FITACCEN furodusa kuma sakataren ƙungiyar 13×13 na ƙasa, Abubakar Bashir Maishadda, ya ba da haƙuri ga waɗanda ba su samu nasara ba a gasar waƙar ‘Jagaba Shi Ne Gaba’, amma ya yi masu albishir da sabuwar gasa wadda ƙungiyar ta ta ɗauki nauyi ta waƙar ɗan takarar gwamnan Kano, Malam Sha’aban Ibrahim Sharaɗa mai take ‘Ɗan Ƙaramin Sauro.’
Furodusan ya yi bayanin ne a lokacin da ya ke sanar da yadda za a shiga sabuwar gasar a shafin sa na Instagram da TikTok, ya ce: “Assalamu alaikum wa rahamatullahi wa barakatuhu, masoyan mu da su ke a faɗin duniya. Zan yi amfani da wannan dama wurin gode wa ɗaukaci da kuma ilahirin dukkanin waɗanda su ka shiga gasar ‘Jagaba Shi Ne Gaba’ challenge, wadda Dauda Kahutu Rarara Jami’ar Waƙa ya saka, president na 13×13.”
“To da ma haka abin ya ke, wasu za su ci, wasu ba za su ci ba. Ga wata sabuwar dama ta sake zuwa, waɗanda ba su ci wannan gasar ba ta ‘Jagaba Shi Ne Gaba’, ga sabuwar gasa wadda 13×13 su ka saka, na waƙar da Dauda Kahutu Rarara ya yi wa ɗan takarar gwamnan Jihar Kano a jam’iyyar ADP, Malam Sha’aban Sharaɗa.
“Wannan waƙa ta YouTube channel ɗin Dauda Kahutu Rarara, waƙar mai suna ‘Ɗan Ƙaramin Sauro’. Wannan waƙa ana so a yi minti 2 ne, ko dai a yi minti biyun farko ko kuma a yi minti biyun tsakiya.
“‘Yan TikTok na ɗaya zai ci mota, na biyu zai ci mota, na uku zai ci mota.
“‘Yan Instagram, waɗanda za su yi shutin kenan su saka a Facebook da Instagram kenan, su ma na ɗaya zai ci mota, na biyu zai ci mota, na uku zai ci mota.
“Waɗannan motocin ƙungiyar 13×13 ce ta ɗauki nauyin ba da su.
“Daga kan na huɗu zuwa na goma ‘yan TikTok za su samu Iphone-13 Pro Max. Haka su ma ‘yan Instagram da Facebook daga na huɗu zuwa na goma da za su yi shutin za su samu Iphone-13 Pro Max.
“Kuma in-sha Allahu gasar za a fara daga gobe ne, a bige ta nan sati biyu. So, ya na da kyau duk wanda bai ci waccan ba ya fito ya yi wannan.
“Waɗanda aka ɓata wa rai su ka ji ba su ji daɗi ba, to ga sabuwar dama nan ta sake dawo masu.
“Da fatan Allah Ubangiji ya ba da sa’a, Allah Ubangiji ya taimake mu, Allah ya ba ƙasar mu zaman lafiya.
“Kada dai ku manta, za ku samu wannan waƙar ta Malam Sha’aban Sharaɗa a YouTube channel mai suna Dauda Kahutu Rarara. Kuma in Allah ya yarda gasar za ta fara daga gobe Alhamis har tsawon sati biyu.
“Da fatan masoyan mu za su yi dafifi domin sauke wannan waƙa domin yin ta. Duk wanda ya ke neman ƙarin bayani, zai iya tuntuɓa ta a kan Instagram page ɗi na ko TikTok; ko ta ina ana iya tuntuɓa ta ga duk mai neman ƙarin bayani.
“Ni ne na ku a ko da yaushe, Abubakar Bashir Maishadda. Na gode.”
A yau Alhamis, 1 ga Satumba, 2022 dai za a fara gasar, kuma ita ma za a yi ta kamar yadda aka yi ta ‘Jagaba shi Ne Gaba’. Yayin ɗaukar bidiyon za ka saka hoton Rarara da na Sha’aban Ibrahim Sharaɗa.
Allah ya ba mai rabo sa’a.