Shugaban Ƙungiyar Tuntuɓa ta Matasan Arewa (AYCF) na ƙasa, Alhaji Yerima Usman Shettima, ya bayyana mahaifin Rahama Sadau a matsayin mutumin kirki, mai son jama’a.
Yerima, wanda shi ne mijin tsohuwar jarumar Kannywood Fati Ladan, ya yi wannan bayani ne a lokacin da ya je ta’aziyya gidan marigayin, wato marigayi Alhaji Ibrahim Sadau.
Shugaban ya shaida wa mujallar Fim cewa, “Haƙiƙa duk wanda ya san Alhaji Ibrahim Sadau, ya san cewa mutum ne mai kirki da son jama’a. Ko da na wannan wuri na ƙara tabbatar da haka.
“Babu abin da ya kamata mu yi masa a yanzu da ya wuce addu’ar neman gafara da rahama a gare shi.”
Ya ƙara da cewa, “Muna kuma fatan halayen sa na kirki su bi shi. Allah ya yafe masa kurakuran sa, Allah ya albarkaci dukkan zuri’ar sa.”


Yerima da tawagar sa sun isa gidan su Rahama da misalin ƙarfe 5:00 na yamma, inda kai-tsaye aka yi masu jagora zuwa inda Rahama take.
An gudanar da addu’o’in neman gafara ga mamacin, wadda Malam Ibrahim PDP ya jagoranta.
Haka kuma sun shiga cikin falon da Hajiya Bilkisu, wato mahaifiyar su Rahama take, sun yi mata ta’aziyya tare da yin addu’o’i.
Daga nan kuma suka fita waje inda ‘yan’uwan mamacin suke, nan ma suka yi masu gaisuwa da addu’a.
Rahama da ‘yan’uwan ta sun yi wa su Yerima godiya da fatan Allah ya maida su gida lafiya.