Daraktar fim ɗin nan da ya ja hankalin Duniya, wato ‘The Voice of Hind Rajab’, ta ƙi karɓar lambar yabo a wani taro da aka gudanar a Berlin babban birnin ƙasar Jamus a wannan makon, bayan da aka karrama wani Janar na sojojin Isra’ila a wajen taron.
Jaridar Middle East Monitor ta ruwaito cewa kamfanin dillancin labarai na Anadolu ya ba da labarin yadda darakta Kaouther Ben Hania, wadda ’yar ƙasar Tunisiya ce, ta zaɓi kada ta karɓi lambar yabo ta “Most Valuable Film” a wajen bikin “Cinema for Peace” da aka gudanar ranar Litinin, inda ta bar kofin karramawar a wurin.
A jawabin da ta gabatar, ta ce maimakon jin daɗi, ta jin wani irin nauyi a rai ne, kuma ta yi amfani da damar wajen yin magana kan batun adalci da ɗaukar nauyin abin da aka aikata dangane da Hind Rajab, wata yarinya ‘yar ƙasar Falasɗinu mai shekara biyar da sojojin Isra’ila suka kashe a Zirin Gaza a cikin 2024, yayin da ma’aikatan ceto da suka yi ƙoƙarin kai mata ɗauki su ma aka buɗe musu wuta.
Ta ce: “Adalci yana nufin ɗaukar nauyin abin da ka aikata. Ba tare da ɗaukar nauyin ba, babu zaman lafiya.
“Sojojin Isra’ila sun kashe Hind Rajab; sun kashe iyalan ta; sun kashe ma’aikatan jinya guda biyu da suka zo domin ceton ta, tare da goyon bayan gwamnatoci da cibiyoyi mafi ƙarfi a duniya.
“Na ƙi barin mutuwar su ta zama wani abin ƙawata jawabi na ladabi game da zaman lafiya. Ba a lokacin da tsarin da ya ba da damar hakan yake nan daram ba.”
Ta ƙara da cewa, “Saboda haka, a daren yau, ba zan kai wannan lambar yabo gida ba. Na bar ta a nan a matsayin tunatarwa. Kuma idan aka nemi zaman lafiya a matsayin wajibi na doka da ɗabi’a, wanda ya samo asali daga ɗaukar nauyin abin da aka aikata na kisan kiyashi, to zan dawo in karɓe ta cikin farin ciki.”
Ben Hania ta ƙara da cewa mutuwar Hind “ba lamari ne na daban ba, wani ɓangare ne na kisan kiyashi.”
Ta yi suka kan wasu ‘yan siyasa da ke bayyana kashe ɗimbin fararen hula a Gaza da matsayin “kare kai” ko “matsaloli masu rikitarwa,” yayin da suke tauye masu zanga-zanga.
“Zaman lafiya yana buƙatar adalci da ɗaukar nauyi, ba kyawawan kalamai masu sheƙi kawai ba,” inji ta.
Shi dai fim ɗin ‘The Voice of Hind Rajab’, an shirya shi ne kan labari na gaskiya na ƙaramar yarinya Hind Rajab, wadda ta maƙale a cikin motar gidan su a ranar 29 ga Janairu, 2024, bayan da sojojin Isra’ila suka buɗe musu wuta a birnin Gaza, kuma daga baya aka same ta a mace bayan kusan makonni biyu na rashin tabbacin inda take.
![]()







