Wata kotu a Kano ta yanke wa jarumar Kannywood, Sa’adatu Mohammed Inuwa (wadda aka fi sani da Samha), hukuncin ɗaurin watanni shida ko kuma ta biya tarar N200,000.
Mai Shari’a S.M. Shu’aibu na Kotun Tarayya da ke zaman ta a Kano ne ya yanke hukuncin a yau Juma’a, 13 ga Fabrairu, 2026, bayan ya samu jarumar da laifin wulaƙanta da kuma lalata takardun Naira.
An gurfanar da jarumar ne kan tuhuma guda ɗaya da ta shafi lalata kuɗin Nijeriya, wanda hakan ya saɓa wa tanade-tanaden Dokar Babban Bankin Nijeriya (CBN Act), 2007.
Samha dai ta amsa laifin da ake tuhumar ta da shi bayan an karanta mata tuhumar a kotu.
Bisa ga amsa laifin da ta yi, sai lauyan gwamnati mai gabatar da ƙara, Musa Isah, ya yi bitar gaskiyar lamarin sannan ya roƙi kotu da ta same ta da laifi tare da yanke mata hukuncin da ya dace.
Jarumar ta roƙi kotu da ta yi mata sassauci, tana mai bayyana cewa wannan shi ne karo na farko da ta aikata laifi, kuma ta nuna nadama ta gaskiya kan abin da ta aikata.
Daga bisani, Mai Shari’a Shu’aibu ya same ta da laifi tare da yanke mata hukuncin ɗaurin watanni shida, tare da zaɓin biyan tarar Naira dubu ɗari biyu (N200,000.00) kacal.

Idan kun tuna, ofishin Shiyyar Kano na Hukumar Binciken Almundahanar Kuɗi (EFCC) ne suka kama Samha Inuwa, a ranar 3 ga Fabrairu bisa zargin wulaƙanta takardun naira.
An kama ta ne bayan ɓullar wani bidiyo da ta yi wanda ya yaɗu a soshiyal midiya inda aka gan ta ɓaro-ɓaro tana goge majina daga hancin ta da takardar naira.
Bayan ta amsa tambayoyin su ne suka tsare ta a cibiyar tsarewa ta hukumar domin gudanar da bincike.
Daga nan suka maka ta a kotu.
![]()







