SHAHARARREN furodusan finafinai ɗin nan ɗan Nijeriya, Kunle Afolayan, a yau ya rattaba hannu kan wata yarjejeniya da gwamnatin Jamhuriyar Benin da nufin sauya fasalin harkokin shirya finafinai da na kafafen sauti da na gani a yankin Yammacin Afrika.
An sanya hannu kan yarjejeniyar wadda aka bayyana da matsayin wani “muhimmin mataki da zai sake fasalta makomar bayar da labaran Afrika da haɗin gwiwar ƙirƙira tsakanin ƙasashe,” a KAP Hub — cibiyar ƙirƙire-ƙirƙire ta Kunle Afolayan kuma hedikwatar kamfanin sa na KAP Group — da ke Legas.
An ƙulla yarjejeniyar ne tsakanin KAP Group na Afolayan da manyan wakilan gwamnatin ƙasar Benin, bayan wata gayyata daga Fadar Shugaban Ƙasar Benin.
A cikin wata sanarwa da KAP Group ya fitar a ysu, an ce taron rattaba hannun “ya nuna wani sabon babban haɗin gwiwar nahiyar Afrika da kamfanin ke jagoranta, tare da ƙarfafa rawar da yake takawa wajen gina dabarun haɗin gwiwar ƙirƙira a nahiyar, domin bunƙasa finafinan Afrika, bai wa matasa dama, da gina ingantattun kayayyakin more rayuwa da za su iya gogayya a duniya.”
Sanarwar ta ƙara da cewa: “Wannan haɗin gwiwa mai tarihi yana nuna hangen nesa iri ɗaya na amfani da ƙarfin finafinai, cigaban matasa da kasuwancin ƙirƙira a matsayin hanyoyin diflomasiyyar al’adu, haɓakar tattalin arziki, da ƙarfafa tasirin ƙirƙira ta Afrika a duniya.”
An bayyana cewa, a wani ɓangare na shirin tattaunawar, Afolayan tare da Daraktan Zartarwa na KAP Group, ’Seun Soyinka, a watan da ya gabata suka jagoranci wata tawagar manyan jami’an gudanarwar kamfanin zuwa Jamhuriyar Benin, inda suka yi tattaunawa mai zurfi da manyan jami’an gwamnati da masu ruwa da tsaki a fannin finafinai da kafafen sauti da na gani.
Tattaunawar ta mayar da hankali ne kan gina tsare-tsare masu ɗorewa domin bunƙasa samar da cigaba a cikin gida, ƙarfafa ƙwarewar fasaha, da kuma mayar da Jamhuriyar Benin wata cibiya mai tasowa a fagen finafinai da ƙirƙira a Afrika.

Rattaba hannun da aka yi a yau ta biyo bayan umurnin da Shugaban Ƙasar Benin ya bayar, wanda hakan ya tabbatar da fara aiwatar da wannan haɗin gwiwa mai sauyi a hukumance.
Membobin tawagar da suka halarci rattaba hannun sun haɗa da: Sinatou Saka, Mai Bai wa Shugaban Ƙasar Benin Shawara ta Musamman kan Harkokin Yaɗa Labarai da Kafafen Sauti da na Gani; Coline-Lee Toumson-Venite, Mai Bai wa Shugaban Ƙasar Shawara kan Fasaha da Al’adu; Bassirou Ndiaye, Shugaban Kamfanin SOPA S.A.; Faissol Gnonlonfin, Daraktan Finafinai da Wasannin Kwaikwayo a Hukumar Bunƙasa Fasaha da Al’adu (ADAC), wanda ya wakilci Ministan Al’adu; da Meto Adoglo, Manajan Shirye-shiryen Labarai a Sèmè City.
Ɓangaren mai masaukin baƙi ya samu jagoranci daga Shugaban KAP Group, Daraktan Zartarwa, da Farfesa Tunji Azeez, Shugaban makarantar KAP Film & Television Academy.
Sabuwar haɗin gwiwar ta ta’allaƙa ne kan ginshiƙai uku: haɗin gwiwar shirya finafinai da za su ba da sahihan labaran Afrika tare da faɗaɗa tasirin su a duniya; tsare-tsaren horas da matasa a dukkan ɓangarorin shirya finafinai da ƙirƙira; da kuma gina tare da samar da kayayyaki da gudanar da wani Birnin Finafinai (Film City) mai inganci a garin Ouidah, Benin.
Waɗannan ginshiƙai uku za su amfana sosai daga ƙwarewar wasu rassan KAP Group kamar KAP Motion Pictures, KAP Film & Television Academy da KAP Film Village & Resort.
An tsara cewa daga yau ranar 19 zuwa ranar 22 ga Fabrairu, tawagar za ta ziyarci cibiyar shirya finafinai ta KAP Group da ke Legas, da kuma KAP Film Village & Resort da ke ƙauyen Igbojaye-Komu a Jihar Oyo — wadda wata cibiyar ƙirƙira ce da ake kallon sa a matsayin abin koyi wajen haɗa shirya finafinai, horaswa da yawon buɗe ido na al’adu a Afrika.
Da yake jawabi kan wannan cigaba da aka samu, Afolayan ya bayyana haɗin gwiwar a matsayin “wani muhimmin lokaci ga finafinan Afrika, inda shugabanci mai hangen nesa, sahihancin al’adu da kasuwancin ƙirƙira suka haɗu domin nuna labaran mu, mutanen mu da ƙarfin ƙirƙirar mu ga duniya ta hanya mafi jan hankali.”
Ita ma Sinatou Saka, Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara ta Musamman kan Harkokin Yaɗa Labarai da Kafafen Sauti da na Gani a ƙasar Benin, ta nuna farin ciki da yadda aka kammala yarjejeniyar.
“Mun yi farin ciki matuƙa da fara wannan haɗin gwiwa da Kunle Afolayan, musamman a ɓangaren gina ƙwarewa,” inji ta.
Ɓangarorin biyu sun bayyana yarjejeniyar a matsayin farkon ƙulla wata doguwar alaƙa ta dabarun haɗin gwiwa da za ta ɗaga darajar shirya finafinai, ilimin ƙirƙira da bayyana al’adun Afrika.
Sanarwar ta ƙara da cewa: “Wannan haɗin gwiwa ya ƙara tabbatar da rawar gani da KAP Group ke takawa wajen sauya labarin finafinan Afrika ta hanyar ƙirƙira, haɓaka hazaƙa da gina kayayyakin more rayuwa.
“Kunle Afolayan yana ci gaba da jagorantar haɗin gwiwar ƙirƙira a faɗin Afrika, yana ƙarfafa murya ɗaya ta nahiyar tare da gabatar da sahihan labaran Afrika a idon duniya cikin ƙwarewa da alfaharin al’adu.”
Haka kuma an bayyana cewa KAP Group kamfani ne na Afrika da ke kan gaba a fannin ƙirƙira da shirya finafinai, talbijin, horo, baƙunci da bunƙasa al’adu.
“Ta hanyar ƙirƙira, gina kayayyakin more rayuwa da haɓaka hazaƙa, kamfanin yana ci gaba da tallafa wa sahihancin al’adun Afrika da labaran ta tare da gina tsarin ƙirƙira mai iya gogayya a duniya.”
![]()







