ƊALIBAI ‘yan Nijeriya da ke karatu a wata jami’a a ƙasar Indiya sun karrama fitacciyar jarumar Kannywood, Rahama Sadau, wadda a yanzu ta ke ƙasar domin ɗaukar wani fim.
Rahama ta je Indiya ne bisa gayyata domin fitowa a fim ɗin gumurzu mai suna ‘Khuda Haafiz’ kashi na 2.
Ana shirya fim ɗin ne a Lucknow, babban birnin jihar Utter Pradesh.

Jami’ar, mai suna Integral University, makaranta ce mai zaman kan ta wadda ke cikin garin na Lucknow, kuma akwai ‘yan Nijeriya da ke karatu a cikin ta.

Jin cewa ga Rahama Sadau a garin ya sa su ka kira ta domin su karrama ta saboda Hausawa sun ce kowa ya ga na gida, ya rasa ahu.
An ɗan yi jawabai da musabiha, inda aka gwarzanta jarumar tare da lissafa nasarorin da ta samu a fagen shirya finafinai a Nijeriya.

A saƙon godiya da ta wallafa a Instagram a yau, jarumar ta bayyana jin daɗin ta, ta na faɗin, “Na yi matuƙar alfahari tare da jin daɗi da na samu gayyata daga ɗalibai ‘yan Nijeriya da ke karatu a ‘Integral University’ ta Indiya.
“Na kasa ɓoye farin ciki na dangane da wannan kyakkyawar karramawa, wadda ke da muhimmanci sosai a gare ni.

“Ku ma ma’aikatan ‘Integral University’, kyakkyawar karɓar da ku ka yi mani abar so ce kuma abar godiya har abada. Sannan su ma ɗalibai masu sadaukarwa da ƙwazo na wannan jami’a mai mutunci waɗanda su ka shirya wannan taro domin karrama zuwa na, kun samu gurbi na musamman a cikin zuciya ta. Na gode da kyautar da ku ka ba ni da komai da komai. Soyayya mai yawa a gare ku.”
Idan ba ku manta ba, mujallar Fim ta ba ku labarin zuwan Rahama Indiya domin shirya fim ɗin na ‘Khuda Haafiz’ kashi na 2.

Kamfanin ‘Panorama Studios’ na masana’antar shirya finafinan Indiya, wato Bollywood, shi ne ya ɗauki nauyin shirya shi, kuma darakta Faruk Kabir ne ke bada umarni.
Kashi na farko na fim ɗin ya fito ne a cikin Agusta, 2020.

Sai dai har yanzu ba mu san rol ɗin da aka ba Rahama Sadau a cigaban labarin fim ɗin da ake ɗauka ba.