• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Monday, October 12, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

An naɗa Farfesa Tengya matsayin sabon shugaban Cibiyar Koyon Finafinai ta Ƙasa

by IRO MAMMAN
February 15, 2026
in Labarai
0
An naɗa Farfesa Tengya matsayin sabon shugaban Cibiyar Koyon Finafinai ta Ƙasa

Farfesa Pomak Frank Tengya

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

Gwamnatin Tarayya ta naɗa Farfesa Pomak Frank Tengya a matsayin sabon Rekta na Cibiyar Koyon Finafinai ta Ƙasa (National Film Institute, NFI) da ke Jos, Jihar Filato.

NFI dai ita ce babbar cibiyar koyar da harkokin finafinai a Nijeriya.

A wata sanarwa da ya fitar a Jos, Mista Brian Etuk, kakakin Hukumar Finafinai ta Nijeriya (NFC) – wadda ita ce ke mai kula da NFI – ya bayyana cewa sharuɗɗan naɗin Farfesa Tengya sun bi tanade-tanaden dokokin aikin gwamnati na Nijeriya da suka shafi tura ma’aikata aiki (wato Secondment Provisions of the Nigerian Public Service Rules and Regulations).

Naɗin nasa zai fara aiki ne daga ranar 1 ga Maris, 2026.

Kafin wannan naɗi, Tengya yana aiki ne a Sashen Nazarin Wasan Kwaikwayo da Finafinai na Jami’ar Jihar Taraba da ke Jalingo.

Sanarwar ta ce Farfesa Tengya, wanda ƙwararre ne a fannin Nazarin Wasan Kwaikwayo da Finafinai (Comparative Theatre and Film Studies), zai kawo gogewar sa ta ilimi da shugabanci da ya tara tsawon shekaru domin jagorantar NFI.

Ta ce: “Ya yi fice wajen jagoranci da bayar da gudunmawar ilimi a manyan jami’o’in Afrika, ciki har da Jami’ar Jos, Nijeriya; Jami’ar Kenyatta, Nairobi, Kenya; da Jami’ar Jihar Taraba, Jalingo, Nijeriya.

“Haka kuma, ya wallafa littattafai da muƙalu na ilimi da dama. Ya yi aiki a kwamitocin Majalisar Dattawan Jami’a (Senate), Kwaleji da Sassa daban-daban, sannan ya riƙe muƙamin Daraktan Hulɗa da Haɗin Gwiwar Ƙasa da Ƙasa a Jami’ar Jihar Taraba, Jalingo, har zuwa lokacin da aka naɗa shi a matsayin Rekta na NFI.”

Manajan Darakta/Shugaban Hukumar Hukumar Finafinai ta Nijeriya (NFC), Dakta Ali Nuhu, wanda kuma shi ne Shugaban Majalisar Gudanarwar NFI ɗin, ya taya Farfesa Pomak Frank Tengya murnar naɗi sa a matsayin sabon shugaban cibiyar, tare da shawartar sa da ya yi amfani da ɗimbin gogewar sa a sabon muƙamin sa.

Nuhu ya bayyana cewa naɗin Tengya ya zo a daidai lokacin da shugabannin NFC suke aiki tuƙuru domin ɗaga dukkan shirye-shiryen karatu da ake gabatarwa a NFI zuwa matakin ƙa’idojin duniya, tare da ingiza ajandar bunƙasa Tattalin Arzikin Ƙirƙira (Orange Economy) na ƙasa, musamman a fannin horas da ’yan kasuwa, gina ƙwarewa da bunƙasa basira.

Ya ce sake fasalin daidaita NFI ya kasance babban abin da shugabancin NFC ya bai wa fifiko a cikin shekaru biyu da suka gabata.

Ali Nuhu ya kuma jaddada cewa horaswa, gina ƙwarewa da bunƙasa basira a fannin shirya finafinai a NFI na da matuƙar muhimmanci wajen amfani da fasaha da sababbin hanyoyin koyarwa domin ƙarfafa ƙoƙarin ƙasa na bunƙasa tattalin arzikin ƙirƙira.

Sanarwar ta ƙara da cewa: “Sabon shirin digiri na biyu (Master’s) a fannin Al’adun Fim da Nazarin Taskar Finafinai (Film Culture & Archival Studies) da aka ƙaddamar kwanan nan, haɓaka shirye-shiryen digiri da difloma, da kuma yunƙurin neman abokan hulɗa na gida da waje domin bunƙasa kayayyakin more rayuwa, duk suna nuna ƙudirin NFC na tabbatar da cigaban NFI yadda ya kamata.”

Cibiyar Koyon Finafinai ta Ƙasa tana bayar da digiri na biyu na haɗin gwiwa a fannin Al’adun Fim da Nazarin Taskar Finafinai; Digirin Farko (Bachelor’s) a Fannin Fasahar Fim; Difloma; da kuma Shirye-shiryen Takardun Shaida na Ƙwarewar Kasuwanci na Musamman a fannin Shirya Finafinai.

Loading

Tags: AliNuhunaɗiNationalFilmInstituteNFCNFINigerianFilmCorporationPomakFrankTengya
Previous Post

Alƙali ya ci Samha Inuwa tara ko ta je kurkuku wata 6

Next Post

Fitaccen furodusa Kunle Afolayan ya yi haɗin gwiwa da Jamhuriyar Benin kan shirya finafinai

Related Posts

Hukumar Tace Finafinai ta karɓi uzirin Tijjani Gandu
Labarai

Hukumar Tace Finafinai ta karɓi uzirin Tijjani Gandu

October 6, 2026
Tinubu da Remi sun halarci bikin fara nuna fim kan gwagwarmayar Abiola
Labarai

Tinubu da Remi sun halarci bikin fara nuna fim kan gwagwarmayar Abiola

October 1, 2026
Cewar Ability: Ba mu kafa KAFIGAN don sharholiya a Kannywood ba
Labarai

Za a ƙaddamar da reshen Kaduna na KAFIGAN ranar Asabar

October 1, 2026
Zaɓen 2027: Shettima ya nemi goyon bayan ‘yan fim da mawaƙan Arewa wajen sake zaɓen Tinubu
Siyasa

Zaɓen 2027: Shettima ya nemi goyon bayan ‘yan fim da mawaƙan Arewa wajen sake zaɓen Tinubu

September 30, 2026
Ina roƙon Rarara ya saka ni cikin ‘Triple R’ domin in samu na abinci – Baba Duduwa
Siyasa

Ina roƙon Rarara ya saka ni cikin ‘Triple R’ domin in samu na abinci – Baba Duduwa

September 30, 2026
Guguwar zaɓen 2027: Sanata Barau Jibrin ya kori jaruma Rasheeda Maisa’a daga tafiyar sa
Siyasa

Guguwar zaɓen 2027: Sanata Barau Jibrin ya kori jaruma Rasheeda Maisa’a daga tafiyar sa

September 29, 2026
Next Post
Fitaccen furodusa Kunle Afolayan ya yi haɗin gwiwa da Jamhuriyar Benin kan shirya finafinai

Fitaccen furodusa Kunle Afolayan ya yi haɗin gwiwa da Jamhuriyar Benin kan shirya finafinai

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!