• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Monday, April 6, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

2023: INEC ta bayyana wuraren da doka ta haramta yin kamfen da taron siyasa

by DAGA WAKILIN MU
September 1, 2022
in Nijeriya
0
2023: INEC ta bayyana wuraren da doka ta haramta yin kamfen da taron siyasa
0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

Yayin da ya rage saura wata ɗaya a fara yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa, sanatoci da na mambobin Majalisar Tarayya, Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta gargaɗi jam’iyyu da ‘yan takara da su guji take dokoki, musamman waɗanda ta haramta a lokacin kamfen.

Daraktan Yaɗa Labarai na hukumar, Mista Festus Okoye, shi ne ya bayyana haka a cikin wata hira da jaridar Punch ta yi da shi a ƙarshen makon da ya gabata.

Za a fara yaƙin neman zaɓe ne a ranar 28 ga Satumba, 2022, yayin da za a yi zaɓen shugaban ƙasa da na ‘yan Majalisar Tarayya a ranar 25 ga Fabrairu, 2023.

Okoye ya bayyana cewa wuraren da dokar INEC ta hana yin kamfen da tarurrukan siyasa sun haɗa da coci-coci, masallatai, gine-gine da ofisoshin Gwamnatin Tarayya na jihohi ko ƙananan hukumomi da kuma amfani da mutum-mutumin ‘masquarade’.

Ya ce ya zama wajibi jam’iyyu da ‘yan takara su bi ƙa’idojin da Dokar Zaɓe ta 2022, Sashe na 92, ta gindaya.

Daga cikin sharuɗɗan da daraktan ya jaddada akwai “yin hani da amfani da mutum-mutumin domin ƙara wa taron siyasa armashi, yin amfani da wuraren ibada, ofisoshin gwamnati ko gine-ginen gwamnati domin yi wa ma’aikata kamfen da sauran su.”

Ya ce: “Sashe na 92 na Dokar Zaɓe ta 2022 ya hana rubutawa ko rera taken jam’iyya ko na ɗan takara ɗauke da kalaman zagi, cin fuska ko aibata wani ɓangaren addini, yare, ƙabila ko wani yankin jama’a.

“Ba a yarda a riƙa amfani da zage-zage a lokacin kamfen ko tarurrukan siyasa ba. Kuma ban da kalaman da ka iya harzuƙa wani ko wasu gungun jama’a su hasala har su tayar da hargitsi. 

“A guji amfani da yare ana cin zarafin wani yare, kuma ban da shaguɓe da kalaman aibatawa da ka iya harzuƙa wasu su ɗauki doka a hannun su.

“Sashe na 3 na wannan doka ya haramta kamfen ko taron siyasa a wuraren ibada, ofishin ‘yan sanda, ofisoshin gwamnati da gine-ginen gwamnati. Saboda haka ba a yarda a tallata jam’iyya ko ɗan takara a waɗannan wurare ba.

“Sashe na 2(5) kuma ya haramta jam’iyya ko ɗan takara ya yi amfani da ‘yan daba ɗauke da makamai. Kada jam’iyya ko ɗan takara ya yi amfani da wasu jami’an tsaro masu zaman kan su ɗauke da makamai a wurin kamfen, taro ko wurin zaɓe.

“Sashe na 7(a) (b) da kuma Sashe na 8 sun jaddada cewa duk wanda ya karya Sashe na 92 za a yi masa tarar naira miliyan ɗaya ko ɗaurin shekara ɗaya, idan ɗan takara ne.

“Idan jam’iyya ce ta karya dokar, za a yi mata tarar naira miliyan biyu. Idan ta ƙara kuma tarar naira miliyan ɗaya.

“Wanda aka kama ya tayar da hargitsi ko ya yi amfani da makami kuma za a yi masa tarar naira 500,000 ko ɗaurin shekaru uku, ko kuma a haɗa masa duka biyun.”

Loading

Tags: Dokar ZaɓeFestus OkoyeHukumar ZaɓeINECjam'iyyu.Majalisar Tarayyatakarawuraren kamfenyaƙin neman zaɓeZaɓen 2023
Previous Post

Rarara ya sake sanya gasar waƙar siyasa

Next Post

An yi mani kan-ta-waye a Kannywood ya fi na naira miliyan ɗaya – Fa’iza Muhammad

Related Posts

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa
Nijeriya

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa

November 7, 2025
Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji
Nijeriya

Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji

November 2, 2025
Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba
Nijeriya

Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba

November 2, 2025
Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje
Nijeriya

Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje

October 29, 2025
Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai
Nijeriya

Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai

August 31, 2025
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar da Sababbin Cibiyoyin Maganin Ciwon Daji

July 24, 2025
Next Post
Fa'iza Muhammad

An yi mani kan-ta-waye a Kannywood ya fi na naira miliyan ɗaya - Fa'iza Muhammad

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!