A wani yunƙuri na haɗa kan ƙungiyoyin sha’irai dake faɗin Jihar Kano domin su zama tsintsiya maɗaurin ki ɗaya, Hukumar Tace Finafinai da Dab’i ta Jihar Kano ta shirya haɗin gwiwa da gamayyar ƙungiyoyin sha’iran Jihar Kano inda suka gabatar da wani gagarumin taron Maulidi domin tunawa da zagayowar ranar da aka haifi fiyayyen halitta Manzon tsira Annabi Muhammad S.AW.
Taron maulidin wanda aka gabatar a harabar Gidan Talabijin na Abubakar Rimi (ARTV), dake titin Maiduguri a Unguwar Hotoro a cikin garin Kano, ya samu halartar ɗimbin al’umma, malamai, attajirai da manyan jami’an gwamnatin Jihar Kano.
Tun da farko da yake jawabi, Shugaban Hukumar Tace Finafinai da Dab’i ta Jihar Kano, Abba El-Mustapha, ya gode wa Allah da ya bashi nasarar shirya maulidin wanda shi ne irinsa na farko da hukumar ta taɓa shiryawa domin nuna ƙauna ga fiyayyen halitta manzon tsira Annabi Muhammad (s.a.w).
Ya ƙara da cewa “manufar shirya wannan taron, baya ga murna da zagayowar ranar da aka haifi Manzo S.A.W shi ne samar da wani dandamali na haɗuwar ƙungiyoyin sha’irai su haɗu a wajen guda domin kyautata alaƙar juna da kuma tafiya tare, domin a duk wani al’amari na tafiya ana bukatar samar da haduwa da tafiya tare domin cimma manufa.
To mu a namu tsarin tun da na samu jagorancin a wannan Hukumar, babban abin da na saka a gaba, shi ne samar da hadin kai da fahimtar juna a tsakanin dukkan wanda yaka a karkashin wannan Hukumar. Don haka muka tashi tsare babu dare babu rana saboda a samu kyakkyawan hadin kai da kuma jagoranci a tsakanin mu da kungiyoyin da suke karkashin wannan Hukumar.
Wannan taro ya zama abin misali da irin yadda manufarmu take tafiya a bisa tsari, saboda wannan shi ne taro na farko da ya hada dukkanin kungiyoyin sha’irai da suke fadin Jihar Kano, aka taru a waje guda domin gudanar taron Maulidin kuma a nan za ku ga shugabanni da kuma mambobin su na dukkan kungiyoyin sha’irai da suke fadin Jihar Kano sun hadu a nan suna gabatar da kasidun yabon Manzon Allah S A W, don haka ina kira ga dukkan kungiyoyin sha’irai, da sauran kungiyoyin da suke karkashin wannan Hukumar, da hadu mu yi aiki tare domin cimma manufar wannan Hukumar ta kyautata tarbiyya da kawo tsarin da ya dace da addini da kyawawan al’adu na Jihar Kano.
A yayin taron Maulidin dai sha’irai da dama maza da mata sun gabatar da ƙasidun na yabo ga Annabi.
Cikin waɗanda suka rera ƙasidu a wajen sun haɗa da Malam Sidi Abba, Mal. Bashir Dan Musa, Mal. Bashir Dandago, Munhamina Hafiz Auwal, Umar Gawuna, Jamilu Nalado Faruq Ibrahim, Ayagi Mustapha, Ali Indabawa.
A ɓangaren sha’irai mata akwai Sayyada Murja Hafiz Abdullah da ta gabatar da ƙasida sai Fatima Labaran Kabara, Naja’atu ta Annabi, da Sayyada Rumaisa Muhammad da dai sauransu.
Taron ba iya ƙasidu ya tsaya ba domin kuwa Sheikh Ibrahim Khalil Shugaban Majalisar Malami ta Jahar Kano ya gabatar da jawabi a kan muhimmancin yin koyi da ayyukan Manzo S A W, in da yake cewa shi son Manzo S A W ba ya tsaya a fatar baki ba ne a rinka ana son sa ba ne, aiki da biyayya a kan dukkan yadda ya gudanar da rayuwar shi ne abin da ya zama wajibi a kan duk wani Musulmi, domin haka babban abiin da za mu nuna na son Manzon Allah shi ne a ga ayyukan sa a tare da mu a wajen mu’amala wannan shi ne tsantsan son Manzo S A W.
Shi ma a matsayin sa na babban baƙo a wajen, Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar Kano, Baba Halilu Dantiye, ya yi kira ga al’ummar Musulmi da su yi riƙo da halaye na Manzon Allah kuma su suffantu da shi.
Ya kuma yi kira ga ƙungiyoyin sha’irai da su tashi tsaye wajen faɗakar da jama’a haƙiƙanin yadda son Manzo yake, sannan kuma su cire ƙyashi da yake tsakanin su don a taru a yi tafiya tare.
Haka ita ma Kwamishinayar Raya Al’adu da Yawon Buɗe Ido ta Jihar Kano, Hajiya Ladidi Garko, ta yi jawabi tare da bayyana jin daɗin ta da shirya taron Maulidin in da ta yi fatan ɗorewar hakan.
Manyan mutane da kuma shugabanni daga hukumomin Jihar Kano suka halarta, cikin su akwai Shugaban Hukumar Raya Al’adu da Yawon Buɗe Ido ta Jihar Kano Alhaji Tukur Sagagi, Shugaban Tashar Radio Kano, Alhaji Rano, Shugaba Tashar Talabijin ta Abubakar Rimi, Hajiya Hauwa Muhammad, dai sauransu.