ALLAHU Akbar! Da asubahin yau Lahadi, Allah ya ɗauki ran mahaifin shahararriyar jaruma, Rahama Sadau, a Kaduna.
Rahama da kan ta ta bayyana wannan abin baƙin cikin a soshiyal midiya.
Su ma ƙannen ta sun bayyana labarin rasuwar a intanet.
Mujallar Fim ta ruwaito cewa a jiya Asabar ne dattijon ya dawo daga aikin Hajji, kuma ya rasu ne a wani asibiti sakamakon gajeren rashin lafiya.
Za a yi jana’izar sa anjima da misalin ƙarfe 10:00 na safe a gidan sa da ke Unguwar Rimi, Kaduna.

Alhaji Ibrahim Sadau ya rasu ya bar ‘ya’ya tara, amma shida aka fi sani saboda alaƙar su da industirin Kannywood, wato Abba da ƙannen sa Rahama, Zainab, A’isha, Fatima, sai kuma Baffa.
Ɗimbin ‘yan fim da sauran jama’a sun yi wa Rahama da ‘yan’uwan ta gaisuwa, suna addu’ar Allah ya jiƙan mahaifin nata.
Shugaban Hukumar Shirya Finafinai ta Nijeriya (NFC), Alhaji Ali Nuhu, ya yi ta’aziyya a soshiyal midiya, inda ya ce, “Inna lillahi wa inna ilaihir raji’un. Allah ya jiƙan shi da rahama, ya sa mutuwa hutu ne a gare shi. Allah ya ba wa iyalan shi da ‘yan’uwa haƙuri da juriyar rashin shi, amin.”
Ƙungiyar Kadawood da ke Kaduna ta miƙa ta’aziyyar ta ga Rahama Sadau.
Ƙungiyar, a ƙarƙashin jagorancin Malam Nura MC, ta ce, “A madadin dukkan membobin ƙungiyar Kadawood Film Makers, muna miƙa ta’aziyyar mu ta musamman ga Rahama Sadau da dukkan ‘yan’uwan ta, dangane da rasuwar mahaifin su.
“Haƙiƙa wannan babban rashi ne ba gare su kaɗai ba, har ma da al’umma baki ɗaya.
“Muna roƙon Allah maɗaukakin Sarki ya jiƙan mamacin, ya sa Aljanna ce makomar sa. Allah ya ba su haƙurin jure wannan babban rashin.”
Allah ya jiƙan Alhaji Ibrahim Sadau, amin.