aka gyara, tare da alƙawarin ƙarin gyare-gyare

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!