• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, August 25, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Yadda mahaifin mu ya rasu kwana ɗaya bayan ya dawo daga Makkah – Abba, yayan Rahama Sadau

* Zan yi koyi da halin sa na riƙo da addini, inji shi

by ABBA MUHAMMAD
June 22, 2025
in Labarai
0
Yadda mahaifin mu ya rasu kwana ɗaya bayan ya dawo daga Makkah – Abba, yayan Rahama Sadau

Rahama Sadau da 'yan'uwan ta a lokacin da ake yi wa mahaifin su sallah

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram
Abba Sadau… a wani lokaci can baya

ABBA Sadau, yayan fitacciyar jaruma Rahama Sadau, ya bayyana alhini kan rasuwar mahaifin su, Alhaji Ibrahim Sadau, wanda ya kwanta dama a yau. Haka kuma ya faɗa wa mujallar Fim yadda ya rasu.

Mahaifin nasu dai ya rasu ne da asuba a yau, kwana ɗaya bayan dawowar sa daga aikin Hajji. (A jiya ya dawo, ba shekaranjiya ba kamar yadda rahoton mujallar Fim na farko ya ambata).

Ya rasu a asibitin sojoji mai suna 44 Nigerian Army Reference Hospital, Kaduna (Asibitin 44), da misalin ƙarfe 4:00 na asuba, bayan da ciwon sugar shi ya tashi.

An yi masa sallah da misalin ƙarfe 10:00 na safe, a harabar wata makarantar Islamiyya da ke kusa da gidan sa a kan Titin Lome, Unguwar Rimi, Kaduna.

Daga nan kuma aka kai shi gidan sa na gaskiya da ke babbar maƙabartar unguwar.

Ana yi wa Alhaji Ibrahim Sadau sallah
Jama’a ɗauke da gawar Alhaji Ibrahim Sadau a makara lokacin da aka shigo da shi maƙabarta

Dattijon, mai kimanin shekara 58, ya rasu ya bar mata biyu da ‘ya’ya tara. Rahama ita ce ‘yar sa ta biyu.

Mujallar Fim ta yi ƙoƙarin jin ta bakin Rahama Sadau, amma haka ya faskara, saboda irin yadda jama’a suka cika ɗakin da take.

Sai dai yayan ta, Haruna Sadau Ibrahim (wanda aka fi sani da sunan Abba Sadau), ya shaida wa mujallar Fim irin halin kiɗimewar da ya shiga sakamakon wancan rashin na mahaifin su.

Abba, wanda furodusa ne a Kannywood, ya ce, “Inna lillahi wa inna ilaihir raji’un! Wannan rashi ba mu taɓa yin shi ba a family ɗin mu gaba ɗaya, sai wannan karon ne muka fara samun irin wannan rashi babba, gaskiya.

“Kuma ya taɓa mu, ya taɓa kowa ma, don ni har yanzu ni ban gama yarda ba, domin jiya ya dawo daga Saudiyya, bayan ya dawo ya ce ba shi da lafiya, ya kira ni a waya ta ya ce in turo masa likita, na ce masa kamata ya yi ya je asibiti a yi masa general check-up, da yake ba yi tafiya.

“Ana kai shi asibitin, sai labari ya canza, jikin sai ya tashi sosai. Da ma yana da ciwo suga da sauran su.

“Muna ta waya da likitan da wadda take tare da shi, har dai aka ce lokaci ya yi. Allah ya ƙaddara a Nijeriya zai rasu.”

Dandazon mahalarta jana’izar a cikin maƙabartar Unguwar Rimi
Jama’a na yi wa marigayi Alhaji Ibrahim Sadau addu’a a bakin kabarin sa

Abba ya ci gaba da bayyana yadda zai riƙa tunawa da mahaifin nasu, ya ce, “Akwai abubuwa da yawa da zan riƙa tuna mahaifi na da su, amma abin da zan fi tunawa da shi, wanda kuma zan yi koyi da shi, shi ne ibada, domin ba za a taɓa zuwa masallaci ka gan shi a sahu na biyu ba, ko da yaushe a sahun farko za ka gan shi. In dai ibada ne, a gaba za ka gan shi; an shaide shi da haka.

“In godiya ga ‘yan Kannywood da sauran al’ummar da suka halarci jana’iza. Wallahi har ƙwalla na yi saboda irin dandazon jama’a da na gani. Allah ya saka wa kowa da alkhairi.”

Wakilin mu, wanda ya halarci jana’izar, ya ruwaito cewa wasu daga cikin ‘yan fim da suka halarci jana’izar da ta’aziyya sun haɗa da Yasin Auwal, Umar M. Shareef, Yusuf Lazio, Sa’adu Cousin, Muhammad Showman, Musty Fashion, A.A. Rasheed Kabala, Abdul S.D., Hajiya A’isha NTA, da Maryam Aliyu (Madam Korede).

Mawaƙi kuma jarumi Umar M. Shareef da darakta Yaseen Auwal suna yi mahaifiyar su Rahama Sadau ta’aziyya
Abba Sadau da Rahama Sadau tare da mahaifin su, marigayi Alhaji Ibrahim Sadau
Abba Sadau a cikin 2022

Loading

Tags: Abba SadauAlhaji Ibrahim SadauKannywoodRahama Sadaurasuwar mahaifi
Previous Post

Mahaifin Rahama Sadau ya rasu kwana 1 bayan ya dawo daga aikin Hajji

Next Post

Mahaifin Rahama Sadau mutumin kirki ne da son jama’a, inji Yerima Shettima

Related Posts

Mutuwar aure na ƙaddara ce – Jaruma Khadija Yobe
Labarai

Mutuwar aure na ƙaddara ce – Jaruma Khadija Yobe

August 23, 2026
Aina’u Ade ta raba wa tsofaffin jaruman Kannywood tallafin kuɗi
Labarai

Aina’u Ade ta raba wa tsofaffin jaruman Kannywood tallafin kuɗi

August 23, 2026
Ƙungiyar ‘Triple R Kannywood’ ta ziyarci jarumi Tanimu Akawu a asibiti
Labarai

Ƙungiyar ‘Triple R Kannywood’ ta ziyarci jarumi Tanimu Akawu a asibiti

August 23, 2026
Ƙungiyar Triple R ta ba jarumin Kannywood Mustapha Musty tallafin N500,000
Labarai

Ƙungiyar Triple R ta ba jarumin Kannywood Mustapha Musty tallafin N500,000

August 18, 2026
Yadda na gamu da ibtila’in karaya a ƙafa – Jarumi Ɗan’azumi Kamaye
Labarai

Yadda na gamu da ibtila’in karaya a ƙafa – Jarumi Ɗan’azumi Kamaye

August 14, 2026
Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba
Labarai

Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba

August 8, 2026
Next Post
Mahaifin Rahama Sadau mutumin kirki ne da son jama’a, inji Yerima Shettima

Mahaifin Rahama Sadau mutumin kirki ne da son jama'a, inji Yerima Shettima

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!